VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Ya aje mata goro da dabino na daurin auren a gadonta.

“Kin ga goro da dabino nan!”

Ta kalli goron da dabino har lokacin dariya take domin maganar Appa ba magana ce mai kama kai ba, sai dai kume? Appa ba zai mata wasa ba, ba zai ce anyi ba alhalin ba ayi ba. A take dariyar ta bace mata bat ta daga kai ta kalli Appa.

“Da gaske Alhaji? Yayana ya zo gidan nan ya nemawa Captain auren Hurriya?”

“Har an daura, yace ba zai iya da rigimarki ba, dan haka ya wuce yace ni na sanar miki….”

Momy ta mike tsaye wayar dake cinyarta ta fadi kasa.

“Aure Alhaji? Auren Hurriya aka daura da Captain?”

“Kwarai, kowa ya ji zai yi mamaki, kuma tabbas Alhaji Turaki ya kai mutumen kirki har ya wuce, ya yaye min bakinciki kuma na yarda zai rike yata da amana”

Momy ta dafe zuciyarta.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un
La’ilaha Illallahu Muhammad Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam”

Appa ya bita da kallon al’ajabi ganin yadda ta yi kamar wadda aka fadawa mugun abu.

“Yanzu duk matan duniyar nan Captain ya rasa wa zai aura sai Hurriya? Yarinyar da duniya ta gama ganin tsiraicinta? Yarinyar da ko ido bata shi a yanzu? Anya Captain yana cikin hayyacinsa?”

“Ita Hurriya ba mace ba ce? Da kike fadar ya rasa wa zai aura sai ita? Wane irin magana kike haka ne Nafisa?”

“Captain ya fi karfin Hurriya bata cancance shi ba, rantsuwa fa na yi cewar Captain ba zai auri Hurriya ba, shi ne Yaya zai shammace ni? Kuma ya biya sadakinta da zinarina da ban taba sakawa ba? Naira miliyan hansi akan makauniya yarinyar da duniya ta gama da ita?”

Appa ya mike tsaye ya daga hannu kamar zai mari Momy sai kuma wata zuciyar ta hana shi, a madadin haka ya nunata da yatsansa.

“Ki san abubuwa da kike fada akan Hurriya, kamar kin mace a gaban waye kike tsaye ni fa na haifi Hurriya, a madadin ki yi farinciki jininki ya auri jini sai ya zama abun bakinciki a gurinki”

“Idan kai ne mahaifin Hurriya sai me? Na yi farinciki ďan ďan’uwana ya dauko yar kishiya ya kawo a matsayin suruka? Ya tsallake Namra ya tsallake duk yaran family ya fada gurin Hurriya”

Appa yayi murmushi yayi girgiza kai.

“Yanzu na fahimci komai, Allah ya huci zuciyarki yara kuma Allah ua ba su zaman lafiya… ”

Appa yayi dariya mai sauti ya fice daga dakin. Momy ta dora hannu a kai tana ta rawa kamar mai jin sanyi.

“Daman wannan ne dalilin zuwa? Har kana fada min Captain ya hakura? Ni kake yi ma wayon Yaya? Ko ba zai auri Namra ba me yasa zaka amince masa ya auri Hurriya? A cikin falona za a nemi auren yar kishiyata ba yata ba, duk tarin dukiyar Yaya da ta matarsa ďa ďaya da suke ji da shi ya rasa wa zai aura a duniya sai Hurriya? Yarinyar ido ya rufe mata? Aka tallata tsiraicinta, yarinyar da uwarta ma ga aiki ta yi, talakawa maskakanta, tarin dukiyar Yaya Yau Hurriya ce yarinyar da zata raba a jiki a dukiyar gidanmu, kuma ta bangaren da ya fi gwabi”

Daki cinyarta tana jin kamar ta zaga tufafin jikinta, a matukar fucece ta fice daga dakin ta shiga dakin Hurriya ta fara yaye Bedsheets dinta ta jefar tana debo kayanta ta watsarwa abubuwan da ke fashewa kuma tana ta fashe su tana watsar tana kuka.

“Ashe sheri ne ya kawo ki bangaren nan, ashe mugun abu na karba na aje gashi nan kina bibiyata”

“Momy lafiya”

Namra ta tambaya tana kallon yadda ta watsar da kayan Hurriya ta fasa abubuwa. Momy ta juyo a lokacin da ta kalli Namra sai tausayin yarta ya kamata.

“Yayana ya daureni ya ci amanata Namra, na ci mutunci na ya watsa min kasa a ido, kuma ya nuna min ďansa ya fi yar’uwarsa”

“Momy dan Allah ki fada min me ya faru?”

“Auren Hurriya ya nema a gurin Appanku, Appanku kuma ya amince aka daura auren a cikin gidan nan yanzu nan”

Namra ta ji kanta ya dara da karfi.

“Aure abun kamar yar tsana? Ban gane aka daura ba, an taba daura auren haka babu kowa?”

“Daga mahaifinku sai Yayana da Yasir aka daura auren”

Wani abu ta ji mai sanyi ya ratsa kanta ya sauko har kafafuwanta.

“Momy da gaske…?”

“Me zai sa na miki karya.? Yaya yayi min abun da ban yi tsammani ba, da ace wani ne yayi min ba yayana ba zan ji zafi haka ba, amman ba komai kowa yayi mai kyau zai gani kuma Wallahi Hurriya ba zata sake zama bangaren nan ba”

Namra ta yi baya baya ta fice daga dakin daman a bakin kofa take tsaye. Dakinta ta shiga ta rufe kofar ta zauna hawaye suka silala mata a hankali.

“Aure?”

Ya tambayi kanta abin dai kamar ba zata fahimta ba. Shi ke nan duk wani fata da take da kuma wanda iyayensu suke yi ya tashi a banza yanzu? Hurriya ta shiga tsakaninta da Salim yanzu kuma ta raba ta da Captain ta aureshi? Ta mike tsaye ta isa gaban madubin dakinta ta zauna a stool tana kallon kanta, shi ita bata kai ba ne da Captain be yi hauka a kanta ba? Taya idonsa zai rufe ya tsallake ta ya fada kan yar’uwarta bayan duk abun da ya faru da Hurriya, to da bata aikata ba ai ta yi abin kunya, ta yi abun da cikaken namiji mai aji irin Captain zai guje ta zama matarsa ko dan saboda kunyar duniya. Salim ma ya kusa hauka akanta amman Captain ya goge mata hadda, ta saka hannayenta ta share hawayenta har yanzu jin take kamar dai ba gaske ba ne. Momy ta turo kofar dakin ta shigo ita ma tana kuka.

“Auren nan ba zai je ko’ina ba, Captain da yake da zuciya da saurin fushi kwana biyu ne zata fita ransa, kuma na san Hajiya Turai ba zata yarda ďanta ya aikata wannan abun kunyar ba, aure ba zai je ko’ina zai lalace”

Namra ta mike tsaye da sauri ta shige bandakinta domin bata son Momy ta ga kukanta, ganin take bata cancanci zubar da hawaye akan namiji ba, sai dai wadannan sun zame mata dole ne. Zaunawa ta yi a kasa bayan ta rufe bandakin tana kuka marar sauti. Momy na ganin hakan ta san yar gudaliyar yarta kuka bakinciki take, ita ma sai rauninta ya karu, jikin bandakin ta tsaya tana buga kofar.

“Namra bude kofar karki saka kanki a damuwa kinji, na san babu dadi amman ki yi hakuri karki wa damuwa kofa dan Allah ki kwantar da hankalinki, ni kaina ba zan bar maganar nan ba ba zan kyale lamarin nan ba”

Kalaman na Momy sai suka zama kamar makamashi mai hura wutar bakincikin dake zuciyar Namra, sai dai hakan be saka ta bude kofar ba, har Momy ta gaji da tsayuwa ta fice daga dakin, tana shiga dakinta mayafi ta dauka da key mota ko jaka bata tsaya dauka ba ta nufi family house dinsu.

 

CAPTAIN JAMAL POV.

A hankali ya fara rankwafa yatsunsa har ya jimke dabinon dake hannunsa yana kallon Daddynsa har lokacin an rasa mai cewa komai. Daddy yayi murmushi yana kallon dansa cike da alfahari kamar yadda Captain din ma yake kallon mahaifinsa ya kasa gasgata kalamansa.

“Da alama dai kuna bukatar na maimaita kaina, abun da nake nufi a nan…. ”

Ammy bata bari ya fadi ba ta mike tsaye cikin tsawa da hargagi ta ce.

“No bana bukatar ka maimaita mana sautin da fadij mutuwa ya fi shi dadin ji”

Ta tofar da yawu.

“Touf! Allah ya tsare gatari na da saran shuka, har abada ďana ya fi karfin wulakantacciya yarinyar yar talaka kuma wanda duniya ta gama ganin tsiraicinta Wallahi”

Alhaji Sadiq ya mike tsaye tana dagawa Ammy hannu.

“Hajiya Turai sai dai hakuri amman Wallahi an daura auren Jamal da Hurriya yau, idan baki yarda ba ki kira Nafisa ki tambaye ta”

Ammy ta kalli Daddy da sauri tana son kara tabbatarwa. Captain yayi murmushi ya rufe idonsa har lokacin hannunsa na rike da dabinon ya kasa maida hannun kuma ya kasa sauke shi kasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected