Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Hajiya ta zauna a kujera tana hade fuska.
“Ja’irar yarinya wato ita nan har ta iya munafurci, to yayi kyau zata ko ci ubanta a gidan nan, ke ma kuma da laifinki miye na zuwa ki yi wannan shigar rabin jikinki duk a waje, Fisabilillahi Khairi wani mutumen kwarai ne zai so ganinki haka? Dan Allah ku rika kiyayewa mana muna fa cikin makiya da basa son cigaban mu, abu kadan dariya za’ayi mana a ji dadi”
“Wallahi Hajiya ba ni kadai nake jan abun magana ba, Hurriya ma baki ga mutanen da suke mata magana ba a gurin, babu wanda be san Adam ba dan gidan Alhaji Buba Sarauta yaron da yayi kaurin suna gurin iskanci amman haka ta zauna yana ta zuba mata dollars har daukarta yayi suka fita ya dawo da ita, amman da yake makira ce shi ne ta kira Yaya ta fada masa ya zo ya tarwatsa min taro”
Ta karasa tana jin wani irin bakinciki ko cake din birthday da ta kashewa kudi mai yawa bata ci ba. Gashi kuma Yayanta ya ci mutuncinta a gaban friends dinta on a special day like this one zai zame mata abun magana.
“To an yi mugun gado, indai shigewa maza ne Hurriya ta fara yi to gurin uwarta ta gado, ba yau aka fara ba a nono ta sha, ba haka ta yi har ta aure min miji ba, ai barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba, kamar kumbo kamar kurensa. Tashi ki saka rufafin kwarai mu tafi asibiti a duba fuskar nan taki kar ta kwana tana miki zogi”
Ta tashi daker tana kuka sosai ta nufi stairs sai a lokacin suka lura da Ruma dake tsaye a stairs din tana kallonsu ita bata sauko ba kuma ita bata koma ba.
“Toh lafiya? Kin san yanzu kin zama aljanna ni tsoronki ma nake, kin zama wata halittar ta dabam a cikinmu”
Hajiya ta fada tana nuna Ruma da har lokacin bata ce komai ba, sai ma juyawa da ta yi ta koma sama, gaba daya ta canja tun bayan da ta dawo daga hannun masu garkuwa da mutane ta tsani gidan da mutanen cikinsa, ba kasafai zaka ganta a wani abu da kowa yake tarayya ba, wannan dalilin ya hanata zuwa birthday din Khairi kuwa da kusanci na kasancewarta yar’uwarta. Hajiya kamar wata gurguwa haka ta hau sama daker ta shiga nata dakin ta dauko mayafinta da jakarta sannan ta kira direba ta fasa masa ya kunna mota za su fita. Sai da ya shiga dakin Khairi sai ta same ta har lokacin kuka take tana zaune a kasa.
“Ba zaki je ba na tafi? Ba saboda zuwanki ne kadai ba ina son na kai kafar nan a duba min”
Cikin kuka Khairi ta kalleta ta ce
“Hajiya ba ki ga wulakanci da Hurriya taja aka yi min ba Wallahi, Yaya ya wulakanta ni gaban friends dina”
“Toh ya zaki yi sai ki yi hakuri munafurci daman ai ya cikawa Hurriya ciki, ganewa ne ba a yi sai yanzu amman na san maganinta ai, ke ma kuma fa baki kyauta ba ni Allah yasa dai Fadeel be ganki da wannan shigar ba, abu kamar karuwar Lagos haba Khairi”
Ta tashi tana kuka ta nufi gurin da tufafinta suke ta bude, cikin kuka ta canja tufafin sannan ta biyo bayan Hajiya Kaltume da tuni ta sauka kasa.
HURRIYA POV.
Tana tsaye a waje har Yasir ya fito ransa a bace ya sake shiga motarsa da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dan leka bangaren Hajiya Kaltume kamar zata shiga wai dan ta wanke kanta ta fadawa Khairi da Hajiya Kaltume ba ita ta zugo shi ya shigo gurin ba, sanin ba za su kwashe da dadi ba ya saka ta juya ta fice daga bangaren ta nufi bangaren Momy. A hankali ta tura kofar falon ta shiga tsoron dake cikin cikinta ya hanata sallama har ta isa tsakiyar falon.
“Salon labe ne ko kuma rainin wayo? Zaki shigo min falo babu sallama?”
“Yi hakuri Momy mantawa na yi”
Ta fada da muryarta da bata gama fita ba.
“Daga ina kika?”
“Gurin Birthday din Yaya Khairi”
Momy ta dauke kai ta cigaba da latsa wayarta, Hurriya na ganin haka ta raba ta haye sama ta shiga dakinta. Sai kusan magariba Namra ta dawo gidan, tufafinta kawai ta cire ta shiga dakin Momy tana bata labarin abun da ya faru ita kanta ta cika da mamaki irin shigar da Khairi ta yi ga kuma wasu watsassun kawayenta da bata san a ina ta samo su ba.
“To ke me kike baki dawo gida da tun dazun ba?”
“Momy ina can ina jiran wanda zai dauko ni fa, gaba daya a hargitse aka watse taron saboda Yaya Yasir ni ma ba dan na boya ba Allah kadai ya san kalar dukan da zai min”
“Ya dokeki saboda shi ya haifa ki? Ai ba zan dauki wannan ba, ya taba dinka kala daya ya kawo miki? Sai yanzu da girmanki zai ce ya saka miki hannu ya dakeki saboda bikin da kanwarsa ta shirya?”
“Momy dan baki ga bikin ba ne, bari na nuna miki dress din Khairi kamar ba yar gidan nan ba”
Ta shiga gallery wayarta ta kama hotunan da ta yi ma Khairi tana nunawa Momy.
“Momy kalli fa, ni ma raina ya bace da abun da ta yi Wallahi, ai na jidadi da Hurriya ta fadawa Yaya Yasir ya zo ya watse taron nan”
“Au Hurriyar ce ma ta fada masa abun da ake yi? Ina ta ganshi to?”
“Oho mu ma kamar daga sama muka ganshi ina ganin ya fada jibgar Khairi na boya ban bari na gan ni ba”
“Ikon Allah yaushe kuma Hurriya ta fara zama munafuka? Hada yaya da kanwa? Wannan kam ba shi da kyau ai, ko bata fada masa ba ai ya san kanwarsa zata aikata yadda take jin ita sa’ar kowa ce kawaye babu na albarka ai dole ma ta aikata, kuma Alhaji ba zai ce komai ba duk abun da Kaltume ta yi ai shi ne daidai a gidan nan ita da yaranta yanzu basa laifi”
“Gaskiya Momy kawayenta gaba daya babu na gari, wani dayan frind dinta ya zo yana yi ma Hurriya liki da dollars”
“Rawa ta yi”
“Aa Momy kin san ai ba zata yi rawa ba, Momy kin san shi ma Adam ne fa, dan gidan Sarauta”
“Ba dai dan Hajiya Nana ba?”
“Shi fa, yaron nan yana wasa da kudi”
“A ina ta san shi?”
“Ni ma ban sani ba, bari ma na tafi na tambayeta”
Ta tashi da saurinta ta bar wayar a gurin ta fice daga dakin Momy bata zame ko’ina ba sai dakin Hurriya. Cikin natsuwa irin na masu son gulma ta tura kofar dakin ta shiga, Hurriya na tsaye jikin windows, dan kwalin abayarta ya sauko saman wuyanta hannunta kuma yana wuyanta tana shafawa zuciyarta kuma ta tafi wata duniyar karatu.
“Hurriya…”
Ta juyo ta kalli yayarta, Namra ta maida kofar ta rufe ta nufi gurin da Hurriya take tsaye.
“Me kike yi”
“Ba komai kawai ina tunanin Hamad ne”
Ta fada tana sauke idonta kasa.
“Ke dai kin saka Hamad a ranki Hurriya, idan yana raye Allah ya bayyana shi idan kuma ya mutu Allah ya jikansa da Rahma”
“Amin”
Hawaye ya sauko mata.
“Da ace yana nan kusa da mu, wata kila da yanzu muna son junanmu ba kamar baya ba, wani lokacin ina jin bukatar abokin tattaunawa, har yanzu na kasa sabawa da rashinsa ina jin kadaici sosai”
“Ki yi ta addu’a abun zai cire miki In Shaa Allah, amman shiga damuwar da kike ina tunanin shi ne silar daya kara jefa Amma cikin damuwa”
“Ina kokari Yaya Namra bana bari ta gane ina cikin damuwa”
“Haka na da kyau, yauwa Hurriya kin san wannan wanda yayi miki karin kudi dazu?”
Ta share hawayenta da gefen hannun rigar abayar.
“Aa ban san shi ba, dazun ne ma na fara ganinsa”
“Toh amman kuma yake miki karin kudin haka nan kawai?”
“Ni ma abun ya ba ni mamaki sunana ma ban san inda ya ji ba”
“Maybe ko ya sanki wani gurin ke ce baki san shi ba”
“Ni da ba fita nake ba, amman ni ma mamaki nake”
“Toh ki yi hankali da shi yaron nan dan shaye shaye ne”
Ta amsa mata kai kamin ta ce.
“Yaya Namra dan Allah zaki taimaka min na fadawa Hajiya ba ni na kira Ya Yasir ya shiga ciki ba?”