Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Bayan sun gama wayar Bappa ya ce.
“Allah yasa dai yaron nan yana raye, na ga duk kokarin da muka yi sun ki yarda su ba mu shi mu yi magana”
Amma ta girgiza kai.
“Yana nan raye Bappa, yana raye In Shaa Allah”
“Yanzu waye zai shiga wannan guri ya kai kudi mai yawa haka? Ai shi ma sai su rike shi kamar yadda suka yi ma kanen Hajiya Kaltume, ni dai da zaki hakura mu ga abun da hukuma za su yi, ko kuma idan za a je kai musu kudin aje tare da police”
Bappa ya kalli Gwaggo dake maganar ya ce.
“Baki ji sun sake jaddada mana kar mu kuskura saka police a ciki ba, kai kuma kuma zan iya zuwa na kai, indai za su sako yaron nan hankalin kowa ya kwanta zan aikata haka, kawai ku yi ta mana addu’a”
Cikin yanayin damuwa Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya.
“Kowa ke da hannu a cikin lamarin Allah ka wulakanta shi ka tona asirinsa”
“Ameen”
Bappa ya amsa. Gidan da Appa ya bata a lokacin da zai sake ta aka fara sakawa a kasuwa, domin filayen da ta mallaka guda biyu a gidan Appa ta san idan ta saka su a kasuwa ba lallai ne ayi saurin siya kamar gidan da yake gyararre ba, duk da haka kuma sai da aka siyar da shi a nakashe, gidan da zai yi miliyan 45-50 aka siyar da shi a miliyan 35 ta hada da kudin da Appa ya bata da dan abun da take da shi ciki har da sarkar gold din da Appa ya siyawa Hurriya duk ta siyar ta hada kudin ta bawa Bappa, ranar da za aje kai kudin babu yadda Gwaggo bata so a saka police a cikin lamarin ma amman Amma ta ki yarda ganin take idan aka yi haka an bata lokaci kuma za su iya kashe mata da kamar yadda suka yi ikirari, Gwaggo kuma na ta ganin rautar Bappa da Amma taya za a dauki kudi mai yawa haka a shiga daji a kaiwa barayi ba tare da sanin sami’an tsaro ba, abu dai kamar a shirin film.
Cikin karfin hali da yarda da kaddara Bappa ya shiga dajin tare da wani dan’uwansa, bayan yayi addu’o’in da be san adadinsu ba, Gwaggo da Amma, Rukayya da duk wani dan’uwa ma suka raka shi da addu’a. Dan’uwa ya tsaya daga waje shi kuma ya shiga ciki ya kai kudin ya aje a gurin da suka bukata. Har ya kai ya fito babu abun da ya same shi, a lokacin da ya fito ya kira gida ya fada musu ya fito sai kowa yayi ta hamdala ana jin sanyi. Kamin hankali ya karkata gurin ganin kiransu ko sakon inda za su ce a je a dauki Hamad amman shiru. Daga bisani suka bi sawun kiran da number da suka kira da ita last time, domin kullum canja number suke idan za su kira. Haka aka kwashe two days babu kira daga garesu kuma babu wani sako kuma idan aka kira wayar bata shiga, hankali Amma sai ya kara tashi, ta kai bata iya cin komai rashin lafiya ta taso mata har sai da aka kwantar da ita asibiti kowa yayi zaton haihuwa ce duba da tsohon cikin da take da shi, sai dai likitocin sun tabbatar musu ba haihuwa ba ce hawan jini ne, har suka so riketa saboda jinin nata ya hau sosai kuma bata iya cin komai sai dai ruwan da suke saka mata suna taimaka mata ta bangaren kuzari. Sai dai yadda ta nuna bata son zaman asibitin da kuma rokon da aka yi ta musu sannan suka yarda suka sallame ta bayan sun fada musu cewar a rika kokarin kwantar nata da hankali if not idan ta zo haihu zata iya samun matsala ta kasa haihuwar da kanta ko ma arasa danta ko ita ko a rasa duka. All zaman da ta yi asibitin Appa be zo ya dubata ba, even for once be daga waya ya kira ya ji jikinta ba, Hajiya Binta kan kwana ne kawai bata taba yi aabitin ba amman kullum can take wuni, babu yadda bata yi ba Appa ya zo ya duba tsohuwar matarsa, na dan Hurriya da Hamad kadai ba har dan cikinsa da take dauke da shi, amman ya kasa zuwa bayan be saba mata musu ko jayyaya mai tsauri haka ba. Yaran Kaltume ma babu mai mata fatan tashin sai na mutuwa, Yasir ne kadai yayi ta zirga zirga a asibitin gurin dubata ta kuma biyan duk wani bills na magani ko na gado, Namra ma taje duba sau daya tare da wata Neighbor dinsu kawar Hurriya da suke good time da ita, shi ma a sace domin idan Momy ta sani sai ta karya kafafuwanta. Hankalin Hurriya ya tashi sosai ta fara nata zazzabin a tsaye, tunanin sai ya hade mata biyu tana ganin kamar zata rasa mahaifiyarta ta kuma rasa dan’uwanta ne a lokaci daya.
Washe garin ranar da aka sallamo Amma asibiti bayan ta shafe kwana biyar a asibitin, Yasir ya zo gidan sake dubata yake musu albishir da cewar Appa zai bada kudin a yau, sun ce a yau din nan za su fadi gurin da za aje a dauko Hamad da Ruma.
“Kai.. Allah ka sasauta mana mutanen nan ba su da imani ko kadan, yanzu bayan kudin da suka karba gurinmu kuma za su za su karba?”
Cewar Gwaggo tana ta juya zancen.
“Wallahi kuwa, ni da kun yi shawara da ni ba za ku bada wannan kudin ba, komai dai ta kama daman na san dole Appa zai biya kudin”
Rukayya ta kalli Yasir tana masa alamar yayi shiru ta ido.
“Kasan jiya muka dawo daga asibitin nan kuma ta nanata zancen nan sai ku saka ranta ya bace”
Amma ta kalleta tana murmushi.
“Rukayya kenan, rai ba zai bace ba dan na bada kudin, ni dai burina su dawo min da ďana”
“In Shaa Allah, zai dawo inda ba sun yaudare mu ba to zai dawo yau din nan tare da Ruma”
Hindu ta kalli Yasir dake maganar ta yi masa tambaya.
“Waye zai je ya kai kudin?”
“Rilwanu me zai kai, yace zai iya zuwa domin gurin da suka fada hanyar garinsu ce yana yawan bi ta gurin?”
“Waye haka dan’uwanku ne?”
“Eh da yake ga Hajiya ta bangaren kanenta”
“Allah sarki Allah yasa su cika alkawari”
“Ameen”
Daga haka babu wanda ya sake wata magana a falon, har Yasir ya mike tsaye ya yi musu sallama ya fice. Hindu ta kalli Rukayya ta ce.
“Je ki raka shi mana”
“Anty Hindu ban saba yi masa rakiya ba”
“Toh ki fara daga yau, je ki raka shi mana, daga can ba sai ki jiyo mana wani labarin ba”
Tashi ta yi ta bi bayansa ba dan ranta ya so ba sai dan ba zata iya musawa kawar Yayarta ba. Ko da ta fita yana tsaye bakin kofar tsakar gidan tsaye yama jiranta kamar ya san zata fito. Suna hada ido sai yayi murmushi ya juya ya cigaba ta tafiyarsa ita kuma ta bi bayansa har gurin mota, ta tsaya yana juyawa kunya duk ta rufeta.
“Ke lafiya kike?”
“Lafiya kalau sai anjima”
Ta juya da sauri ta bar shi tsaye ya bita da kallon mamaki, before murmushi ya baibaye fuskarsa. Misalin karfe hudu na yamma Yasir ya kira wayar Amma yayi mata bushara da cewar an kai kudin kuma sun fadi gurin da za a je a dauko su Hamad da Ruma yanzu haka suka hanyar daukosu tare da Kanen Appan Alhaji Sa’idu sai kuma Kawu Garba wani dan’uwan Hajiya Kaltume da kuma Yasir din duk a mota daya.
“Alhamdulillah”
Amma ta bada tana sauke wayar, jikinta ya hau tsuma ma dadi farin ciki ya ziyarci zuciyarta ya mamaye ilahirim jikinta, dan zazzabin da take ji sama sama da rashin kuzari duk sai ta neme shi ta rasa. Hurriya ta mike tsaye da sauri tana murna.
“Amma zan hau Napep na tafi gidan yanzu ina son Hamad ya dawo ina nan”
“Ai ni ma ba zan iya jira a nan ba, kira Gwaggo na fada mata”
Hurriya ta fita dakin da sauri ta kira Gwaggo, a nan murna ta kaure Gwaggo sai Hamdala take, ta waya Gwaggo ta fadawa Bappa halin da ake ciki, sannan ta dauki permission din fita tare da Iyami, sanin yadda ďa da uwa suke ya saka Bappa ya amince su tafi ba dan wannan babban dalili ba ba zai taba yarda dayansu ya sake takawa gidan ba, domin be manta cin mutunci da kuma wulakancin da Appa yayi masa ba. Gwaggo da kanta ta fita makota ta samo direban da zai tukasu a motar Amma domin bata iya tuka mota yanzu ita kuma ba iyawa ta yi ba, haka ma Rukayya balle kuma Hurriya da bata gama girma ba ma. Gwaggo da Amma suka shiga baya, Hurriya ta shiga gaba aka bar Rukayya tsaron gida, ba su isa gidan ba sai da suka biya suka dauko Hindu domin dazun kamin ta bar gidan ta fadawa Amma idan aka dauko Hamad a fada mata.