Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“I miss you so much, ina jin kamar mun yi shekara ba mu hadu ba haka nake gani”
“Dazun fa kawai muka rabu”
“Yeah kin san na yi alkawari i will spend every hour keeping you safe kuma yau bana tare da ke maybe that’s why na kasa natsuwa”
“I’m safe My Noor baka bukatar ka damu”
“I love you”
“I love you more more more”
Yayi murmushi sannan ya ce.
“Wane hukunci Appa ya yanke? Akan Hamad? Na manta ban tambaya na yana lafiya?”
“Yeah… Amman har yanzu ba su yanke hukunci ba”
“Okay… Je ki kwanta kin ji mai tsada, sleep tight”
“I will i love you”
“Ki yi mafarki kin ji babyna”
Ta yi dariya ta kashe wayar, ta bude dakin ta fito a lokacin da ta sauko sai ta samu Hamad da Amma suna hawaye little Hamad yana kan cinyar Hamad yana rike da hannunsa.
“Me aka yi ma kuka kuma?”
“Farinciki, ban yi tsammanin rayuwa zata sake ara min lokaci na ga wannan ranar ba, ban yi tsammanin dawowar Hamad ba, yanzu iyalina sun cika maza uku mace ta daya”
Hamad ya share hawayensa ya kalli Hurriya.
“Da ace da gaske kowa ya mutu, da ba zan sake farinciki ba, kullum ina tunanin rayuwar baya, idan na tuna ni kadai ne a raye sai na ji na tsani kaina ina yawan tuna gargadin da kike mana na zaman lafiya da juna ni da Hurriya, a lokacin da na yi zaton bata raye my heart keep bleeding, kullum ina tunanin da ma ace ban yi ba”
Amma ta kalli Hurriya still tana hawaye.
“Jamal yaron kirki ne sosai, mai tunani da hangen nesa mai rikon amana mai tausayi ba tare da duban mai zai samu a gaba ba, karki yarda ko da wasa ki batawa mijinki rai Hurriya, ba ko wane namiji ba ne ďan kunama, Jamal namijin da ko wace mace zata dauka uba ne har ta goya da zane, kar wata rana yayi miki wani abu ki manta duk wannan, Allah baya son mai butulci”
“In Shaa Allahu Amma”
Ta maida kanta kasa tana kara godiya ga Allah, a yanzu kam abubuwa da yawa sun daidaita a rayuwarta…
*** *** *** **** ****
BAYAN WAƊANSU SHEKARU….
Ruwa aka sheka yau a Calabar kama da bakin kwarya, sanyi ya sauko ta ko’ina ni’imar Allah ce da rahma. Ko ina yayi tsit abubuwa da yawa sun tsaya saboda ruwan da aka yi wasu na tuni suka shige gidajensu. Ta bangaren bangaren Hurriya ma haka labarin yake daman ba sanin kowa ta yi a garin da aiki ya kawo mijinta ba, idan ma ta sani ba barinta fita yake ba, ya saba mata da zaman katon gidan da sojoji suke gadinsa by fire by force, tun tana complain har ta gaji ta karbi dokar ta zuba masa ido.
Jamal ya fito bathroom yana daure da bathrobe ya nufi dansa dake kuka yana ta masifa.
“Tun da na shiga wanka yaron nan yake kuka amman kin gagara rarrashinsa, saboda kawai baki san zafin haihuwa ba”
“Shi din ne ya cika zuciya fa, wai idan ya fara kuka ba a kama shi ba shi ba zai hakura ba, to ni za a nunawa zuciya ni da nake da Hamad da…”
Ya dora dansa a kafada sannan ya juyo ya kalleta.
“Da wa?”
“Da oga Jamal…”
“Wato idonki yayi kwari har wani kiran sunana kike kai tsaye ko?”
Ta kashe masa ido daya.
“Wayar kai tana ta ringing dazun”
“Waya kira?”
Ya nufi wayar ya dauka yana jijjiga dansa.
“Har five missing calls miyasa baki dauka ba?”
“Yaya Namra ce fa, ko na dauka idan ta ji ni ce ba zata yi magana ba, ka san ai ta saba kira idan ta ji muryarna ba zata ce komai ba sai ta kashe waya”
“Amman ai wani baya zama daya da wani, idan ita tana yanke alaka dake ke sai ki sada ai ke din jininta ce babu yadda zata yi”
“Amman dai Allah yana gani na yi iya yadda zan iya na janyo ta a jikina ta ki ba ni hadin kai, idan na kirata da waya bata dagawa idan na mata magana bata amsa min, haka haihuwar nan da ta yi ina shiga gidanta sai ta bata rai ta dauke min fuska to ya zan yi?”
Ya zauna bakin gadonsa ya maida Aliyu a hannunsa.
“Zo ki ba shi nono, laifinki ne da kike bari yayi kukan ai baki kusa…”
“Ni yar aikinsa ce da zan rika zama kullum kusa da shi saboda kar yayi kuka?”
“To miye aikin ki a gidan idan ba kula da yarana ba? Kin ga ni Baby idan kika yi wasa Allah zan ki sha wahala a garin nan kin san dai baki da kowa a nan sai Allah ko? Ina Manal?”
“Na siyar da ita miliyan biyar na ci tsire”
Yayi dariya ya girgiza kai
“Wallahi da ke ma sai na siyar da ke, bukin nan na Musib da za mu je kawai Appa ya ga babu ke…”
“Wallahi Appa ba zai barka ba, idan ya fara maka masifa sai ka rikice”
“Baki san Appa ya fi so na dake ba yanzu?”
“Ni kuma Daddy da Ammy sun fi ko da kai…”
“Aa aa dama dai jikokinsu kika ce sai na yarda amman ke din? Ta ina?”
Ta bude ido.
“Zan nuna maka kuwa, Allah ya kai mu Kaduna lafiya”
“Ameen bashi nono dan Allah kuma ki daina wofintar min da yaro dan Allah”
“Ban masa komai ba kawai zuciya ce fa, Ammy tace haka ka yi kana karami da an kyaleka sai kuka sai fushi….”
“To miyasa za a aje ni din? Kuma Ammy ta daina zama da ke tana baki labarin kurciyata haka kawai”
Ta ra kwafar da kai tana daga masa gira daya.
“To yaya?”
Yayi dariya yana mika mata Babanshi.
“Wato baki horu ba ko? Duk abun da na yi Miki jiya sai da kika samu baki fada min magana yau har da su daga gira?”
Yana fadar haka sai murmushin dake fuskarta ya gushe ta bata fuskar.
“Na bari yi hakuri”
“Matsoraciya, babu abun da za a fasa yarinya, kara ma ki saba soja fa kika aura ai sai hakuri kawai”
Ya sumbanci goshinta sannan ya mike tsaye yana dariyar keta ta fara shafa mai. Tana rumgume da Haydar tana ba shi nono har ya gama shirinsa ya saka uniform sannan ya zauna kusa da ita yana amsa kiran da Namra ta sake masa.
“Lafiya Kalau ya yaranki?”
“Lafiyarsu kalau, Ya Hurriya da su Manal? Da Daddy”
“Lafiya Kalau”
“Captain daman ni ce nake son na je Gusau yau kuma babu flight, shi ne nace bari na tambaya ko zan samu ta bangarenka lefen Musib za a kai kuma bana son aje ba tare da ni ba”
Captain ya daga hannunsa ya dafa matarsa.
“Wallahi Daddy ya karbe komai nasa a gurina, ya cire sunana a komai ba ni da ikon komai nasa yanzu sai dai ki kira shi ki yi magana da shi”
“Me yasa?”
“Saboda na ki yarda na aje aiki na tsumduma a harkokinsa”
“Okay bari na kira Momy sai ta mishi magana ko Ammy”
“Okay ki gaishe da Sadiq”
Captain na sauke wayar Hurriya ta kalleshi sai ya sumbanci idonta
“Yaushe yayi haka?”
“An kwana biyu”
“Amman kansan baka kyauta masa ba ko? Be kamata ka yi haka ba”
“Babyna mutum be da ra’ayin kansa ne? Bana son kasuwanci Allah ya gani na fi jindadin aikina”
“Haba Noor idan baka maka ba wa zai masa? Kai kadai yake da shi fa, kuma wani abun ko bama so haka zamu daure mu aikata saboda iyaye”
“Baki fatan na kai Major General ne? Yanzu gashi an kara mukami kuma a haka sai na bar aikina na koma ga wanda ban saba ba, ba wai ba zan yi ba ne gaba daya, zan yi amman na hada biyu”
“Ni daman ba son aikin naka nake ba, kullum muna wannan garin gobe muna can ni dan Allah ka aje ka ka bi abunda Daddy yake so if not…”
Ta aje masa babynsa ta mike tsaye sai yayi hanzarin mikewa ya rumgume ta ta baya.
“Me zai faru haba yan matana my one and only daga ke ba kari idan ina soja, idan na zama dan kasuwa kuma… That’s the whole different story”
Ta Bude baki ta juyo ta kalleshi.
“To me kake nufi”
Da dariya yayi ya rumgume ta yana sumbantarta.
“Uwargidata kuma amarya wasa nake, kar a hana ni abinci a yau”
Ta yi dariya tana lilo a jikinsa.
“Karamin aikina ne kuwa”
Ya shiga gyara mata girarta.