Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Shiyasa zan yi haka ai, idan na barta a nan cikin satin nan zata iya tarewa, idan kuma ta haihu da ďana ai zance ya kare, ina nan garin idan kuma ta tare sai dai ta tare a gidana”
“Wannan ba mafita ba ne lokacin da zai saci kafa ya tafi mai nawa ko gani be yi ba, ki dai canja shawara”
Ammy ta juyo ta kalli Momy kamar zata fasa kuka. Momy ta yi shiru domin ita ma bata san abin yi ba a yanzu kanta a rufe yake.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un wannan abu da me yayi kama? Wane irin rayuwa ne wannan? Ni na rasa ma me ye abun yi, babu abun da yafi min bakinciki kamar neman auren yarinyar nan da aka yo a cikin falona kuma aka yo sadakinta da sinari”
“Zinarin ma mai tsada, yarinyar ko gani bata yi. Amman ni na san abun yi ni na sani, ta yaro ai kyau take bata karko”
Ammy na maganar zuciyarta na kuna, kamin ta mike tsaye ta nufi bangaren da mijinta yake sauka idan ya zo gidan.
Daddy yana fitowa daga dakin ya hau sama ya shiga dakin Captain kicibus suka yi da Daddy shi zai fito Daddy kuma zai shiga dakin.
“Daddy”
Captain ya fada yana sauke idonsa saka haka nan dai yake jin kunyar Daddy a yau.
“Kai ba mace ba miye na rufe kai a daki? Ko Ammy kake yi ma boyo?”
Captain yayi murmushi yana sosa bayan kansa. Daddy ya ce.
“Mahaifin yaron nan ne Adam ya zo tare da Iyalinsa, ya fara koro min bayana na takatarda shi saboda ina ganin kai da mahaifin yarinyar ne kuka dace da yin shawara ko yanke hukunci”
A take bacin rai ya mamaye zuciyar Captain da tsananin fushi ya ce.
“Me suka zo yi Daddy?”
“Kamata yayi ka sauko mu ji, bana son bata lokaci 5pm zan wuce Kaduna”
Daddy ya karasa yana duba agogo hannunsa, a tare da Captain suka sauko, a tunaninsa iyayen Adam din za su sake bukatar ya basu dansu ne ko kuma wani abun da ya shafi karar da ya shiga a DSS. Captain be ji zai iya gaisawa da ko daya a cikin family ba domin dan su ya janyo musu kallon marasa mutunci yake musu. Salim be kalli gurin da Captain yake zaune ba domin kowa baya marmarin ganin abokinsa a yanzu.
Sai da Daddy ya kalli Captain da fuskarsa take a gintse sannan ya ce.
“Ina tunanin kun san Captain, ko da iyalanka ba su sani ba kai dai ka san da cewar Jamal ďana ne, Salim zai iya fadar hakan, dalilin da ya saka na dakatar da kai daga bayani saboda na kira shi ne, domin shi da mahaifinta suke masu hakkin akanta yanzu, kasancewarsa mijinta an daura Aurenta da Jamal a yau…!”
Da matukar firgici Salim ya kalli Captain da goshinsa ke kyalli kana arba da shi zaka san ango ne latest. Kallo kallo suke da Salim kowa ya kasa dauke idonsa.
“Maa Shaa Allah, abu yayi kyau Allah ya saka maka da alheri a wannan jihadin da ka yi, kuma ya baka wuyan dauka”
Cewar Bashir Sarauta yana jinjina kokarin Captain na toshe kunnuwansa a wannan mawuyancin yanayin da ba kowa zai iya ba. Salim ya dauke idonsa da mugun karfi ya mike tsaye fuuu ya fice daga falon
“Zaka iya cigaba ko kuma ka fara daga farko saboda ya fahimci me ke tafe da ku”
Alhaji Bashir ya kalli Captain cikin yanayin damuwa ya ce
“Daman mun zo nan ne akan maganar abun da ya faru da ne yi ma kowa dadi ba, DSS sun sanar mana su suka dauki Adam sakamakon karar da Captain ya shigar, sun ce sun dauke shi ne saboda bincike yanzu haka dai sun dawo da shi yana asibiti domin sun masa duka sosai daurin da aka yi masa ma likita yace sai an sake daura shi… Dalilin da ya saka muka zo nan shi ne mun bincike Adam akan abun da ya faru daman kuma tun farko an yi masa fada kuma mun tambaye shi taya hotunan suka fita, sai yace mana be sani ba, kuma ya fada mana cewar tabbas yana tare da yarinyar ne…”
A wannan gabar ne Captain ya kasa jurewa ya kalli Daddynsa cikin yanayin bacin rai domin baya bukatar a nanata masa abun da ya riga da haddasace.
“Daddy na dauka magana ce mai muhimmanci za su yi, amman wannan yana maida hannun agogo ne baya”
Daddy ya kalli Captain with serious face domin ko da Alhaji Bashir Sarauta ba abokin kasuwancin Daddy ba ne ta wata fuskar ya kai ya haifi Captain and duk wani abu na nuna rashin mutunci ko rashin girmama na gaba Daddy baya lamuntar dansa Jamal ya aikatawa kowa.
“Respect yourself ka saurare shi ka ji abun da yake tafe da shi”
Captain ya maida hankalinsa gurin Alhaji Bashir Sarauta ba dan ransa yana so ba, dai dan bin umarnin Daddynsa.
“A yanzu maganar da nake da ku, yanzu haka Adam ya fada mana gaskiyar cewar kazafi aka yi ma yarinyar nan!.. ”
Yadda ya fadawa Captain gaskiyar abun da ya faru haka iyayensa suka fada. Daddy ya girgiza kai cike da takaici ya ce.
“Duniya ta lalace, mun zo wani zamani da bayan tarbiyar dole dai muna hadawa da addu’a ga yaranmu, ban da abun zuciya da aikin shaidan miye abun chusa kai da nemana halaka akan me zaka dage sai yarinya ta so ka, bayan hakan be samu ba kuma sai ka ce sai ka nemi lalata rayuwarta? Yanzu ya bata sunansa ya bata nata da bata gidansu ina amfanin haka?”
Alhaji Bashir Sarauta ya ce.
“Babu ai na fada masa da abu ne mai kyau da yanzu celebration muke muna murna amman ga abun da ya janyo mana, ita kanta abokiyar shaidancin tasa gashi ita ma ta janyowa kanta ta samu nata kaso”
Daddy ya girgiza kai.
“Dole ai zata samu haka ko ma fi, ko bare ka aikatawa haka ai ba zaka ga daidai ba balle kuma yar’uwarka ta jini, sun jefa yarinya a damuwa ba tare da hakki ba”
“Shiyasa na zo na baka hakuri kuma na roki yafiyar abubuwan da suka faru, daman aiko sammaci bana nan Iyalina suka yanki ticket suka aiko da sunana, gashi kuma shari’ar ta zame mana biyu, sannan yaron nan gashi babu lafiya, dan Allah ayi hakuri a janye karar nan da Captain ya saka gudun kar mu kara yin abin kunya, domin idan aka ce za’ayi shari’a har wadanda ba su da waya da redio zansu iya jin wannan abun kunyar, wani ma zai iya cewa da kai nake shari’a ranka ya dade ba domin canja labari be da wahala a gurin mutanen mu yanzu…”
Daddy yayi jimmmm na dan lokaci, ya sauke dogon numfashi yana nazari, be kai ga yanke hukunci ba ya kalli Captain dake karanta sakon taya murna da Salim ya aiko masa ya ce.
“Captain yanzu meye abun yi me ye shawara, ko da yake ya kamata ace an ji ta bakin mahaifinta ma?”
Ya dago kai ya kalli mahaifinsa.
“Daddy zan janye shari’a daman kuma yin haka ba abu ne mai wahala ba, zan yi hakan on one condition Adam zai yi video ya fadawa duniya gaskiya kuma ya roki yafiyar Hurriya if not na zan janye shari’ar nan ba kuma Monday nan zamu shiga Kotu, hakan ne kadai zai wanke Hurriya a idon duniya kuma daman na mata wannan alkawarin”
Mahaifiyar Adam din ta dubi Captain ta ce.
“Haba ďana wannan matakin be yi tsauri ba? Zai iya bata hakuri a sirrance kuma ya fada mata gaskiya, amman fitowa yayi video yaje viral sai kara lalata lamarinsa ne”
“Ita da take mace ya lalata mata rayuwa balle kuma namiji? Da be aikata ba wata kila da duk hakan be faru ba”
Yan’uwan Alhaji Bashir ne suka shiga rarrashin Captain ko zai sauko daga wannan hukuncin amman fir yace idan ba haka ba shi ba zai hakura ba. Alhaji Bashir ya dubi Daddy ya ce.
“Ranka ya dade a taimaka a saka baki lamarin nan”
Daddy ya nuna Captain.
“Shi ne mijinta, kuma wannan case din a hannunsa yake, ina tunanin a yanzu ko ubanta be kai shi iko da ita ba, kuma ya saukaka muku a haka din ma, ni ban yi zaton zai yi saurin amincewa ba, yin haka zai wanke matarsa daga zargi da zagin da danku ya ja mata, kuma idan ma ba ku aminta yaron ya bada hakuri ta wannan sigar ba ko kotu aka je Kotu zata saka shi ya bada hakuri kuma ya fadawa duniya abun da ya faru, daga karshe kuma ya fuskanci hukunci”