Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Subhanallahi haka Yasir ya fasa miki baki saboda yar iskar yarinyar nan?”
“Ba laifin Ya Yasir ba ne Hajiya, laifin Appa ne yana mugun son yarinyar nan, ya fi kaunarta da duka sauran ƴaƴansa, dubi yadda ransa ya bace saboda na fada mata gaskiya bayan kuma gaskiyar ce”
“Hmmm ai ni ganin nake kamar ba banza uwar yaran nan ta bar Alhaji ba, ita kanta ai ba a banza ta aure min miji ba, yanzu kuma saboda yaran nan Allah kadai ya san ran mutun nawa zai ɓace a gidan nan”
“Wallahi sai na rama komai ta dade”
“Toh ki rama dai ta sigar lalama, in ba haka ba Alhaji ko Yasir su ci ubanki kin san jira kawai suke”
Ta tashi ta fice dakin tana wani zakuɗa ita ga balagaggiya. Hajiya ta shirya cikin koriyar Atamfa ta saka farin mayafi ta sauki jakarta mai kala daya da gyalen da kuma talkaminta ta saka sannan ta dauki wayarta ta kira daya daga cikin drivers din gidan ta sanar masa fitarta. Gurin da take aje kudi ta bude ta dauko kudi mai yawa ta zuba a jakarta sannan ta rufe ta rataya jakar ta fito rike da wayarta sai kamshi take zubawa irin na manyan matan masu kudi kuma masu miji da ikon gida.
“Hajiya fita zaki yi?”
Maama ta tambaya.
“Eh wani guri zamu je da Hajiya Fatee”
“Allah ya tsare, Hajiya kin ga yadda Ya Yasir ya fasa bakin Khairi”
“Na gani, ku ma sai kun yi taka tsantsan ai, ni ba dan ubansu daya ba ai sai na tsora ta na ce aurenta yake son yi”
“Lallai ya fi sonta da mu ma”
“Hmmm Allah dai ya kyauta, ki tashi sauran yan ‘uwanki kar su yi latti makaranta, ni na fita”
Daga haka ta fice daga falon Maama na yi nata Allah ya tsare. Ko da ta fito direban har ya tashi motar ya juyata tana fuskantar gate domin ya san uwargidan Alhaji Haruna Mai Yadi bata daukar raini. Tana shiga motar be tsaya da ita ko’ina ba sai gidan aminiyarta Hajiya Fatee, yana aje ta ya juya a can ma ba su bata lokaci ba, Hajiya Fatee ta kira direban dake kai su kauyen ta sanar masa sun shirya, ba su yarda su tafi da motarsu ba saboda tsoron masu kidnapping da kuma tonon asiri, sai dai su dauki shatar motar kasuwa ta zo ta dauke su har gidan Hajiya Fatee ta kaisu inda za su je, kasancewarsa mijin Hajiya Fateen ya dade da rasuwa ita kadai ce a katon gidan sai yan matanta biyu da kuma masu aiki da danta Fadeel ya zuba mata.
Misalin karfe tara da rabi na safe suka kama hanyar kauyen gidan zalla dake cikin local government din Kwatarkwashi. Suna tafe suna hira Hajiya Fatee na kara fada mata yadda matar danta Afrah ke son mulkar mata ďa ta saka shi ya manta da ita. Idan ta kai aya sai Hajiya Kaltume ta dauko nata zancen na abun da ya faru tsakaninta da Alhaji a jiya. Sanar da shi da suka yi cewar suna nan tafe ya saukaka musu wucewa kai tsaye dakin da yake gabatar da tsiface-tsifacensa. Sai da ya fara yi musu maraba da zuwa sannan Hajiya Kaltume ta ciro kudi 300k ta aje masa tana masa godiya.
“Aiki yayi Malam, dan haka na zo da kaina na kawo maka goronka, kuma na yi maka godiya”
Malamin da hakoransa ke daskare da jan goro ya yi dariyar jindadi da farinciki ya jinjina kai.
“Hajiya ai na fada miki, indai muka yi aiki ba a dawo mana da shi, kuma kar tunanin kin yi kin yi baki dace ba yasa ki karaya a gurinmu, idan kin ji ana malam anjima da nisa ba ma gobe da nisa ba to kika zo nan kakarki ta yanke saka kawai”
“Na gani ai Malam Wallahi na gode, domin shekara da shekaru ina neman yadda matar nan zata bar min mijina amman abu ya garara sai an yi kamar za a rabu sai kuma ka ga ba rabuwar bace, sai yanzu Allah ya kawo karshen abun, sai dai ko yanzu ni ina jin tsoro domin na lura ya shiga damuwa matuka gaya saboda sakinta da yayi, ina jin kar ya ce zai dawo da ita domin saki daya yayi mata”
“Ina ko alama! Karki damu Hajiya, idan har mutum zai mutu ya dawo to kishiyarki zata dawo gidan, ai farraqu muka musu ita tana gabam yana yamma har abada ba zama a tsakaninsu”
Wani kalar dadi ya lullube Hajiya Kaltume.
“Haka nake so, kuma ina son a koya mata hankali so nake ka yi mata wani aikin da ba zata sake aure ba har abada, tun da ta zabi kishi da ni to ko bayan ta bar gidan mijina sai ta dandana bakincikin da nadanar auren Alhaji da ta yi, sannan be sake ta sai da ya damka mata kudi har miliyan asirin, Malam ina son a lalata duniyar da ya bata, har da gidan da ya mallaka mata idan akwai yadda za’ayi a ruguza gidan ko ma ya karbe abunsa, kuma a daureta ko kare kar ya sake sha’awarta balle har ta yi aure”
“Wato so kike a lalata duniyar da ya bata, ba wadda ya bata kawai ba, har tata duniyar da ta mallaka za a iya lalatawa idan kina so”
“Aiko idan ka yi min haka, ina mai tabbatar maka aikin Hajji bana da kai za’ayi, kuma zan maka kyautar kudi har naira miliyan daya”
Malamin ya sake yin dariya yana gyara babbar rigarsa.
“Hajiya na miki alkawari akaifa kishiyarki ba zata sake amfana da ita ba, ba duniyarta ko ta mijinki da ya bata ba, har dukiyar wani idan ya dauka ya bata ba zata taba amfanarta ba, ita da aure ko sai lahira idan ana yi, kuma yadda ba a mutuwa a dawo haka ba zata sake dawowa a gidan mijinki ba”
“Alhamdulillah”
Hajiya Kaltume ta fada tana daga hannu sama ta yi ma Allah godiya, sannan ta kalli Hajiya Fatee suka taba suna dariya. Daga bisani Hajiya Fatee ta kora masa da nata bayanin.
“Malam nima da tawa mtsalar na zo yau, suruka ce ta saka ni a gaba, ta mallake min ďan yaki ya kara aure kuma baya jin maganar kowa sai ta matarsa, ga kudi yana da shi amman ko kyauta zai yi sai abun da ta so yake bayarwa, ni so nake a raba su ya sake ta saki uku idan da dama”
Malamin ya amsa mata da kai.
“Ya sunanta, ya kuma sunan ďanki?”
“Afrah ake kiranta, shi kuma Fadeel”
Ya dauko kasa dake cikin farantin katako ya dora a cinyarsa yayi zane zane ya jinjina kai ya dago ya kalli Hajiya Fatee.
“Lallai sai kin tashi tsaye, ta mallaki danki Mallaka bata wasa ba, kuma idan ba ki yi da gaske ba abu ne mai wahala ya sake yin aure ko da kuwa ta mutu”
“Ka ji irinta ba, shedaniyar yarinyar na sha wahalar yarinyar da can babu ruwansa da ni ma, sai da na tashi tsaye, dan abun da ubansa ya bar min duk a can ya kare, ba dan Allah yasa nasa gadon yayi albarka kuma ya samu babban aiki ba da yanzu mun kade”
“Toh lallai dai gata nan ko yanzu a tsaye take akan danki”
“Dan Allah a zaunar da ita, idan da dama ma a kwantar da ita a saka ta bacci ko a sumar da shegiya”
Malamin yayi dariya
“Ai tun da kika zo nan komai zai zama tarihi Hajiya, ki bada kudin karan alkamin kawai a saka aiki”
Da sauri ta bude jakarta ta dauko kudin da ba zai wuce 30k ba ta aje masa.
“Ga wannan ban zo da kudi mai yawa ba, amman dai a fara saka aiki da wannan idan zan dawo zan ciko jaka da yardar Allah”
“Toh shi ke nan ba matala idan na gama aiki na hada abubuwa zan kira na fada muku sai ku zo ku karba ko kuma ku aiko ko kuma ni da kaina na aiko muku”
A bisa wannan suka yi masa sallama suka fito suka dawo cikin motar. Direban ya a kama hanya, ba su yi nisa da garin ba suka rage gudu ganin an tsayar da motocin dake gabansu a zatonsu sojoji ne, hankalinsu be tashi ba sai da suka fara jin harbe harbe wasu na ihu.
“Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un Bandits ne”
Direban ya fada, da sauri Hajiya Fatee ta kalli Hajiya Kaltume da cikinta ya soma murdawa.