Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Amma karya yake, karfe 1:30pm aka tashe mu shi ne na ce nasa yaje yayi sallah saboda bus din mu sai 2pm take zuwa ai, shi ne ya taso min fa masifa har zai yi dambe da ni gaban yan makaranta har da yan ajinsu fa”
Hamad ya juyo ya kalleta a fusace.
“Toh ina ruwanki da ni da zaki ce na tashi na yi sallah, kafiri ne ni ko bana sallah aka ce miki? Salon friends dina su fara tsokana ta suna cewa bana son sallah”
“Na ji ba zan sake maka magana ba, amman ni ma karka sake zuwa class dinmu ka ce na ara maka wani abu, ba ruwana da kai karka sake taba min komai kuma safata da ka saka yau ban yafe ba karka sake min taba min komai”
Amma ta mike tsaye tana kallonsu kowane zuciyarsa ta kawo kamar abokan gaba.
“Wannan fadan duk na minene wai? Ku kullum baku zaman lafiya? Kai kake binta amman kai da ita babu zaman lafiya, abinci ma ba zaku ci a plate daya ba, magana mai dadi babu tsakaninku kullum sai fada?”
Hamad ya ce.
“Ita ce bata ba ni respect ai”
“How? Kai ne babba or ni? Ni ce babba ai kai ya kamata ka ba ni respect”
“Ni ba zan taba baki respect ba i hate you kuma kika sake min wata maganar banza sai na ballaki”
Hamad na kaiwa nan ya juya ya fice rike da jakarsa har yana bankade Hurriya.
“Amma kin ga ko? Imagine”
Amma ta dafe kanta ta zauna bakin gadon tana fashewa da kuka.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”
A take jikin Hurriya yayi sanyi ta bar jikin kofar ta karasa inda Amma take ta zauna kusa da ita, domin suna yawan samun tsabani da Hamad saboda rashin jituwa dake tsakaninsu su yi fada wani lokacin har dambe suke, Amman Ammansu bata taba kuka ta zubar da hawaye ba akan haka ba sai yau.
https://chat.whatsapp.com/LimnMeG0kWvIfT6JQvVMh1
☆❁ ❁☆
3️⃣
“Amma I’m sorry laifin fa duk na Hamad ne shi ba a masa magana ya ji”
Amma ta dago da idanuwanta da suka kumbura ta kalleta.
“Ke ai kina ji? Kuma ke ce yayarsa ki daina biye masa mana, ki zauna lafiya da dan’uwanki dan Allah, kullum ina fada muku haka amman baku ji, Hurriya ki daina biye masa kina kallon ba sonku ake a gidan nan ba, a madadin ku so kanku kullum sai rigima da junanku”
Amma na magana Hurriya na yawo da idonta akan akwatunan da suke tsaye gefen kofar dakin da bata lura da su ba sai a yanzu.
“Amma kayan miye a akwaitinki?”
“Tafiya zan yi”
Hurriya ta dubeta da sauri tana kallonta da ya kumbura sosai.
“Amma ina zaki je?”
“Gida zan koma gurin Gwaggo”
“Saboda me?”
Amma ta yi murmushi hawaye na sauko mata.
“Hurriya abincina ya kare a gidan mahaifinku”
“Kamar Yaya? Toh ba sai ya kawo wani ba? Amma me ya faru kika yi kuka? Me yasa zaki tafi?”
Amma ta rufe ido ta dantse baki.
“Je ki kira Hamad”
Hurriya da bata gama fahimtar abun da yake faruwa ba idonta ya cika da hawaye har ya zubo ta kasan gilashin da shi ne rayuwarta. Ta mike tsaye ta fice daga dakin kamin ta isa dakin Hamad ta cire hijabin dake jikinta ta rike a hannu tana tafe tana hawaye har ta isa bakin kofar dakin. Murda kofar dakin ta yi ta tura ta shiga, Hamad dake sanye da short yana kokarin cire safar kafarsa ya kalleta.
“What? Amma ta miki fada ko? That’s good next time sai ki sake shiga min hanci”
Ya fada azatonsa Amma ta yi mata fada ne sosai, daman haka take sometime idan aka yi mata fada kuka take.
“Ba saboda haka ba ne, Amma ta ce na kira ka kuma kuka take yi, ban san abun da aka yi mata ba”
Be tsaya ya karasa cire safar daya ba ya sauko da kafar ya biyo bayan Hurriya da tuni ta juya bayan ta isar masa da sakon Amma. Hamad na shiga dakin ya karasa inda take zaune ya zauna bakin gadon babu abun da zuciyarsa take nuna masa sai fadan da suka yi da Hurriya.
“Amma saboda Hurriya ne ko?”
Amma ta share hawayenta ta kalleshi, sannan ta kalli Hurriya ta mika mata hannu. Hurriya dake tsaye jikin kofar dakin ta karaso da sauri hawaye na sauko mata ta kasan gilashin dake idonta. Amma ta kama Hamad ta dauki hannu Hurriya ta dora a saman hannun na Hamad.
“Dan Allah ku zauna lafiya, ku so junanku ku kaunaci junanku, kai baka da wata yar’uwa da ta fi Hurriya, Hurriya ke ma baki da wani dan’uwa da ya fi Hamad, wannan yawan fadan da kuke yi ku daina anyi ance da rashin bawa juna girma duk ku aje shi a gafe, musamman ma kai Hamad idan baka canja wannan hallayar ba zaka sha wahala a gidan nan kana kallon yadda kake rayuwa ma yanzu balle kuma idan bana nan”
“Amma ina zaki je?”
Hurriya ta tambaya daman ta kagu ta ji domin hankalinta yayi matukar tashi akan hawayen da ta gani a idon mahaifiyarta ga kuma tufafinta a shirye. Amma ta kalli Hurriya sai ta rasa ta ina zata fara amsa mata tambayarta, at her age it’s too early ta fada mata sakinta mahaifinsu ya yi, ita kanta kalmar tana mata nauyin furtawa a yanzu balle kuma yadda ƴaƴanta za su ji idan ya sauka a kunnesu har su fahimta.
“Gida zan tafi gurin Gwaggo ba na fada miki ba? Sai na haihu zan dawo, za’a rika kai ku kuna duba ni”
“Me yasa ba zaki haihu a nan ba? Kuma kike kuka?”
Hamad ya tambaya ya tambaya yana kallon cikin idonta kamar mai kokarin kure karyarta. Amma ta yi murmushi ta share hawayenta.
“Saboda bana jindadi a yanzu, bayan kun fita rashin lafiya ta taso min, kuma ina yawan yin haka a duk lokacin da kuka tafi makaranta, kuma kin fi kowa sanin bana son mai aiki na fi sha’awar na yi komai da kaina, ni da mahaifinku muka yanke shawarar zan koma gida na zauna har sai na haihu na samu lafiya, shiyasa ban tafi ba na jiran har sai kun dawo na sanar da ku, kuma na ja muku kunne dan Allah ku zauna lafiya”
Kalaman da Amma ta yi a yanzu sun sanyaya zuciyar Hurriya har ta samu kuzarin cire gilashin idonta ta goge hawayenta ta maida abokin rayuwarta.
“Allah ya baki lafiya Amma, zamu rika zuwa kullum”
“Ba kullum ba dai sai a lokutan da mahaifinku ya zaba, kuma ku masa biyayya dan Allah ku zauna lafiya da kowa, ke dai na san baki da rigima Hamad ne mai matsala”
Hamad dai be sake cewa komai ba sai kallon mahaifiyarsa yake zuciyarsa na raya masa wani abun na dabam.
“Ku rike karatunku, boko da Islamiya karku saka wasa”
“In Shaa Allah Amma zamu zama yara masu kirki”
Hurriya ta fada da murmushi a fuskarta. Hamad kam kallonta kawai yake kamar wadda aka cewa mutuwa zata yi anjima.
“Je ka saka tufafinka ku rika min kayan na kai mota”
Ya mike tsaye ya fice daga dakin cikin wani yanayi kamar ba shi ba, yadda ya natsu a lokaci daya wani tunani ya zo masa sai ka dauka wani babban saurayi ne.
“Amma wa zai rika ba mu abinci?”
“Haka ne na manta ma yau ban girka muku komai ba, sai da ku sarrafa wani abun ku ci, ko kuma ku sha tea, idan mahaifinku ya dawo zai fada muku gurin da zaku karbi abinci, gurin Momy ko Hajiya Kaltume shi zaku tambaya”
“Toh Amma Allah ya dawo mana dake lafiya”
“Ameen”
Ta amsa tana danne abun da take ji a zuciyarta, sannan ta mike tsaye ta dauki hijabinta ta saka ta fara fitar da kayan Hurriya na taya ta kamin Hamad ya fito shi ma ya saka hannu suka dauka suka kai mata gurin mota. Ta saka wasu a bayan mota wasu kuma a back seat sannan ta shafa kan ƴaƴanta tana murmushi Hurriya ma murmushin take Hamad kuma ya hade rai kamar wadda aka yi ma laifi.
“Allah ya muku albarka ya tsare ku, kuma na fada muku zan kara jaddada muku ban da fada ku daina fada dan Allah”
A nan din ma Hurriya ce ta amsa Hamad kuma yayi kamar be ji ba, shi dai sai kallon mahaifiyarsa yake fuska babu annuri.