VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Hurriya ta tashi gaban madubin da take ta juyo ta kalli Momy dake kallonta kamar maciji yayi arba da kyanwa.

“Daga yau babu ke babu Captain, kar wata magana ta sake shiga tsakaninki da shi, kuma ko kallonsa kika sake yi sai kusa kasheki… Na fada miki”

Hurriya ta daga kanta da sauri, Momy ta ja kofar dakin ta fice, Hurriya ta dafa zuciyarta domin ba kadan Momy ta tsorata ba.

“All because of Captain? Ya Allah…. Kamar za su cinye ni ni miye nawa a ciki? Saboda kawai yana kula ni, su basa kaunar wani ya nuna min tausayi”

Ta koma ta zauna tana busar da iskar bakinta, gaba daya ma sai ta ji gidan ya fita ranta. A karo na biyu ta mike tsaye sai dai banbancin wannan tsayin da na farkon wacan na shigor da Momy ta yi ne a birkice tana mata masifa wannan kuma na neman barin gidan dakin ne. Green hijabi dinta ta dauka ta saka ta saka shoes dinta ta fice daga dakin, ta san ba ta isa ta tambayi Momy permission din fita daga gidan ba daman babu ruwanta da ita ko da zata fita ta dade a waje balle kuma yanzu da take jin haushinta. Haka ma ba zata tunkari Hajiya Kaltume tace mata zata fita ba daman ba bangarenta take ba, kuma duka duka yau ta dawo daga gidan bayan shafi sati daya da ta yi a asibitin. Tana fita harabar gidan na Momy ta isa gate dinta sai yaja ta tsaya tana tunanin ta saci kafa ta tafi gidansu Husna ko kuma dai ta hakura ta koma a gidan da baya mata dadin zama a yanzu? Jingina da ta yi da gate din tana kallon Babban gate din gidan da masu gadi suka bude. Ganin Motar Appa ya kara karya mata guiwa daman shi baya son fitarta tun tana da gata a gurinsa balle kuma bayan da ya saka mata takunkumin zama gida da hana ta zuwa gurin Amma ba tare da dalili ba. A madadin direbansa ya nufi bangarensa sai ta ga akalar motar ta nufo gurin da take tsaye wato bangaren Momy, Hurriya ta bar jikin gate din da sauri ta juyo zata dawo ciki gabanta na faduwa zuciyarta na raya mata Momy ta hada ta Appa ne wata kila saboda Captain shiyasa har ya dawo yanzu kuma ya nufo bangaren yayi mata fada. Sai dai horn din da ta ji anyi ya katse hanzarinta na guduwa ta koma bangaren na Momy, a lokacin da ta juyo sai ta an faka motar daidai gate din Momy, an sake danna horn. Cikin karfin hali da hararon laifinta ta nufo motar ta mahaifinta da be cika hawa ba sai lokaci zuwa lokaci, daman haka yake idan ya hau wannan gobe zai iya hawan wata. Daidai gurin gilashin motarsa dake back seat ta tsaya domin ta san bangaren da mahaifinta yake zama a duk lokacin da direba yake tuka shi. Appa ya sauke gilashin motar ya kalli yarsa.

“Hurriya na ganki tsaye a nan kamar cikin damuwa, na saka direba na zo kuma sai kika gudu?”

“Na dauka fada zaka min”

Ta fada a shagwabe tana taba yatsun hannunta.

“Fada me kika yi?”

Ta yi shiru tana kallon kasa, sai tausayinta ya kama shi, soyayyar da yake mata irin ta uba da ƴa tana ta dawo masa a hankali.

“Shigo mota”

Ta daga kai ta kalleshi sannan ta zagaya ta shiga ta dayan side din, direban yayi baya kadan ya canja akalar motar suka nufi bangaren Appa.

“Wani abun aka miki ne?”

Ta kalli Appa tana mai mamakin yadda yake son ya ji damuwarta a yau, abun da aka haka rame aka binne shekaru hudu da suka wuce. Ta girgiza kai

“Aa”

“To ya na ga duk kin bata rai? Wani abu kike so?”

Ta sake dubansa neman sanin damuwarta da yake kokarin yi a yanzu ya fi komai faranta mata rai.

“Ina son na tafi na duba Amma ne!”

Ta furta abun da ba da shi ta fito bangaren Momy ba, farko fitowarta na neman son tafiya gidansu Husna ne, sai dai kuma bata san kalma da zata fito a bakin Appa ba idan tace masa gidansu kawarta Husna zata ce bayan sun yi baran-baran da mahaifinta saboda munafurcin da aka mata sherin cewar ta kulla.

“Ki saki ranki, daman takardu na dawo na dauka ki jira ni a mota yanzu idan na fito sai mu sauke ki a can na wuce, amman karki kai dare”

“Ba zan kai dare ba Appa”

Ta amsa muryarta na karkarwa saboda kokarin danne kukanta da take. Ta manta when last ta shiga mota daya da mahaifinta, ta manta when last mahaifinta ya nuna damuwa da ita, ta manta rabon da magana mai taushi mai dadi ta shiga tsakaninta da mahaifinta. Ta zauna a motar na tsawon lokacin da ya fita ya shiga bangarensa ya dauko abin da zai dauko ya fita ya dawo cikin motar. A lokacin da ya dawo cikin motar sai ta karkarta idonta tana kallon mahaifinta irin kallon da an shafe mata yinsa a rayuwarta. Direba na tuki Appa yana duba takardun da ya dauko ita kuma tana kallonsa idan hawaye suka sauko mata sai ta share cikin hikima ba tare da ya gani ba, lallai a yau ta kara yarda da tabbatar da ko wace ƴa a duniya gatanta uba ne, ko magana yake maka mai dadi zaka ji ka fi kowa rabo da dace a duniya.

“Hurriya ina tunanin dawowa da yaran nan a gidan nan, saboda ita can ba lafiya ta wadace ba, kuma ni ba wani sanina suka yi sosai ba, yadda nake rayuwa da duk yarana su ban yi rayuwa da su a haka ba, ya kamata su dawo nan ni daman bana son rikon ƴaƴa a gurin kowa, na fi son yarana suna hannuna, ballantana kuma su da suke kanana, yanzu suke bukatar gata”

Da gaske Appa ne yake wannan maganar ko kuma dai mafarki take yi? Shawararta yake nema ko kuma fada mata ne yake abun da zai faru? Ta juyar da fuskarta ta matse kwalla sannan ta juyo ta ce.

“Za su fi jindadin zama a can Appa saboda Amma tana can kuma Gwaggo zata kula da su sosai”

Sai a lokacin Appa ya dago ya kalleta.

“Ga ki zaki iya kula da kanenki ai kamin a sama miki admission, kuma za a iya daukar mai aiki ta kula da su, amman maganar gaske ni bana son zaman yarana a ko’in sai a gidana”

Tabbas haka ne, ba ita kadai ba kowa ya shaida hakan a familynsu Appa baya bada rikon yayansa ga kowa ko da kuwa Hajiya Binta ce da ta kasance mahaifiyarsa, shiyasa a lokacin da aka haifi yaran be je duba su ba kuma be je duba mahaifiyarsu ba ya baya kowa mamaki, sannan ya kyale su be tana cewa bari ya dauko su ko shi ya tafi ya gansu ba. Wani mamakin be kamata ba sai da Appa ya katse mata hanzarin tunanin da take ta hanyar aje mata kudi mai kauri a dan space din dake tsakaninsa da yarsa.

“Ki bawa Hassan da Husaini wannan, kuma ki musu magana ina son zan shigo mu gaisa da yarana”

“Toh Appa”

Wannan karon bata iya taimako kanta ba har sai da hawayen suka zubo mata, ta dauki kudin ta bude motar ta fita ta shiga cikin gidan. Appa na zaune a motar yana kallon kofar gidan ya takure fuskarsa a yanayin damuwa kamar mai tunanin wani abu, can kuma ya sauke ajiyar zuciya.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, Allah ka raba mu da aikin dana sani”

Ya fada yana kallon twins din da Hurriya ta fito tana rike da su ta nufo motarsa. Bude gefensa yayi sai suka zo da gudu kamar wasu wadanda suka saba rayuwa da shi, suka shige motar suna murna. Jinin alakar uba da ƴaƴa ya saka sun wayanci shi din ubansu ne tun a ranar da Rukayya ta tafi da su har suka kwana a gidan, daman kuma Gwaggo na nuna musu hoton mahaifinsu a wayar Rukayya saboda su san shi ko da ba su rabe shi ba.

“Gwaggo tace na kawo maka su ka gansu”

Hurriya ta fada cikin rashin jindadi domin bata so Gwaggo ta hana shi shiga gidan ba. Appa yayi murmushi domin shi ba yaro ba ne ya gama fahimtar komai a kawo masa yaran da aka yi a waje.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected