VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Misalin karfe goma sha biyu na rana Maryam da wata yar’uwarta suka sauka airport din sokoto, Appa ya aika da mota a sirrance aka daukosu tun daga sokoto har garin Gusau, bata samu isowa gidan sai karfe biyu da rabi, saboda yanayin tafiya. Ko da ta shigo gidan yana cike da mutane kamar jiya, masu zuwa gaisuwa da gaske da kuma masu zuwa cin abinci, ta fito motar tana sanye da mask sai doguwar rigar Abaya da ta rufe jikinta kovina ruf. Cousin dinta ta ma ta fito motar kowacensu tana rike da jaka, suka shiga bangaren na Hajiya Kaltume, tun a waje suka gaisawa da mutane suna musu ya hakuri har suka shiga can ciki gurin Hajiya Kaltume dake kwance a kan gado zazzabin na dawainiya da ita. Sosai Maryam ta yaba halin kawarta na kirki tana kukan rashinta, ita kanta mutuwar ta taba ba kuma ta zo mata bagatatan a lokacin da ba ta yi tsammani ba, na ita kadai ba mutuwar Salma ta bawa kowa mamaki, ko da yake ba a mamakin ikon Allah, sai dai jin cewar tana lafiya kalau gashi bata dade da gama karatu ba, ya saka kowa tausaya mata. Bayan Maryam ta yi gaisuwa sai kuma ta yi kuskuren gabatar da kanta a gurin Hajiya Kaltume saboda ta san wacece ita, ba dan tana son auren mijinta ba sai dan abotar dake tsakaninsu da Salma.

Hajiya Kaltume dake kwance ta tashi zaune ta gyara hijabinta tana kallon fuskar Maryam.

‘“Daman ke ce yarinyar?”’

Maryam ta dago ta kalleta, ba ta yi zaton Appa ya fada ma Hajiya komai a game da maganar aurensu ba, domin shi da kansa ya bukaci su bar maganar a sirrance har sai idan an daura aure sannan kowa ya ji, ta dayan bangaren kuma bata zaton Salma zata boyewa mahaifiyarta wacece ita saboda ta gargade tun a ranar da suka yi bankwana a airport.

“Ke ce yarinyar da kika haddasa mata bakinciki?”

Maryam ta maida kanta kansa tana jin kunya na rufeta. Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana jin kamar da wuka a kusa da cakawa Maryam ta kasheta.

“Ke ce fitsarriyar yarinyar da kika hakikance sai kin auri ubanta? Duk saboda ku yata ta mutu, ke da Iyami ba za ku gama da duniya lafiya ba, Allah ya tsine muku albarka”

Maryam ta san wacece Iyami domin tana labarin yadda gidan Appa yake ciki da waje, ba ta gurinsa ta ji ba ta gurin bincikar yadda rayuwar gidansa take ta ji.

“Shi ne saboda baki da kunya kika dauko kafa kika zo yin murna ko?”

Maryam ta dago da sauri.

“Subhanallahi wake murnar mutuwa? Ni kawar Salma ce ba makiyiyarta ba”

“Kawarta ba zata ce zata auri ubanta ba, mugun kwadayi da dogon buri ya saka zaki auri ubanta tsohon da ya isa haihuwarki, kin ji kunya yarinyar kin ji kunya rayuwarki zata lalace nan gaba, na rantse da Allah sai kin wulakanta”

Fada sosai Hajiya Kaltume take yi, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ana riketa ana rufe mata baki amman ta kasa daina saboda zafin mutuwar yarta da take ji, ga kuma silar komai a gabanta tana gani ita tana raye. Hajiya Fatee dake waje ta taso ta shigo cikin dakin ta ita da mutanen dake waje ciki har da Hajiya Binta. A fusace Maryam ta mike tsaye cikin masifa ta ce

“Miye laifina dan na zo gaisuwar yarki? Tun daga garin Naija na taso na zo garin nan saboda gaisuwar Salma, akan wane dalili zaki tara min mutane, to bari jiki na fada miki kanki kika tonawa asiri, domin wanda be san mijinki zai kara aure ba yau ya sani, kin kunyata kanki da mijinki”

Tana aje aya Maama ta dauke ta mari, ta kai hannu zata rama Khairy ta rike suka fara dukanta, cikin karfin hali ta fara ramawa ita da cousin dinta aka hau rabasu daker aka kwaci Maryam hannun Maama da Khairy. Hajiya Binta ta dakawa Hajiya Kaltume tsawa

“Wai ke kan kanki farau aure? Wane irin mugun kishi ne yake damunki? Kina babba amman baki san ki tsawatarwa yayanki ba sai dai ki bude musu kofa?”

“Hajiya Karki kara min bacin rai, daman kullum goyon bayan dakinki kike baki tana ganin farina ba, ai ni ba wani abun na yi miki ba amman kika dauki tsana da kiyayar duniya kika dora min, ko wani abun na tare miki?”

“Magana kike ta rashin hankali da tunani Kaltume, ashe mutuwar Salma bata isheki ishara ba? Girma kike kina cin kasa? Jiya ma danki sai da ya kuka min akan abun da kika yi ma Rukayya, yaro yana son yarinya amman kina neman shiga tsakaninsu saboda bakin kishi da ba zai haifar miki da komai ba? Yanzu kuma kin zo gaban mutane kina kunyata mijinki akan abun da baki da tabbaci? Kuma ko da kina da tabbaci ya kamata ki ci mutuncin yarinyar da ta dauko kafa daga nesa ta zo miki gaisuwa? Kim kunyata kanki kin kunyata mijinki. Shiyasa kullum nake yabon Iyami kun fita shekaru amman ta fi ku hankali, wannan abun da kike yi hauka ne?”

“Hauka ne Hajiya, idan kina da magani sai ki ba ni, na gaji da abun da kike min, ba ba ku san me nake ji a zuciyata ba, ba kussn yadda yata ta rasa rayuwarta kun saka ni gaba kuna kunna min wata wutar, na yi kishin kishin halak ne, ni na auri Haruna tun ba shi da komai har ya zama komai, ni nasan fadi tashin da muka yi na rayuwa”

Hajiya Binta ta nunata da tsaya rai a bace.

“Karya kike ki fada min wannan, tun kamin a haifeki na ke kula da dana, ni na san fadi tashinsa ba ke ba, ke kullun kara hauka kike ba hankali ba yayanki ma gasu nan kin fara koya musu irin tarbiyarki”

Hajiya Kaltume zata sake yin magana wata yayarta ta rufe mata baki, tana bawa Hajiya Binta hakuri.

“Babba babba ne ko yayane, dan Allah Hajiya ki yi hakuri, wani lokacin Kaltume bata iya rike halshe, kar idonki ya rufe Hajiya ayi babu dadi a nan?”

“Babu dadi na nawa kuma? Ita da yarta ta mutu idonta be bude ta yi hankali ta natsu ba? Me ye bata fada min ba? Ai wannan yar bata da albarka sam…”

Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta daki kirjinta dake mata zafi da ciwo a lokaci daya tana kuka mai karfi ta ce

“Ba yar albarka ba ce ni Hajiya Binta, ki aura masa yar albarka ki kawo, ni kuma ki saka bindiga ki halbeni ni da yayana”

Hajiya Binta ta kashe ido tana kallon surukar dake mata rashin albarka ta ce.

“Idan kin kwana da aure yau Kaltume na kwana a mace…! Sai na nuna miki ruwan nono ya fi karfin wulakantawar”

Hajiya Binta ta kalli Maryam da ke tsaye gefe daya tana karewa Khairy da Maama kallon daukar fansa ta ce.

“Wuce mu tafi yarinya…”

Maryam ta juya ta fice tare da Cousin dinta, Khairy da Maama kuma suna jin kamar su rufe Hajiya Binta da duka babu hali, Ruma ce kadai ke rusar kuka saboda abun da ke faruwa baya mata dadi sam. Hajiya Fatee da wasu yan’uwan Hajiya Kaltume suka bita suna bawa Hajiya Binta hakuri amman ba ta sauraresu ba ta fice. Yayarta ce ta dawo dakin tana fadar.

“To yanzu me ye amfanin haka? Jiya kin ci mutuncin yarinya yau kin ci ta wannan yarinyar kuma abun be tsaya iya kansu ba sai da ya kai ga uwar miji? Haba Kaltume, mutuwa tana saka mutane natsuwa amman ke kamar ana turaki?”

“Anty Hauwa ki bar ni da bakincikin da yake cikin raina, ni na san me nake ciki, ni na san irin halin da nake ciki”

Ta fashe da kuka mai karfi. Maama da Khairy ma sai da suka yi kuka saboda ganin mahaifiyarsu na kuka, daman kuma zafin mutuwar yar’uwarsu be isa barin zuciyarsu ba. Sai bayan Sallah La’asar lokacin mutane sun dan fara ragewa, daman wasu sai dai su zo su yi gaisuwa su tafi, Appa ya aiko ya aiko kiran Hajiya Kaltume tare da Khairy da Maama da Ruma, suna jin haka suka san ba dalilin kiran, Hajiya Kaltume gabanta ko faduwa baya yi saboda zuciyarta ta riga da dake, yadda abubuwa suka riccabe mata bata fargabar faruwar komai a yanzu. Can cikin uwar dakin Appa suka shiga, Appa yana zaune kana ganin fuskarka kasan ransa a nace yake. A kasa Maama da Khairy har Ruma suka zauna, Hajiya Kaltume ta zauna a kujerar sofa daya dake dakin idonta a kumbure ga wani ja da suka yi tsabar kuka da bakinciki da suka rumgume.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected