Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Hurriya yau ji take kamar ta cinye Amma saboda murna?”
Hurriya ta saka dariya tana kallon Rukayya dake taje kanta.
“Mama Rukayya da kun fada min Amma ta fara motsa hannunta da sai na saci hanya na zo”
“Shiyasa ai ba a fada miki ba, ki saci hanya ki zo nan wannan Kalwar ta hada ki da Appanki, kin ga wannan mai fuskar yan wuta kiris ya rage ta shigeta, na tsani kamar nan kamar mutuwata”
“Yanzu ai bana gidanta na koma gidan Hajiya, kin ga zan samu sauki, Hajiya bata hana ni zuwa ko’ina balle ma kuma idan nan ne”
“To ya aka yi kika koma wai?”
“Ita ta rarrashi Appa kuma ya yarda”
“Wata kila ta ga wahalar da kike sha a gidan ta miki yawa ne”
Hurriya dai ta yi murmushi bata sake cewa komai ba, domin bata son a zafafa a maganar. Bayan sun yi Sallah la’asar ta fito tsakar gidan ta zauna tare da Amma, twins kuma suna ta wasansu kamin ta su fado kanta saboda tsokarnasu da take, sai aka jone ita da su aka rasa waye karami, ita da kurciyarta bata gama fita jikinta ko kuma su da a yanzu suke tasowa. Ana daf da fara kiran Sallah Magariba, Hurriya ta shiga ta dauko hijabinta da jakarta domin sun yi da Hajiya Binta zata wuni a nan ammam ba zata kai dare ba.
“Gwaggo zan tafi, Hajiya ta ce kar na yi dare”
“Toh kin koshi dai ko? Idan kuma kina son dan’waken ki tafi da shi”
“Aa na koshi a bawa yan biyu a ciki”
Sai suka saka dariya yana mulmula kan katuwar tabarmar da Gwaggo ta shimfida. Hurriya ta kai kasa tare da kai bakinta a goshin Amma ta sumbanci, goshinta ta sumbanci gefen fuskarta dama da hagu.
“Ina sonki Ammana Allah ya baki lafiya”
Amma ta yi murmushi tana binta da kallon da raunataccin idanuwanta. Gwaggo ta kalli Rukayya dake hankalinta ke kan waya ta ce
“Ba zaki rakata ba? Ke dai kullum kina nan a waya, sai ta saka ki hauka idan baki yi hankali ba”
Rukkaya ta kyalkyale da dariya.
“Gwaggo littafi ne nake karantawa na Khadeeja Candy, mai suna Mairo wai an bata apple ta ce a kara mata gorar binni, wai yan binnni gorabar taushi ne da ita”
“Kyaje can ta shirmenki, kullum ai cikin karatun littafi kike, tashi ki karata ta samu Napep”
Rukayya ta mike tsaye har lokacin dariya take, sai da ta shiga ta aje wayar ta sako hijabinta sannan ta fito tana gyara talkamin kafarta.
“Mu tafi yar gidan Gwaggo, ke ko kishinki bata yi sai fada take min ban raka kishiyarta ba”
“To idan ma ba yar wuta ba, wace kishiyar ce zata yi kishi da Hurriya baiwar Allah, kifi musulmin nama”
Hurriya ta yi dariya, ita kanta Gwaggo dake maganar dariyar ta yi, kamin ta raka da addu’a, Amma kuma ta bita da kallo tana dan murmushi kadan. Tare suka isa da Rukayya har titi suna tafe suna hira, Rukayya sai tambayarta take wai halin Hajiya Kaltume na nan ko ta daina.
“Me zata daina kuwa Mama Rukayya ni dai arzikina, daya bana gidan yanzu duk wani abun da zata fada ko ta yi ba zai shafe ni ba”
“Wallahi kin huta, ai kara da Hajiya Binta ta dauke ki, kika rabu da wannan bakar kalwal mai bakar zuciya”
Hurriya ta kalleta tana murmushi.
“Amman dai Mama Rukayya wasa kike so? Hajiya fa mahaifiyar Yaya Yasir ce”
“And so what? Ke baki ga yadda ta maida Amma ba? Ta mallake Appanku baya jin maganar kowa sai nata? Ni fa da zan samu sa’arta sai na dauko fansar duk abun da ta yi mana, saboda tana tsaye nan a makoshi?”
“Toh kuma ki yi Yaya da Yaya Yasir?”
“Wai ke ina ruwanki da Yasir din ne? Ke fa wata rana kamar munafuka haka kike”
Hurriya bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba.
“Mama Rukayya ke dai yi a hankali, dan kin san Yayana fa, shi yake zane mu idan muka yi laifi”
“To ni sai ya dake ni? Ke yarinya kama kanki, ai ko kirana yayi ban daga ba sai kin ga yadda hankalinsa yake tashi, idan kuma ya zo ya karbi wayata ko ya gan ni da wani ya fara kishi kenan, ni Rukayya i no dey carry last, haba ni ba halin Amma ne da ni ba, kowa ya ce min kule chasss zan ce masa”
A karo na barkatai Hurriya ta yi murmushi, ta tsayar da mai napep ta shiga bayan ta fada masa unguwar da zai kaita.
“Toh Allah ya tsare, damo sarkin hakuri”
“Amin Mama Rukayya na gode”
Mai napep yaja suka dauki hanya. A bakin gate ya sauke ta ta ba shi kudinsa sannan ta shiga cikin gidan, tana yin arba da daya daga cikin motocin da mahaifinta ya fi yawan hawa gabanta ya yanke ya fadi, tun a nan ta fara rage tafiyarta, hakalimlnta be tashin ba sai da ta kunna kai cikin falon ta yi arba da Hajiya Kaltume da Appanta, Hajiya Binta kuma tana zaune saman kujera.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…
Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660
@
2⃣2⃣
“Hurriya an dawo”
Far’ar da Hurriya ta gani a fuskar Hajiya Kaltume lokacin da take fadar haka ya fi daga mata hankali fiye da ganinsu da ta yi a gidan. Cikin rashin kuzari da faduwar gaba ta karasa kusa da Hajiya Binta ta zauna a kasa, sannan ta mikawa Appa gaisuwa.
“Lafiya Kalau”
Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Kaltume na murmushi tana kallon Hurriya irin murmushi na murnar ganinta, bayan kuma a kasan zuciyarta ba haka ba ne.
“Hajiya Ina wuni?”
“Lafiya Kalau mutan aljanna, an dawo? Tun dazun muke nan ai, Hajiya ta ce kin tafi duba Iyami ya jikin nata”
“Tana jin sauki?”
“Sosai?”
“Eh”
“Maa Shaa Allah…”
Ta kasa cewa Allah ya bata lafiya, saboda hausawa suna cewa addu’ar fatan alheri ta makiyi karbabbiya ce, wai idan yayi maka sai an karba. Hurriya ta juya a hankali ta kalli Hajiya Binta dake zaune fuska ba yabo ba fallasa.
“Hurriya an dawo?”
“Eh Hajiya sannu da gida”
“Sannu dai yar Albarka, kin yi Sallah?”
“Aa ina tahowa ne aka yi kira”
“To tashi ki shiga ciki ki yi Sallah ki”
Hajiya Kaltume ta ce
“Ai da ta bari sai mun tafi sai ta yi sallah a can”
“Babu inda Hurriya zata tafi, ai na fada miki tun da ya koreta ta dawo nan kenan idan kika ga ta bar gidan nan to bana raye ne”
A take Hajiya Kaltume ta saka kukan munafurci.