VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Karka shiga, ba a nan zaku kwana ba, na yi magana da Momynku a can zaku kwana ku zo muje”

Be jira cewarsu ba ya kama hannun Hurriya zuciyarsa na masa babu dadi, daman can shu baya son kukan wani ko ganin wani a damuwa balle kuma yaransa, sanin cewar shi ne silar damuwar ya saka shi jin babu dadi gaba daya abubuwan sun zo masa ta yadda be yi zato ba. Ganin Appa ya nufi kofar fita falon tare da Hurriya ya saka Hamad ya bi bayansu, sai da suka fita harabar gidan gaba daya, sannan Appa ya tsaya ya tsayar da yarsa ya daga kanta ta kalleshi.

“Haka zamu shiga bangaren Momynki kina ta kuka Hurriya? Dan Allah ku yi hakuri idan ba so kuke ni ma na yi kukan nan ba, ba ku san abun da yake cikin zuciyata ba, ina cikin wani irin tashin hankali da rudani marar misaltuwa”

Kai kawai ta iya daga masa ta saka hannayensa ta share hawayenta tana ta aikin hade kukan dake neman ya gagari tsayawa a iya bakinta da idonta.

“Ammanku ba mutuwa tayi ba, zaku iya zuwa ku ganta a duk lokacin da kuke so, ita zata iya zuwa ta ganku, Hamad na san kai ne mai zuciya ka sakawa kanka hakuri dan Allah ko dan yar’uwarka”

Ko saitin gurin da Appa yake tsaye Hamad be kalla ba, yadda ya dauke kai yana kallon wani gurin sai ka rantse da Allah ba da shi Appa yake magana ba, domin a yau kam ba shi da abokin tsana kamar Appansa saboda sanin cewar ya rabu da Amma, ko da kuwa ba zai iya fadar abun da ya faru tsakaninsu ba, hausawa suka ce mai lalabe a duhu balle an haska masa, a banza yayi fushi balle an taba shi. Appa ya dauke kai ya rika hannun Hurriya suka cigaba da tafiyar, da kansa ya shiga falon, be zarce ko ko’ina ba sai Stairs kai tsaye ya nufi dakunan da suke gefen bedroom din Momy kamar yadda suke a kowane bangare, ya san dakin Namra da na Musib da Miwan dan haka be taba dakunansu ba ya nufi wani dakin ba dabam ya tura kofar dakin sannan ya saki hannun Hurriya daki ne dake dauke da furniture na mutum daya domin Appa ya saka an zuba furniture an gyara ko wane daki duk kuwa da kasancewar wasu dakunan babu kowa, ba dan komai ba sai dan irin haka ko kuma idan an yi baki ko ma idan yaransa sun yi sha’awar canja daki daga wani zuwa wani. Hurriya ta daga kafarta ta shiga cikin dakin ta isa bakin gadon da zai wadaci mutum daya ta juyo ta zauna ta a hankali tana kallon Appanta dake jan kofar dakin. Gam… Kofar na amsawa gabanta ya yanke ya fadi, gaba daya sai ta ji kamar wata duniyar aka kawo ta, sai ta ji kamar wani gidan da bata san kowa ba kuma bata da gatan kowa a ciki aka kawota. Rabon da ta shiga bangaren Momy ma an dade, babu ruwanta da bangare sai da dalili ita ma Momy bata shiga nasu bangaren ita ta ware kanta dabam a gidan. Dayan dakin dake kusa da na Hurriya Appa ya budewa Hamad

“Nan zai mana Hamad?”

Ya daga kai sannan ya saka kai ya shige dakin da kansa ya turo kofar dakin ba tare da ya jira mahaifinsa ya rufe masa ba. Appa ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya sauka, Namra da Musib suka hada ido suna mamakin yadda Appa ya shigo da Hurriya be ma bari ta zo da kanta ba.

“Musib ina Miwan?”

“Ya fita da magariba nan Appa”

“Namra da Musib dan Allah a zauna lafiya, yaran nan kanenku ne, jini daya ne ku da su, bana son na ji wani tashin hankali ko fada, Hamad dai kun riga kun san halinsa ba sai an fada muku ba, duk wani abun da zai yi ku kawar da ido ni kaina da nake mahaifinsa hakuri nake da shi, Hurriya kuma kun san babu ruwanta da fita dan Allah a zauna lafiya”

Nasiha yake musu amman zuciyarsa cike take da kunci da damuwa narar misaltuwa. Appa ya amsa cike da ladabi

“In Shaa Allahu Appa”

Ya dan motsa kansa kadan alamar gamsuwa sannan ya nufi kofar fita.

“Sai da safe Appa mu kwana lafiya”

“Allah yasa”

Ya amsa sannan ya fice. Yana sakin kofar falon Musib yayi kwafa ya mike tsaye ya nufi stairs Namra ta bi bayansa, ita ta shige dakin Momy Musib kuma ya nufi dakin da zuciyarsa ta raya nasa Hurriyya na ciki. Ya tura kofar dakin kamar abun arziki ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta idonta shar da hawaye.

“Yar gatan Appa, da kansa ya riko hannunsa ya kawo ki, kuma saboda ke yayi ta fada da Momy”

Uffan Hurriya bata ce masa ba, har ya gaji da tsayuwa ya bar mata kofar a bude yayi tafiyarsa. Runtse ido ta yi tana jin wani sabon kuka na zo mata, ta dawo a rakube gurin ta ta san cewar zata sha azaba da wahalar zama, da ma ace bangaren Hajiya Kaltume aka ajeta ko ba komai zata samu sauki ta wani bangaren saboda Yasir, amman a na bangaren ta san babu mai sonta, gaba daya sai ta ji ta zama wata marainiya ashe ba sai da rashin uwa da uba ake maraici ba. Musib na barin kofar dakin Hurriya ya nufi dakin Hamad ya tura, kwance ya hango shi saman gadon ya baya kofar baya, kuma budewar da Musib yayi be saka Hamad juyo dan ya duba ko waye ba. Wani mugun kallo da tsana irin ta yan uba Musib ya jefi kanensa da shi, sannan ya bar kofar dakin shi ma be rufe masa ba, Hamad na jin alamar an tafi ya juyo ya sauko saman gadon ya iso gurin kofar ya rufe ta da karfi ya saka key, Musib da be jima da barin bakin kofar ba ya juyo ya kalli kofar jin yadda aka bugata da karfi.

“Zaka sha wahala yaro”

Yayi kwafa ya nufi dakin Momy sai wani huci yake kamar mace, daman shi ne mai kishin da matan ubansa a gidan sai dai yana boye abun a zuciyarsa, yadda yake jin kiyayyar Iyami da Hajiya Kaltume ko Momynsa bata jin kiyayyarsu haka domin ita sai idan kishin ya motsa mata ne take kula su ko kula wani abu da ya shafesu.

Daren sai ya zamewa Hamad da Hurriya dabam, sanin cewar rabuwa mahaifiyarsu ta yi da mahaifinsu ya hana Hurriya rutsawa har safe, sai ta raya daren da kuka Hamad kuma bayan ya gama nasa fushin bachi ya sace shi. Ta bangaren Appa ma yadda ya ga rana haka ya ga dare, kwanan Hajiya Kaltume ta bangaren be kuranye masa damuwarsa ba, sai ma ya kasa kwantar daga karshe ya koma falo ya zauna ya kunna Tv sai dai kuma babu mafitarsa a cikin kallon kamar yadda babu shi a cikin bacci sai ma karin damuwa, me yasa ya aikata shi ne abun da ya tsaya masa a rai yake ta tambayar kansa, idan kuma ya tuna da abun da yake ji idan tana gidan sai ya ga kamar yin haka shi ne daidai.

Washe gari da wuri Hajiya Kaltume ta tashi, daman duk ranar girkinta da wuri take tashi ta shirya masa abun karyawa, kasancewar bata da mai aiki tun bayan da ta dauki Iyami aiki ta aure mata miji bata sake yarda ko mai sharar gida ta sake dauka ba, sai dai ta yi komai da kanta ba kamar Momy ba da masu aiki ne suke mata komai sai dai ta ci idan kuma ranar girkinta ne sai dai ta dauki na Appa ta kai masa.
Ko da bakwai ta yi ta gama hada masa ruwan zafin tea da gasa masa bread dan ya fada mata tea kawai zai sha baya son cin komai. Yana shan tea yana hamma saboda bachi da ya gagareshi da dare da alama yana neman fansa a yanzu da safiya.

“Wai dazun ina barin bangarenka Hajiya Fatee ta kira ni”

Ya dan juyo kadan yana kalleta alamar ina saurarenki.

“Wai danta Fadeel ya samu tsabani da matarsa shi ne take son na zo”

“Allah ya kyauta…”

Yadda ya amsa mata ya karantar da ita izinin zuwa ne, daman kuma ta san ba zai hanata ba.

“Ameen zaman auren ne na su, zaman lafiya ta gagara Allah ya shirya tsakaninsu”

Appa dai be sake cewa komai ba, har ya shaye tea ya aje cup be taba bread ba. Hakan kuma be yi ma Hajiya dadi ba domin ta san damuwar ba zata wuce ta ƴaƴan Iyami ba ko kuma ta Iyamin ma gaba daya. Ta dauke cup din ta fita ba tare da ta fada masa yanzu ta tafi ba da safen nan. Ta isa bangarenta rike da cup din. A dinning din da duka matansa suke fara cin karo da shi a kowane falo idan suka fito daga bangarensa ta aje cup din sannan ta nufi dakinta, tana shiga ta raba jikinta da tufafin da ta saka da safen nan ta daura tawul ta shiga bathroom, a gaggauce ta yi wanka gudun kar ta yi latti sanin cewar inda za su je kaune dake gaba daji baya daji. Ko da ta fito ta samu Khairi zaune akan gadonta fuska a kumbure musamman bakinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected