VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Misalin karfe takwas na dare aka jera manyan motoci na alfarma a kofar gidan Bappa kai kana ganin motocin da manyan matan da suka zo bikon amarya ka san amaryar mai tsada ce. Bappa ne ya fara yi mata nasiha sannan Gwaggo Hindu ma ta yi mata Amma kam sai ta kasa cewa komai sai kuka take tana fada Hurriya ji take kamar ƴar zata tafi ta barta ne tafoya ta har abada, ita kanta Hurriya bata iya rike kanta kuka take.

“Ki yafe min Amma ki yafe min”

Shi ne abun da take ta fada ta rike Amma da karfi daker aka banbare hannunta, kusan ta saka mutane da yawa kuka, 3M Nene wato kakar ango ta bada a yi bikon Amaryar sai kuma akwati daya na manyan laces da atamfa da turare da Ammy ta hada na bikon Amarya, haka suka aje kayan sannan suka dauki Hurriya. Husna na rike da hannun kawarta har gaban mota sannan iyeye suka shiga tare da Hurriya Suna ta zauna daga gaba aka ja motocin sai gidan Appanta. A babban falonsa aka shiga da Hurriya aka zauna da ita tana sanye da lifaya an rufe kanta da fuskarta.

“Maraba Maraba Maraba”

Shi ne abun da Appa yake ta fada har ya zauna yana kallon inda yarsa take zaune a natse.

“Ki ji tsoro Allah Hurriya akan dukan lamurranki, ki bi biyaya ga mijinki domin shi ne abokin rayuwarki a yanzu kuma shi ne jigonki, ki bi shi sau da kafa neman aljannarki ya tashi daga karkashin kafafuwanmu ya koma gurin mijinki, ki yi koyi da mahaifiyarki mace ce mai tsananin biyayya agareki kuma mai son abun da nake so, indai kin bi halin mahaifiyarki mijinki ba zai taba kuka dake ba”

Hurriya ta mike tsaye ta matsa kusa da inda take jin muryar mahaifinta sai wata daga cikin kanen Appa ta kamata ta zaunar da ita gaban Appanta. Hurriya ta rike kafafuwansa tana kuka.

“Na gode Appa, da yardar Allah ba zan saka ku ji kunya ba, Appa ka yafe min dan Allah”

“Na yafe miki Hurriya baki min komai ba, ke yar albarka ce.”

Shigowar Yasir ne ya hana kwalla dake idon Appa zubowa domin ya shigo da zolaya ne.

“Wayo take Appa dan ta samu a yafe mata, ai ba mutuwa zaki yi ba aure ne dan haka ki daina wani rokon gafara, ko Appa ya yafe idan ban saka baki ba ba ta yi ba”

Duk suka yi dariya har Hurriya da ta daga kai tana jin kamar ace zata iya ganin yayan nata mai tsananin nuna kauna a agare tun kurciya har girmanta. Yasir ya daga mayafinta ya dubi fuskarta.

“Kanwata, yau zaki tafi ki barmu ko? Rayuwarki zata koma wani gida tare da wasu Iyali da ba mu ba, Allah ya baku zama lafiya, kuma zan jaddawa angon nan cewar kanwata mai zurfin ciki ce ko da tana cikin damuwa bata fada dan haka ya rika kula”

Hurriya ta kwanto jikinsa tana kuka.

“Yayana yayan da ya fi na kowa”

“Ina alfahari da ke kanwata”

Appa da kansa ya bukaci a shiga da ita gurin yan’uwanta ta yi musu bankwana, haka kuwa aka yi bangaren Hajiya Kaltume aka fara shiga da ita, aka zaunar da ita a falon, Hajiya Kaltume ta fito ta tsaya daga sama bata sauko ba saboda bakinciki, daga inda take tsaye ta yi Allah sanya alheri. Khairy kam saukowa ta yi tana kuka sosai kamar ranta zai fita ta yi rama kamar ba ita ba, da kanta ta zauna a gaban Hurriya ta kira sunanta da muryar kuka sai Hurriya ta kasa amsawa.

“Ki yafe min dan Allah… Na san na cutar da ke amman ki daure ki duba hakkin jinin dakw tsakaninmu ki yi hakuri ki yafe min dan Allah…”

Rukayya Allah Allah kawai take kar Hurriya tace ya yafe mata, domin ta san halin yarta da sanyin hali. Hajiya Kaltume dake tsaye can sama kuma tana jin kamar ta sauko ta lakadawa Khairy shegen duka akan wannan abun kunyar da ta yi mata. Ruma ma ta roki yafiyarta tana kuka ta rumgumeta, daga bangaren Hajiya Kaltume aka wuce da ita bangaren Momy, a falo aka samu Momy tare da Namra suna zaune da Miwan. Hurriya ta zauna kasa tana neman yafiyarki tana kuka.

“Babu wanda zai ce kin masa wani abu da saninki Hurriya, halinki mai kyau ne, ni na yafe miki haka Allah ya kaddara haka ya so, Allah ya ba ku zaman lafiya”

Shi ne abun da Momy ta fada tana hawaye, domin a yanzu ta yarda babu sarki sai Allah babu yadda zata yi da abun da Allah ya kaddara faruwarsa. Daga gidan Appa aka wuce da ita family house din mijinta ta gaisa da su Nene da Hajiyar Maru, kanen Mahaifin Captain da kanenen mahaifiyarsa da wasu daga cikin danginsa, babban akwaiti aka bude mata kowa ya kawo nasa kyautar a zuba wasu tufafi wasu kudi. Da aka kawo a gurin Ammy sai ta kama hannun Hurriya ta saka mata key mota.

“Barka da zuwa Turaki Family yarinya, ba dan Captain yana ďana ba, amman tabbas kin yi dacen miji fatan ba zaki ba shi kunya ba”

A take falon ya dauki ihu kowa na murna da mamakin Ammy ta yi ma Hurriya kyautar mota, a sabuwar motar aka saka Hurriya da masu kaita gidan mijinta suka kama hanya zuwa gidan Captain. Kusan rabin unguwar Gidan dawa sai da suka san da Amarya a unguwar saboda manyan motocin da suka rika ratsa titin suna shiga cikin unguwar. Wani mamaken gidan da za a iya karamin gida hudu a ciki aka shiga da Hurriya, har gaban babbar kofar falon aka faka motar, kan wani jan carpet da aka shimfida na musamman domin Amarya Hurriya ta sauko da kafafuwanta tana lullube da fuskarta aka shiga da ita gidanta mai cike da kamshi ga guďa na tashi ta ko’ina.. Dakin da aka ware a matsayin na Captain a ciki dakuna biyar da Appa ya cika mata da kayan daki aka zaunar da ita akan gadon na alfarma, kan lallausan zanen gadon da aka siya mata gurin Khadeeja Candy. Iyaye suka sake yi mata nasiha sannan suka tafi, aka barta da Husna sai yan matan Amarya. Ba dauki dagon lokaci ba aka shigo da ango yana sanye da shaddarsa fara mai matukar kyau. Kana ganinsa ka ga ango baki baya rufuwa fuska dauke da annuri. Kusa da matarsa kuma uwargidansa ya zauna abokansa na zolayarsa shi dai be ce komai ba sai murmushi yake. Su ma abokansa da yan’uwa suka yi ta su nasihar sannan su Husna suka kara da taku suna dariya domin babu mai aure a cikinsu.

“Ba sai kun fada mana ba, angonta ya ta jadda mana amaryar mai tsada ce, dan haka ba mu bukatar tayawa zamu bada abun da ba a isa a mayar mana ba… Ko wace mota da zata yan matan amarya akwai jakar kawayen amarya a cewa kowa jaka tana dauke da kyauta da kuma kudi na siyen bakin amarya”

Hakan da Cousin din Captain ya fada va karamin faranta ran amarya yayi ba, suka ji dadi suka daga mazan har matan suka fice suna murna tare da addu’ar alheri ga ma’auratan. Sai da kowa ya fice sannan Captain ya daga mayafin Amaryarsa ya leka fuskarta ya kalli hawayen dake zubo mata.

“Mai tsada… Idan ba ni ba wa za a kawo wa Amarya tana kuka har yanzu?”

Ta yi murmushi cikin kukan ta ce.

“Idan ba kai ba, wa zai auri makauniyar amarya?”

Sai ya rumgumeta yana dariya.

“Ni ne idonki ai, na huta baki bukatar kallon kowa daman a yanzu”

Ta sauke ajiyar zuciyata tana lafewa a jikinsa kamar wata kyanwa. Ya kama hannunta ya rike yana murza yatsun a hankali.

“Na gode Allah da ya nuna min wannan ranar Alhamdulillah, ban yi tsamanin abubuwa za su zo mana haka da wuri ba, ko da yaushe tsarin Allah mai kyau ne”

Ita dai bata ce komai ba tana kirjinsa sai shakar dadaddan kamshinsa take. Ya dago ya ssauke lifayar daga kanta zuwa wuyanta ya shafa kanta.

“Maa Shaa Allah, Amarya ta kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, kin ga yadda kika yi kyau yau kuwa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected