Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Mama Kulu ina wuninku”
Ta gaishesu, duk suka amsa mata har Kulu, sannan Hurriya ta ce.
“Mama Kulu wai ki zo”
“Ni”
Ta nuna kanta.
“Eh”
“In ji wa?”
Dayar dake zaune kusa da ita ta saka dariya.
“Ke ma dai da neman tsawaita zance kike, waye zai kiraki duk gidan nan ban da Momy? Kuma tun da kika ga Hurriya a kin san ita take nemanki”
Hurriya dai bata ce komai ba ta juyo ta fara tafiya, a bakin kofar ta tsaya har sai da Kulu ta fito sannan ta tare tace.
“Ba Momy ke nemanki ba, Hajiya”
“Hajiya kuma?”
She asked with shock.
“Eh nima na dawo daga waje na ganta tsaye tace na kiraki kuma kar na bari kowa ya ji, ta ce ki same ta bangarenta magana ce mai muhimmanci”
“Toh… Allah yasa dai lafiya”
Hurriya dai ban da kallonta babu abun da ta yi, domin ita ma bata san dalilin kiran ba balle ta fada mata ita kuma bata daina faduwar gaba ba har ta isa bangaren na Hajiya Kaltume. Daman Hurriya tana isar mata da sako ta shiga bangaren Momy ta bar a guri..
Cikin tsoro ta shiga falon da Momy tana sallama. Ruma ce kadai zaune a falon tana cin abinci, hannu ta sauke ta aje plate a kasa bayan ta amsa sallamar Kulu, ita kanta mamakin ganinta a bangaren take.
“Hajiya na ciki ta ce tana son ganin”
“Eh tana ciki bari na kirata”
Ta mike tsaye tana tsude hannu ta nufi stairs, slowly ta tura kofar dakin Hajiya ta lake.
“Hajiya ga Kulu mai aikin Momy a kasa tana nemanki”
“Je ki ce mata ta shigo”
“Nan eh?”
“Eh”
Ta juya ta koma, tun kamin ta karasa saukowa ta fadawa Kulu sakon Hajiya Kaltume.
“Ta ce ki shigo”
“Na shigo kuma?”
Ruma ta daga mata kai, Kulu ta daga kai ta kalli stairs din da bata taba hawa ba, tun zuwanta gidan, shigarta bangaren Hajiya Kaltume ma za a iya kidayashi domin bata zuwa sai idan Momy ta aikota, kuma ba kasafai Momy take haka ba. Da tsoro Kulu ta taka ta hau stairs sai ta rasa wane daki zata shiga domin duka dakunan a rufe suke kuma bata taba kaiwa gun ba balle ta gane wanene dakin Hajiya Kaltume. Kwatantawa ta yi da dakin Momy sai ta isa bakin kofar dakin ta yi sallama ta kwankwasa.
“Shigo”
Ta murda kofar ta shiga idonta na bayyana tsoronta a fili domin bata san dalilin kiran ba, gashi ance mata magana ce mao muhimmanci kuma har ba a son kowa ya ji. Kusa da kofar ta tsaya ta rigina tana zuba gaisuwa.
“Hajiya ina wuni”
“Rufe kofar ki matso nan”
Ta juya ta kalli kofar sannan ta saka hannu biyu ta rufe ta, ta matsa kusa da Hajiya ta zauna a kasa.
“In ce dai ba wani laifin na yi ba”
Hajiya Kaltume ta kalleta tana murmushi.
“Aa ba ki yi laifi ba for now, na ma kiraki ne na yaba miki, sai dai nan gaba ban sani ba ko zaki yi laifin idan kika biyewa sherin zuciya”
“Hajiya kin saka ni a hudu me ya faru?”
Hajiya Kaltume ta gyara ta kalleta da kyau irin duban nan dake nuna babu alamar wasa a zancenta.
“Ke kika dauki kudin da yake uwar dakinki Nafisa, da sarkokinta da kuma sarkar Namra ko ba haka ba?”
Hausawa suka ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. A take gumi ya karyowa Kulu ta fara hadeye yawu tare da dora hannu akai tana zaro ido.
“Ni Kuma? Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un Allah Wallahi Hajiya… ”
Hajiya ta daga mata hannu.
“Ban ce ki rantse min ba, abun da na sani ne nake fada miki, kuma bana bukatar ki jadadamin, idan kuma kin yi musu zan mu iya zuwa ni da ke da Nafisa da kowa ma na gidan na nuna gurin da kika boye kudin, bayan dakunanku cikin itacen fulawa”
Jikin Kulu ya fara rawa irin rawar nan dake kara bayyana rashin gasjiyarta.
“Kin ga daga nan sai Alhaji ya koreki, daman kuma ita Nafisa na san ba zata kyaleki ba sai ta hadaki da Police, baki ga aikinki ba ki ga kudin da kika sata, kuma ga zubewar mutumci da zuwa gurin yan sanda”
“Hajiya ki rufa min asiri dan girman Allah ki yafe min, ki dubi girman Allah ki rufa min asiri, Wallahi zan maida duk abun da na dauka, dole ce ta saka na sata, shekarata nawa a gidan nan amman ban tana daukar ko akaifa ba balle kudi”
Ta karasa da kuka sosai ko’ina na jikinta yana rawa, ta dayan bangaren kuma tana mamakin ta ina Hajiya ta san da wannan bayan bata fadawa kowa ba, kuma babu wanda ya san gurin da ta binne kudin.
“Ban ce ki maida kudi ba, da ki maida kudi da karki maida kudi duk daya ne a gurina, ni ina ma jinjina miki da kika aikata hakan, domin Nafisa ban da bakar rowa da wulakanci bata aje komai ba, na kira ki a nan saboda na fada miki cewar na sani, kuma na jidadi da baki wahalar da kanki gurin bayyana gaskiya ba, ni nan da kika ganina har duniya ta nade ba zan taba fadawa kowa cewar ke kika saci kudin Nafisa ba ko sarkarta”
“Hajiya ina kika ji wannan magana?”
“Da wa kika yi maganar?”
Ta daga hannayenta sama.
“Wallahi ban yi da kowa ba.. ”
“Karki damu da inda naji, ba wani ya fada min ba, abun da nake son ki damu da shi ne, abun da zan fada miki yanzu”
Ta kara gyara zama tana hade yawu da karfi.
“Toh Hajiya”
“Daga yanzu ina son ki zama karkashin ikona ba ikon Nafisa ba, ita kike yi ma aiki amman ni nake da iko dake, ina son ki saka min ido sosai akan uwar dakinki, kuma nan gaba duk abun da na ce ki aikata zaki aikata shi”
“An gama Hajiya Wallahi an gama.. Komai kike so shi za’ayi”
“Yayi kyau, ke kuma asirinki zai yi ta rufuwa har ki mutu, kuma zan cigaba da biyanki bayan biyan da Nafisa take miki”
“Hajiya ni ba sai kin ba ni komai ba, kawai dai ki rufa min asiri idan kika min haka kin biya ni”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta dauke fuskarta ta dauki wayarta tana latsawa, haka ta kyale Kulu a gurin tana ta share gumi har na kusan minti biyar sannan ta kalleta ta ce.
“Wake share dakin Hurriya?”
“Ni ce Hajiya ni nake sharewa na yi mopping ko’ina na saka turare”
“Yayi kyau da ba ke ba ce zan ce ki karba ki share saboda, aikin da nake son ki fara min a yanzu shi ne, ki shiga dakin Hurriya ki bincike min komai na dakinki idan kika ga wata laya ko wani kullin magani ko wani abun na dabam ki dauko min shi”
“Toh Hajiya amman sai gobe, saboda dare ne yanzu, kuma Momy bata son kowa ya shiga bangarenta idan tana nan”
“Ni ma ban ce ki yi yanzu ba, amman dai ki tabbatar kin samo wani abu karki zo min hannu sake, domin ni na san akwai abu a dakin shiyasa na ce miki ki dauko, kamar yadda na san ke kika yi sata kuma na san gurin da kika boye kudin”
“Toh Hajiya, Wallahi zan yi”
“Shi ke nan tashi ki tafi”
“To na gode Hajiya na gode Allah ya saka da alheri Allah ya rufa mana asiri, Allah ya kareki daga duk shari”
Hajiya Kaltume bata ji zata iya amsa addu’ar ba dan haka bata amsa ba, sai kawai ta daga mata hannu. Kulu ta tashi ta fice rike da zanen da ya kwance kuma ta kasa daurawa sai rike shi da ta yi a jikinta ta sauka haka. Hajiya Kaltume bata sake fitowa dakin ba sai da ta auna lokacin da ya kamata ace Khairy ta dawo cikin gidan sannan ta fito dakinta ta nufi dakin Khairy, sai ta same ta kwance ruf da ciki bandir din 1k a gafenta wayarta ma a gafenta aje. Sai da Hajiya ta gama kallon komai sannan ta zauna kusa da ita ta kai hannu ta taba ta
“Ke Lafiya kike?”
Khairy ta bude ido.
“Lafiya kalau”
“Waye ya zo gurinki?”
“Waya fada miki wani ya zo gurina?”
“Na ga Hurriya na tambaye ta ina ta fito tace min ke ta raka gurin saurayinki, waye wannan?”
Khairy bata son jin magana dan haka ta ce.
“Baki san shi ba”
“Hakan yayi, danan bana son saninsa, domin bana son ganin kowa a tare da ke sai Fadeel”