VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ba zaka tsaya ta fito ku gaisa ba?”

“A gaishe ta dai Hajiya”

Ya amsa yana kin hada ido da Hajiya Binta, girgiza kai kawai Hajiya ta yi ta cira kafa suka karasa bakin madaidaicin gate din da tuni Hamad ya bude har ya shiga ciki. Yanayin yadda Hajiya Binta ta tararda Iyami be mata dadi ba, daman kuma ta san za’a rine wai an saci zanen mahauciya, mai ciki ba a rabata da laulayi balle kuma ita da take cikin damuwa, sai dai ganin Hajiya Binta ya saka ta ji kamar an dauke mata ciwo, suka ta yi hira kamar yadda suka saba.

“Jiya muke zancenki da Gwaggo na ce ina tuna haihuwar Hurriya da irin hidimar da kika yi”

Hajiya Binta ta yi murmushi.

“Abu kamar jiya, yanzu Hurriya ta cika sha shida cif”

Hurriya ta wara ido tana mamaki yadda ta manta birthday dinta.

“Eh fa Hajiya amman ai sai October 10”

“To October ba ya kusa ba? Miye rage yan kwanaki ne kawai”

“Hajiya zaki yi ma Appa magana yayi min celebration please”

Iyami ta ce.

“Kin san halin Appanki ba son irin abubuwan nan yake ba, shi gaba daya rayuwarsa irin ta mutanen da ne”

“Zan masa magana da kaina, maybe zai yi min gashi ma dazun ya fada mana a falon Hajiya ya ce ni da Hamad a waje zamu yi karatu”

Mamaki ya cika Amma har sai da ta bude baki ta kalli Hajiya dake murmushi.

“Shi da kansa?”

“Shi da kansa fa, sai dai ki yi ta addu’a kuma ki yi musu, ai maso uwa ya so yayanta, abu dai ne idan ya zo babu yadda za’ayi sai hakuri kawai, amman sakin nan ba karamin mamaki ya ba ni ba”

Amma ta sauke kai kasa tana jin wani rashin dadi yana ziyartar zuciyarta. Hurriya ta tashi ta fice zuwa dakin Anty Rukayya haka take jjnta kamar wata sa’arta saboda tana wasa da ita sosai kamar yaya da kanwa, wannan ya saka Hurriya bata kallon Rukayya a matsayin kanwar Amma sai idan babin girmamawa ne, ba ita ba ko Hamad wasa yake da ita, daman kuma hausawa sun ce karamar uwa madaukar zunubi. Amma ta ce

“Haka Allah ya so Hajiya komai Allah ne yake tsarawa Allah dai ya ba mu ikon cinye jarrabawar wannan jarabarwar”

“Toh Ameen ina nan ina ta addu’a, da yardar Allah Iyami sai kin koma dakin domin sakin nan naki har hawan jini yake son tasar min, Allah ya sauke ki lafiya, da na shiga gidan ma sai na ji duk yayi min dabam”

“Ameen”

Amma ta amsa tana jin zafin barin gidan Appa da ta yi, ba tare da laifin komai ba. Gwaggo ce ta shigo suka suka ta hiran kowa yana fadin abun da ya fahimta game da lamarin, Amma kuma tana fadar yadda Appa ya canja mata tun kamin sakin. Cikar da cikin Hajiya Binta yayi a gidan danta be hana ta cin abinci a gidan Amma ba, saboda tana son Amma kuma ta san idan bata ci ba Amma zata ji babu dadi domin abinci Amma take fara ci kamin ta ci na kowa wani lokacin ma bata taba abincinsu sai ta ce ta koshi. Bayan sallah la’asar Yasir ya iso gidan daukar Hajiya Binta kamar yadda mahaifinsa ya umarce shi, cikin gidan ya shigo suka gaisa da sannan ya fito tare da su Hurriya a daidai lokacin da Rukayya ta sallami bakonta ta nufo karamar kofar shiga tsakar gidan da suka fito.

“Yasir ya gida”

Ya sake mika masa gaisuwa a karo na biyu bayan gaisuwar farko da suka yi a lokacin da ya shigo.

“Mutumen da na gani saurayinki ne?”

Wani kallo ta yi masa jin yadda yayi mata tambayar kai tsaye kamar da zolaya kuma kamar gaske, domin murmushin dake fuskarsa ya hanata fahimtar komai.

“Dan makarantar mu”

“Dan makarantarku har cikin gida? Lallai yana da matsayi da alama”

Murmushi kawai ta yi ta maida dubanta gurin Hajiya da Amma ta rakota suna tafiya suna hira.

“Allah ya kiyaye hanya, Hurriya sai kun dawo”

“uhmmm za a shiga a cigaba da karatun ko? Ko last time da na zo har na fita baki sani ba tsabar karatun littafan soyayya, to aje a karasa kar a manta page din da ake”

Ta girgiza kai still tana murmushi.

“Yasir ka cika shiga min hanci fa… Haka kemin idan na je gidanku ko zama na yi sai ka ce ba daidai na zauna ba”

“Toh ki fyato ni mana idan kin isa”

A nan ma murmushi ta yi ta shige ciki, shi ma ya bita da kallo yana murmushi Hurriya da Hamad kam tuni sun kai cikin mota, inda sabo sun saba da ganin tsokanar yayansu akan kanwar Mamansu ba sabon abu ba ne a gurinsu Amma ma ta saba gani balle kuma su. Amma da kanta ta budewa Hajiya mota ta shiga ta rufe sannan ta juya ta koma ciki Yasir ya shiga ya fara jan motar.

“Yasir na ce ko a fara sabunta kayan dakina ne na kusa samun kishiya?”

Hurriya ta saka dariya Hamad kuma yayi murmushi tare da cewa

“Hajiya yanzu kuma kin fasa aurena?”

“Eh ga babba me zan yi da yaro! Yasir ya ishe ni gashi har yana nema min kishiya, ko da yake Kaltume ai ba zata yarda ka dauki wannan ba sai dai wata”

“Ke tsohuwa waya fada miki har yanzu ana irin zamaninku da ake yi ma mutane auren dole? Ni zan zabo wadda nake so na yi aurena”

“To Allah ya nuna mana, kuma ya bada ta gari”

“Ameen”

Ya amsa yana cigaba da jan motar. Sai da ya fara isa gidan Hajiya ya sauketa sannan ya juyo ya kama hanyar gidansu, a harabar Hajiya Kaltume ya faka motarsa ya bude ya fito Hamad ma ya fito tare da Hurriya gaba dayansu suka nufi hanyar falon Hajiya Kaltume.

“Hurriya me ya samu gilashinki?”

Yasir ya tambaya domin tun zuwansa daukarsu ya lura da fashewar gilashin nata. Ta kai hannu ta taba gilashin.

“Faduwa na yi”

Karaf Hamad yayi ya ce.

“Karya take wani bakon Momy ne ya mareta ni kuma ya na fasa masa tayun mota gaba daya”

Daga Huriyyar har Yasir tsayawa suka yi kallonsa da mamakin furucinsa.

“How?”

“Wuka na saka wukar Momy ta yanka ƙashi na yi ta cakawa ina yanka har da sai da na fashe duka tayun”

Maganar yake yana nuna yadda yana yana cize baki alamar ƙeta. Cikin mamaki Yasir yayi dariya ya bugo kan Hamad.

“Baka da kyau yaron nan bura’uba”

Hurriya ta yi murmushi for the second time ta sake jin Hamad ya burge ta a yau, bayan da ya fadi cewar zai zama likita saboda yayi mata aikin ido yanzu kuma ya fasa tayun wani saboda ya mareta, ita dai ta san bata jituwa da Hamad suna yawan yin fada da samun tsabanin amman kuma yana nuna damuwarsa da kulawa a duk wani abu da ya shafeta, idan wani ya taba ta yana jin zafi fiye da yadda shi idan aka masa yake ji. Yasir ya shiga tambayar me ta yi ma bakon yayi mata marin da ya saka gilashinta fashewa.

“By Misteke na fito… ”

Shi kansa be ji dadin jin karami dalili da be taka kara ya karya ba ya saka bakon marinta marin kuma mai zafi.

“Mutane ba su da hakuri kuma ba su da hakuri…”

Ya rufe baki yayinda yake tura kofar falon ya shiga.

“Toh Wallahi ba zan dauka ba, wannan wulakanci da rainin wayon da Nafisa take min yayi yawa”

“Me ya faru?”

Yasir ya tambaya domin shi kadai ne be san wainar da ake toyawa ba. A take ta amaye masa cikinta tana wani cika domin ba karamin cin mutunci ne a gareta ba Momy ta zargeta da haka duk kuwa da irin rashin zama lafiyar da suke. Yasir ya kalli Hamad, Hurriya ma ta kalli Hamad Hamad ya kalleta kowa yayi shiru, shi dai Hamad ba zai yi laifi yace shi yayi ba, kuma idan an gano shi yayi hakan ba zai dame shi ba, Hurriya kuma ba zata tonawa dan’uwanta asiri ba, balle kuma Yasir da ko da yaushe yake kashe wutar fitina.

“Toh Hajiya Ki yi hakuri, dan Allah ku daina wannan fadan, bana jin dadi haka Appa ma ba dadi yake ji ba, kuma dai ba yara kuke ba be kamata ace kuna biye zuciya ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected