Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Ranar wunin biki Hurriya ta chaba ado da farin lace da farin mayafi domin farar rana ce da ko wace ƴa mace take fatan gani a rayuwarta, kallo daya zaka yi ma Hurriya ka fahimci babu yaki babu ja Captain ya zabo daya a cikin dubu, innocent face dinta ta sha light makeup, an gyara gashin kanta ya kwanta baya kamar ba a taba kai masa hannu ba, farar kafarta ta sha jan lalle mai daga hankali kowa ne jarumin namiji mai son ido da kwalliya, ga jiki ya sha dilka ta ko’ina kyali take kamar tsadadden lace dake jikinta. Ya yadda mutane suke fada yadda ta yi kyau take auna irin kyau da ta yi, domin a nan aba a lamunce mata da ga yadda kyauta yake a fili ne. Duk shagalin da ake na bikinta bana ganin kowa sai dai ta yi saurare a nan ma sai da yarda ta rasa wasu masoyan da Allah yayi alkawarin wanda ya rasa su kuma yayi hakuri zai masa sakamako da Aljanna, wato masoya biyu idanuwa. Hurriya na zaune dakin Gwaggo akan gadonta tare da Husna da wasu daga cikin kawayenta na makarantar su da boko da islamiya da Husna ta gayyato Amma ta shigo dakin tana sanye da lace mai tsada brown color ita ma ta sha nata lallen sai dai nata na hausa ba yayi baki sosai yayi mata kyau.
“Husna ke da kawayenki ku dan ba ni guri zan yi magana da Hurriya”
Husna ta tashi tare da kawayen suka fice, zuwa falo wasu kuma suka fita harabar gidan da Appa ya saka aka gyara ko’ina saboda Hurriya. Amma ta zauna tana kallon yadda fuskar yarta ke sheken amarci.
“Kamar jiya aka haife ki, ina tunawa lokacin da mahaifinki ya shigo me ya Gwaggo ta bari aka haife ki a gida, saboda baya son matansa na haihuwar gida, ya fi son a tafi asibiti, sai Gwaggo tace ai na haihu lafiya kuma ya amsa ƴa mace,mahaifinki ya shigo ya saka hannu biyu ya karbe ki, a take a gurin ya rada miki suna ba tare da yayi shawara da ni ba, ya ce barka da zuwa Hurriya, Allah yayi miki albarka yasa ke din mai amfanarmu ce, kuma ya nuna mana aurenki, ashe Allah ya amsa”
Amma ta sauke kai kasa tana taba akwatin sarkar zinarin dake hannunta.
“Ina cikin wani irin farinciki a yau marar misaltuwa, burin ko wace uwa ta ga auren yarta, kuma da mijin da yarta take so yake da halin kwarai, Wallahi ban yi zaton rayuwa zata ara min lokaci na kawo yau ba, ashe dai zan tashi zan yi magana zan aurenki Hurriya”
Amma ta bude akwatin sarkar zinarin dake hannu ta dauko sarkar da take a matsayin sadakin Hurriya ta yaye mayafinta ta saka mata a wuyanta.
“Ina miki murna ganin wannan rana mai daraja, Allah yasa ki shiga gidan aurenki a sa’a kuma ya baki yaya masu yi Miki biyayya kamar yadda kika yi min, ina kaunarki ƴata Allah ya bawa wannan yaron ikon yi miki adalci da kaunarki kauna ta hakika ta har abada”
Hurriya ta rumgume Amma da sauri tana kuka irin yar da bata son rabuwa da uwarta.
“Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana”
Amma ta yi ma Allah godiya tana kuka kamin ta dago Hurriya daga jikinta ta kama hannayenta ta rike.
“Ban sani ba ko ba zan samu yin magana da ke na anjima ko kuma ya kasance cikin mutane ne ba zan iya fadar wani abun ba, dan haka nake son baki wani sirrin zaman aure a yanzu wadda uwata ta ba ni kuma shi ya taimaka min har ake ganin kamar na mallake Appanku”
Hurriya ta natsu sosai ta mika hankalinta a gurin mahaifiyarta.
“Ki rike hakuri, hakuri wani abu ne mai wahala aiwatar ba, amman ba shi da wahala ga wanda ya dauki rayuwa da sauki, da hakuri na mallake zuciyar Appanku, idan yana magana ko yayi fushi bana katse shi, saurara nake na ji kalamansa kuma na yi hakuri ko da kuwa sun bata min rai, idan ya ba ni rashin gaskiya karba nake na rike ko kuwa ni ce mai gaskiyar, sai bayan ya huce sai na lurar da shi kuskuren inda aibu yake, ko kuma na fada masa gaskiyar a inda take, idan na ga yana son abu ina kokarin na ga na fi sonsa, shiyasa ban taba nunawa yayansa kiyayya ba, na rike mahaifiyarsa kamar tawa ina kyautata mata ina mata biyayya kamar yadda nake yi ma danta, ina sa yawan kyauta saboda dangin miji da makota basa son mace mai rowa ko mai tsananin son abunta, idan na ga yayi wani kuskure ina nuna masa illar haka kuma na nuna masa hanyar da ta fi saukin bi, ban taba nuna masa ina kishin Nafisa ko Kaltume ba, kuma ba dan bana yi ba, sai dan na fi karfin zuciyata na boye abun a raina, shiyasa baya taba yarda cewar bana son matansa saboda na iya takuna, kuma na rike girki na iya tuka tuwo yayi kyau na yi dadddar miya Appanku da ku kanku kuna ci suna santi, na rike tsabta na rike kamshi mahaifinki ya taba fada min idan ya ji kamshi turaren da ba nawa sai ya ji a dabam, duk abun da na san mahaifinku zai bukata kamin ya fada na aiwatar idan kuma na kyama ne ina gudun nake kauce masa, da wannan na gagari matan ubanki har suke ganin kamar na mallake shi na masa magani, idan girkina ya dawo da wuri Appanku yake dawowa gida, ke ma ai kin sani saboda ina masa hira, ina ba shi labarai masu dadi, na yi masa hira mu tattauna abubuwa da yawa na yadda rayuwa take ciki, ni ce radio sa ni ce tv sa idan ina kusa da shi bana yarda hankalinsa ya tafi ko’ina zai a gurina, idan kuma ba girki ba ne ina kokarin kiyayewa na ga ban shiga hakki abokan zamana ba, idan zai yi zabe ni nake zaba masa komai, ban tana yarda Appanku ya saka kayan da yake ra’ayi ba a ranar girkina, saboda kwalliyar tawa ce ba tashi ba, ni nake zaba masa kayan da zai saka, sai kuma na yi sa’a shi din mutum ne mai tsananin so na mai saurarena mai gudun bacin raina…”
Amma ta yi murmushi tana tuna baya.
“Idan Appanku ya ce Iyami kar ayi kaza, Wallahi bana aikatawa saboda ya ce kar ayi, ina ba shi lokacina sosai ina jin maganarsa ina bin dokokinsa, saboda ni ce a kasa shi ne a sama shi din jagorana ne, Allah ya riga ya ba shi wannan girma, ni kuma dole na bi saboda na samu aljanna ta, kuma kar ki yarda wani ya fahimci irin zaman auren da kike da mijinki ba mai dadi bane ko da kuwa kun samu tsabani, ki sama ma’ajiyar sirrinsa mai rufe duk wani asirinsa, kuma ki rika lura wane hali miJinki yake shiga idan yana ciki damuwa idan yana fada ya yake, idan yana farinciki ya dabi’unsa yake, abun da duk kika ji zaki iya dauka ki nuna masa tun farkon zamanku, wanda kuma ba zaki iya dauka ba ki fahimtar da shi da wuri ba sai daga baya ba, karki yarda ki raina mijinki ko da kuwa shi din abun rainawa ne a gurin wasu mutane, ki zama macen da idan ran mijinki ya bace ke zai rika tunanin ko ma ya nufo saboda ke kike kwantar masa da hankali. Kin ga abubuwan nan da na fada miki, wata rana sai kin zo kina fada min yan’uwan mijinki suna tunanin kin mallake shi, kuma wata rana mijinki ko aure ya kara zai yi ta ganinki ne wata macen ta kasa sarrafa shi saboda karatunki ya saba dauka, wani darasin zai masa wahalar zama a kai, da haka na gaggara a gidan mijinki sirrin ba na iya kyau bane kawai har da na iya zama, ai wata macen bata da kyau amman a haka mijinta yake sonta fiye da kyau, karki yarda wata macen ta fi ki a gurin mijinki”
Amma ta saka hannu ta share hawayen Hurriya dake zuba tana murmushi.
“Allah ya miki albarka”
“Ameen Amma na gode”
Ta fada cikin kuka wasiyar Amma na ratsa jikinta. Rukayya ce ta shigo dakin tana sanye da anko kamar sauran yan gidan, ta yi matukar kyau blue atamfar ta karbe ta sosai.