VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ba zan mata magani ba, amman Allah zai mata”

Yasir yayi sauri cire hannayensa aljihu.

“Rukky Please aa karki fara abun da ba halin ba”

Ta kalli Yasir sai kuma ta dauke kai ta rika hannun Hurriya suka fice daga falon, Hajiya ta bita da harara da maganganun kala kala.

“A dare kamar wannan yarinya budurwa ace bata gidansu, kuma ta shigo nan tana neman fada min magana ita marar tarbiya”

“Haba Hajiya Rukayya tana da tarbiya Wallahi dan Allah ki daina fadar haka, kuma baki san abun da ya kawota ba, be kamata ku samu tsabani da ita ba, ni zaku haifar da matsala”

Yana magana fuskarsa a raunace kamar zai yi kuka. Sannan ya bi bayansu yana jin Hajiya na jan tsaki.

A waje Hurriya sai rantsuwa take yi ma Rukayya na cewar bata san yaron ba, amman saboda shi Appa ya rufeta da fada.

“To miyasa ba zaki bude baki yi magana ba, idan kina irin wannan zaman sai kin cutar da kanki, ba zaki bude baki ki yi magana ba sai ki zauna kina kuka, ko da kina da gaskiya a rashin gaskiyar za a baki”

“Basa bari na yi magana kuma idan na fada basa yarda”

“Amman duk abun da ba halinki ba ai an san ba halinki ba ne”

“Toh sarkin masifa me kike karanta mata?”

Rukayya ta juyo ta kalli Yasir da isowarsa kenan gurin, shi ma kansa yau sai ya bata haushi saboda abun da mahaifiyarsa ta yi. Bata ce masa komai ba ta kalli Hurriya

“Daman na fito daga gidan Anty Hauwa ne na ce mai napep ya biyo ta nan zan duba ki”

Hurriya ta rike hannunta tana jin kamar ta bita amman ba hali.

“Zan sallami mai napep din sai na sauke ki gida”

“Aa na gode yanzu zan tafi”

Ta saki hannu Hurriya ta fara tafiya sai ya kirata.

“Rukky”

Ta juyo ta kalleshi.

“Na ce zan sallami mai napep zamu sauke ki gida tare da hurriya daga nan ta duba Amma”

Bata son tace masa no, kuma ta san Hurriya zata so ganin Amma domin ta dauki lokaci bata saka ta a ido ba, ko da tace zata je sai Appa ya hana saboda Hajiya Kaltume tace zuwan da take tana tafiya ne dan ta fadi karya da gaskiya.

“Tahm”

“Hurriya shiga ki dauko Hijabinki”
Ya fada sannan ya nufi gurin motarsa ya ja motar ya iso har gurin da Rukkaya take tsaye, bata shiga motar ba sai da Hurriya ta fito sanye da dogon hijab dinta har kasa, sannan ta bude ta shiga front seat Hurriya ta shiga baya, ya fara driving suka fito gate a nan ya sallami mai Napep din sannan ya ja motar suka kama hanya.

“Rukky please bana son wani abu marar dadi yana shiga tsakaninki da Hajiyata, idan ma ta fada miki wani abu marar dadi ko ta yi miki abun da bw dace ba, ki danne ina son ki dauke ta kamar mahaifiyarki, saboda ni kuma ina tunanin ina da alfarmar da zaki yi haka a gareni”

Ta hade yawu can cikin ranta take cewa Allah ya tsare ta Hajiya Kaltume ta zama uwarta.

“In Shaa Allah”

Ya kalleta yana murmushi.

“Thank you”

Ita ma ta mayar masa da murmushin daga haka be sake cewa komai ba ita ma kuma bata sake cewawa har suka isa gidan. Hurriya ce ta fara budewa ta fita motar Rukayya na kokarin fita Yasir ya shigo ya dakatarda ita.

“Ina zaki je?”

Ta masa kallon rashin fahimta.

“Gida mana…”

“Ni kuma sai ki bar ni a nan?”

Ta yi dariya.

“To ka fito mu shiga gidan bakonka ne?”

“Ki dai tsaya mu yi hira ko raina zai saki ni raina ma duk a bace yake”

“Waya bata maka rai Hurriya?”

“Idan kina son jin labari zauna”

Ta yi murmushi sannan ta dawo ta zauna ba tare da ta kalleshi ba.

Hurriya na shiga cikin gidan ta fada dakin Gwaggo da sallama da muryar dake nuna alamar kuka ta yi. Amma na jingine jikin kujera ita kadai a falon tana fuskantar tv dake falon, ta dan karkato kadan ta kalli Hurriya. Hurriya ta isa gurin sai ta kwanta saman jikinta ta fara hawaye, bata son ta fada mata abun da ya faru saboda kar ranta ya bace gashi ba magana take ba balle ta bata shawara.

“Amma na Allah ya baki lafiya, Allah ya tashi kafadunki”

Ta cikin Amma ta iya amsawa da ameen ta kwanto da kanta saman kan Hurriya ta rufe ido. Gwaggo ta fito daga dakinta tana mata maraba.

“Yau Hurriya ce a gidan nan kuma da dare, amman dai Alhaji be san kin zo nan ba ko?”

Hurriya ta dago hawaye shakaf a fuskarta ta kalli Gwaggo.

“Be sani ba, Ya Yasir na biyo zamu kawo Rukayya ne”

“Daman tace sai ta biyo ta ganki, na dauka ma can zata kawana gidan Hauwa, saboda na ga dare yayi sosai”

“Tana waje ita da Yaya Yasir, Gwaggo zo”

Hurriya ta kama hannunta suka koma cikin dakin, ta zauna bakin gado Gwaggo ma ta zauna daman tana ganin ruwa hawaye a fuskarta ta san akwai abun da ya faru.

“Wani abu aka yi Hurriya?”

“Sheri aka yi min Gwaggo…. ”

Ta labarta mata abun da ya faru, sannan ta dora da abun da mahaifinta yayi mata recently before birthday Khairi.

“Appa ya siyawa kowa sabon kaya na birthday din Yaya Khairi amman ni Hajiya tace kar ya siya min ina da kaya da yawa, na masa magana sai yayi min fada, Gwaggo yanzu Appa baya so na ko kadan idan na matsa kusa da shi sai yayi ta min fada, zaman gidan ba ya min dadi kowa tsarguwata yake”

“Ki yi hakuri Hurriya zalinci be taba doreba, kuma komai yana da iyaka wata rana sai labari, ke dai ki yi ta addu’a ki yi ta fadawa Allah matsalarki zai magance miki ita, mu ma muna nan muna yi kuma akwai wani littafi da na siya miki na addu’o’i mantawa na yi ban bawa Rukayya ta kai miki ba”

Gwaggo ta tashi ta nufi gurin da ta aje littafin husnul muslim ta dauko ta mika mata.

“Addu’o’i ne da suka zo daga bakin Annabi Muhammad, karki yi wasa da su, domin ba mu san me za a sake jifanke ko mahaifiyarki da shi ba, kuma duk abun da zaki ci ki yi bismillah, sannan kar tsoro ya saka a baki wani abun da aka san an cutarwa ne ki ci ko ki aikata, yanzu girma kike yi ya kamata ace kina kara wayo”

Ta share hawayenta

“Na gode Gwaggo”

“Ba komai Allah dai ya tsareki, kuma ina kara gargadinki ban da sakaci da addu’a, kin ga rashin daukar addu’a da muhimmanci ne ya jefa Iyami a halin da take yau, sannan kuma zan karbo miki maganin tsari akwai wani mai bada taimako na yi magana da shi ya ce sai an ba shi 150k sannan zai fara yi na Iyami aiki, ya fada mana jefa ce aka yi mata mai hatsarin gaske, kuma idan ba mu yi fa gaske ba zamu rasata”

“To yanzu ina za’a samu 150k Gwaggo?”

“Ina nan ina ta kokari Hurriya, idan kuma haka bw samu ba dole gidan nan zamu siyar mu nemi karamin wannan mu siya sauran kudin sai mu yi maganin da su domin lafiyarta ta fi mana komai”

“Amman idan aka yi zata warke Gwaggo? Kin san ana ta yi amman babu wani sauyi”

“Muna fatan haka, shi dai mutane da dama sun karba kuma an dace, mu ma muna fatar mu dace wannan ciwon nata ya isheni Allah kadai ya san abun da take ji a ranta, ina fatar na ga ta warke kamin na mutu”

Cikin kuka Gwaggo ta karaso maganar ita kanta a yanzu bata da wata damuwa da ta wuce ta Iyami. Hurriya ta tashi rike da littafin ta fito sai ta tsaya daga bakin kofar dakin tana kallon Amma dake kallon kofar dakin tun da suka shiga ciki, wasu hawayen ne suka subuce mata sai ta fashe da kuka. Amma ta girgiza mata kai tana jin kamar ta yi mata magana a dama, shigowar Rukayya ne ya saka Hurriya boye fuskarta Gwaggo kuma ta taso ta fito daga dakin tana fada.

“Wane irin abu ne zaki je ki zauna har dare haka Rukayya”

Yasir dake bayanta yana sallama yayi saurin tare mata fadan.

“Tun isha’i take nan kofar gida Gwaggo laifina ne ni na tsayar da ita, ayi hakuri dan Allah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected