Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Captain ne silar lalata komai, a duk lokacin da na yi masa maganar Hurriya ture min maganar yake, saboda yana min kallon wani dan iska, daga baya na fahimci sonta yake shiyasa kansa yake yi ma campaign”
“To kai miyasa baka kirkiri taka Jam’iyar ka yi takara da shi ba? Da ka yi hakan da auren nan yanzu be faru ba”
“Ban yi tunanin zai yi jihadin aurenta a haka ba, na dauka zai hakura da ita ni da shi duk mu rasa…kuma na yi tunanin da gaske din ta aikata sai bayan da gaskiya ta bayyana abun ya zo min a wani iri”
“Ya fika kaunarta shiyasa ta tari yakin gaba da gaba, gashi kuma daga karshe gaskiya ta bayyana cewar bata aikata ba, ka ga ya ci riba, kark sake kirana Salim”
“Ni zaki ce kar na sake kiranki?”
“Ubana ne kai? Alakar dake tsakanina da kai saboda Hurriya ne, yanzu kuma ta yi aure dan haka babu sauran wata alaka tsakaninmu, gaskiya Captain ya fada kana wasa da zuciyar mata shiyasa ko wace macen ka gani sai na nuna kana sonta, da farko ni daga baya kuma ya koma gurin Hurriya, ai kara da ya hana ka aurenta hakan zai koya maka darasi”
“Ko kuma ya koya masa darasi ba, idan har aboki zai iya cin amanar abokinsa na kurciya ya karbe masa yarinyar da yake sannan ya datse alakarsu har ya nuna shi da bindiga kuma yayi masa barazanar rasa aikinsa me kike tunani? Dole shi ma hakki zai bibiye shi”
Namr taja tsaki ta yanke kiran. Daga ita har Salim Momy Hajiya Kaltume da kuma Khairy kwanan bakinciki suka yi a ranar duk saboda bikin Hurriya.
WASHE GARI…
Misalin karfe goma na safe Hurriya na kwace jikin mijinta yana gyara mata baki bayan sun gama cin abinci da breakfast da aka aiko musu daga Family house din su Captain.
“Tashi mu zagaya na fada miki yadda gidanki da dakinki yake”
Ta dan dago kamar bata son motsi, cikin siffar shagwaba da son kuka ta ce.
“Ni dai da ka bar shi, ba amfani tun da ba gani zan yi ba”
“Zaki taba ai, kuma idan ya bude zaki gani”
“Wannan idon abu ne mai wahala ya bude, Appa ya kashe kudi mai yawa akan ido, kullum kara rufewa yake ba budewa ba, yanzu kuma ya rufe gaba daya”
Ya dora gemunsa a saman kanta yana taba fuskarta.
“Zai bude Hurriya zai bude da yardar Allah… Ina ta shirye shirye akwai abun da nake jira ina son nan da dan lokaci zamu tafi Ethiopia akwai wani asibiti ido mai kyau zan saka a dubaki a can zasu Miki aiki kuma ina da yakinin Allah ba zai kunyata mu idonki zai bude”
Ta yi shiru tana sauraren yadda yake gangarawa da hannunsa zuwa gurin da bata tsammani.
“Idan kuma idon be budewa gaba daya fa?”
“Zai bude, ki daina fadar hakan ki yarda zai bude”
Ta zabura ta tashi zaune daidai da sauri ta ture hannunsa. Sai yayi murmushi ya cige baki ya kashe mata ido kamar tana kallonsa.
“Iya daga kafar na yau ne kawai, you better get ready for tonight…”
Ya rada mata a kunne sannan ya mikar da ita tsaye tana bata fuska kamar zata yi kuka, gaba daya sai ta ji tausayin kanta ya kamata.
“Kin tuna ranar da kike fada min na yarda dake na ce miki na yarda baki aikata ba, amman ban tabbatar ba, to anjima zan tabbatar”
Ji ta yi kamar kasa ta bude ta shige ciki tsabar kunya a yanzu ta fahimci inda zancensa ya dora tun a karon farko da yace mata zai tabbatar. Dariya yayi ya rumgume ta ta baya tana takawa a hankali har suka fita dakin. Kitchen suka fara yana fada mata abubuwan dake ciki wadanda aka siya gurin Khadeeja Candy, sannan suka fito suka shiga dayan dakin nan ma ya fada mata abun da ke ciki idan ya fada mata sai ya kai hannunta ta taba ta ji yadda yake da haka har suka fito harabar gidan nan ma ya rika fada mata yadda tsarinsa yake.
“Amman wata zata zauna da ni ko? Idan ka fita”
“Saboda me?”
“Zan ji tsoro ni kadai ai, kuma ban zan iya komai ba ai”
“Baki bukatar yin komai for now, kuma idan zan fita zan tafi dake gida gurin Ammy ki zauna idan zan dawo sai na dauko ki kamin su bar garin nan”
“Wani garin za su koma”
“Kaduna suke zama, ni ma ai da zarar lokacin da aka ba ni a nan ya kare can zan koma a zamu zauna, amman kamin mu zauna can sai mun fara tafiya ayi miki aikin idonki tukuna…”
“Da ace idon zai bude, kai nake son na fara gani Captain…”
Ya kwantar da kansa a kafadarta.
“Ba zan ce Aa ba, amman maybe zan zama mutum na biyu da zaki fara gani saboda iyaye suna raye”
Ta juyo ta saka hannayenta ta lalaba inda saitin fuskarsa yake ta rike fuskar.
“Kana karfafa min guiwa, kai kake fara yarda da ni kamin kowa, na jihadin lokacin da ka yarda ban aikata ba, kuma idan a rufe ido da kunnenka daga jin duk wani abun da za a fada a kaina, har ranar yau ta kasance, duk wata macen mai dacen aure a bayana take a yau…”
Ta yi dage ya duka mata da fuskarsa ta sumbanci shi a gurin hancinsa.
“We deserve each other shiyasa Allah ya hada mu a tare kuma ya tare duk wani abu da zai shiga zuciyata ya bata zamanmu har yau ta kasance”
Hawaye ya sauko mata.
“Ina kaunarka Yaya”
“Yayanki yana gida wannan mijinki ne, My Baby Pearl…”
Ya kwantar da ita a kirjinsa yana shafa bayanta. Cikin gidan suka dawo duk yadda ta so ta ki be barta ba sai da ya taimaka mata ta yi wanka, sannan shi ma yayi suka fito ita da shi suna daure da tawul daya, ita tana ta gabansa shi kuma yayi mata rumfa a baya, har gaban madubin dakin suka tsaya ya cire tawul din sai ta yi saurin juyawa ta rike shi dariya ya sa domin shi ma babu tufafin a jikinsa.
“Idan ba ni ba wa za a kawo w tsaleliyar budurwa kamar wannan kuma ya kyaleta”
Ta saka mishi haka, hakan ya saka shi dauko mata tufafinta ya taimaka ta saka sannan ya shafe mata jikinta da mai kyau ya saka nasa tufafin ya dauki hoda da kansa ya shafa mata ya saka mata man lebe ya saka mata turare sannan wasan ya canja salo. Be kyaleta ba sai da ya ga lokaci na tafiya tukuna ya shiga ya sake tsabtace kansa ya fito ya sumbance ta.
“Zan tafi na gaishe da su Ammy na san yanzu wasu za su fara zuwa ganin amarya kar ayi gulma da ni”
“Ni kadai zaka bari?”
Ya saka bakinsa cikin nata ya sake sumbanta tukuna ya sake ta.
“Mutane za su shigo yanzu ai”
Ya amsa ta sannan ya nufi wayarsa dake kara ya dauka ya duba mai kiran.
“Nafi’u…”
Ya furta sannan ya amsa kiran.
“Hello oga barka da safiya ya aikin”
“Sorry na kira ban sani ba ko kana cikin wani aiki”
“Go ahead”
“Hotunan nan ne aka sake yadawa tsakanin jiya da dare zuwa yau, kuma mun bibiye account din sai kuma samu an goge na alhani amman mun samu information din dayan da ya saka hotunan umarni kawai muke jira mu kama shi a Bincike ina ya samu hotunan”
“Irin wannan ma baku bukatar umarni na Nafi’u just do it ina yaron yake…”
“Kaduna… Ka yi duk yadda za’ayi ku kama shi please kuma ku bincike shi da kyau”
“Okay Sir”
Ya sauke wayar cike da mamakin mai kokarin hana su jindadin rayuwa a yanzu.
“Me ya faru?”
Ta tambaya domin jin yadda yake amsa wayar da kuma yadda yayi shiru bayan amsa wayar ya tabbatar mata da ba kalau. Kallonta yayi sai yayi murmushi ya nufo inda take ya saka zauna.
“Babu komai Babyna wani abun ne da ya shafi aikina”
“Ka tabbata?”
“In Shaa Allah”
Ya sumbanci gefen fuskarta yana kallonta wani irin sonta da son kwanciyar hankalinta ke fisgarsa. Be bar gidan ba sai da mutane suka fara zuwa daga yan’uwansa da na Appa da na Amma musamman wadanda ba garin suke ba.