Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ai na gani, shiyasa yanzu ni ma bake kama jikina, Momy ma bata nuna min komai yanzu amman ita ta saka daina nuna min kyama”
“Zata daina with time, nan gaba zata gane kuskuren abun da take ta daina”
“Allah yasa”
“Ameen”
Ya mike tsaye.
“Ammyna Dada will take a little nap okay?”
“Okay Dada get well soon…”
“Ba dai Soon ba Ammyna, Mamanki ta riga ta shafa min ni ban san yadda aka yi ma muke raba pain din nan ba”
Hurriya ta saka masa dariya sai ya kai mata rankwashi a kai ya nufi dakinsa. Tashi ta yi ta bi bayansa sai ta samu har ya hau gado, remote ta dauka ta rage ac sannan ta lullube shi sai ya saka hannunsa da karfinsa ya janyota ta fado kansa.
“Come here ni kike yi ma dariya dazun dan kin ga gaban Ammyna ne ko?”
Ya fara kokarin tsikararta yana hada mata da mitsika sai ihu take data dariya.
“Na bari Allah na bari Captain”
“Oh Really Captain kai tsaye?”
Ya ma tashi zaune gaba daya yana chakularta.
“Yayana haba Dada Manal, My Noor na bari Allah na daina kuwa, haba Sojana”
Ya sumbance ta ta daga blanket din ya saka ta ciki shi ma ya lulluba ya rumgume a dolenta ta yi bachin da bata tashi yi ba har da su numshari.
*** *** *** **** ****
Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Godiya ta tabbata ga Allah da ya ba ni ikon rubuta wannan littafin. Inda na yi kuskure Allah ya yafe min, darasin dake ciki kuma Allah yasa ni da ku mu amfana da shi.
Haka kuma ina rokon yafiyar wadda duk na batawa rai cikin rashin sani ko ganganci a yafe min da Allah, idan mu ne yau ba mu ne gobe ba.
Ba zan aje alkalamin ba har sai na yi godiya ga duk wanda ya siye littafin Hurriya ma’ana yan paid group na Hurriya, da kuma yan Arewabooks. Na gode na gode na gode, na san kauna ce sila. Allah ya bar min ku.❤️
And to those that read my book without paying da wadanda suka yi forwarding, na bar ku da Rabbi
Malam Mai Tawakkali ina godiya Allah ya kara budi ya karo wasu customers masu yawa
Daga Marubuciyar.
ZAKI
FULANI
GOBENA
HAFSATU MANGA
RAI BIYU
DEENAH
BABBAN GORO
SALEENA
CIWON SO
BAKAR WASIKA
ZAGON KASA
ZABIN RAI
WANI GARI
HURRIYA
Ta ku har kullum
KHADEEJA CANDY
(Oum Namra)
08036126660