VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Wayyo Amma ma, Amma….. Amma… Amma… Ke….. Amma na”

Namra ta yi saurin rika hannunta tana kuka.

“Hurriya ba gani nan ba, ta zo muje ciki Momy tana nan ai”

Ta fisge hannunta, sanin kanta ne daga Momy har Hajiya Kaltume babu wanda ta isa ta jingina a cikinsa ta yi kuka, domin ba su dauke ta kamar sauran ƴaƴansu ba.

“Kira min Yayana kira Yayana”

 

Domin karanta labarin ziyarci shafin dake sama na arewabooks @Khadeejacandy ko kuma ku yi searching din Hurriya.

@

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

1️⃣

Kamin direban ya isa gida duk wanda ke cikin motar ya dauka Hurriya shudewa zata yi, saboda kukan da take yana yin sama da nufashinta kamar nunfashin zai fice daga jikinta gaba daya. Namra ce take rike da ita tana kuka tana bata hakuri.

“Yi Hakuri Hurriya In Sha Allah zai dawo lafiya Allah zai tsare su”

Hurriya bata iya furta komai, gashin idon nata ya rufe gaba daya saboda kukan hawayen ya hanata ganin dishe-dishe ma da take gani idan babu gilashi a idonta. Direban na fakawa Salma da Khairi suka fita suna kuka suka nufi bangaren Hajiya Kaltume suna kuka, Namra kuma ta tsaya ta riko Hurriya suka fito.

“Bana ganin komai Yaya Namra idon ya rufe gaba daya… Karki bar ni nan dan Allah tsoro nake ji… Kira min Yaya Yasir ko ki kaini gurin Amma ko ki kira min Appa na dan Allah”

Tana maganar muryarta na rawa saboda numfashim da ya sarke ta. Ta san a gurin dayan su ne kadai zata yi kukanta ta more kuma ta fada musu abun da ya faruwa. Kowane ďa ko ƴa idan abun farinciki ko kishiyarsa ya same shi guduwa yake gurin uwarsa, sai dai ita a yau bata da wannan gatan, ba dan mahaifiyarta bata raye ba sai dan bata tare da ubanta, bata taba sanin zafin rashin Amma a gidan ba sai yau, ko wane ďa yana bukatar uwa a kusa da shi balle kuma ita da take da lalaurar ido. Dukawa ta yi a gurin ta dora duka hannayenta biyu a kai ta kwalla ihu da kukam muryarta tana kuka har sai da duk wanda ke harabar gidan hankalinsa ya dawo kanta.

“Wayyo Amma ma, Amma….. Amma… Amma… Ke….. Amma na”

Namra ta yi saurin rika hannunta tana kuka.

“Hurriya ba gani nan ba, ta zo muje ciki Momy tana nan ai”

Ta fisge hannunta, sanin kanta ne daga Momy har Hajiya Kaltume babu wanda ta isa ta jingina a cikinsa ta yi kuka, domin ba su dauke ta kamar sauran ƴaƴansu ba.

“Kira min Yayana kira Yayana”

Namra na cira kafa da zimmar tafiya kiran Yasir sai ta hangoshi ya fito da saurinsa ya nufo inda yake.

“Hurriya”

Hurriya na jin muryarsa ta mike tsaye da sauri ta fara lalaben inda zata ganshi.

“Yayana Yayana Yayana”

Kusan duk wanda ke tsaye yana kallonta sai da ya tausaya mata, domin lalurar rashin gani babbar matsala ce. (Alhamdulillah da kyautar Allah, if you can read this ku gode Allah, ba zabinku ba ne, kyautar Allah ce, and don’t forget littafin na kudi ne idan kika karanta baki biya ba, ko kika min sharing na barki da Allah)

Yasir na isowa ya rika hannunta dake ta rawa take da fatar bakinta.

“Yayana dan Allah ka kai ni gurin Amma… Dan Allah..”

Without second thought yaja hannunta ya karbi key hannun dayan direban da ya aje Hajiya Kaltume few minutes before the incident happen. Ya bude motar Namra bata kara jin tausayinta ba sai da ta ga yadda take lalaben motar zata shiga, Yaisr ya taimaka mata ya saka ta a back seat sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya murza key ya juya motar cikin tashin hankali, ba dan yana namiji ba da tuni shi ma ya fashe da kukan kamar yadda kanensa da mahaifiyarsa suke kukan. Shiru Hurriya ta yi a cikin motar domin bata ganin komai sai duhu zucuyarta kuma ta cika fa tsoron abun da ya faru. A harabar gate din gidan Yasir ya faka motar sannan ya budr ya fito da Hurriya. Sai da ya daga gate din gidan sai kuma ya ji ba zai iya shiga ciki ba domin ba zai iya zama mutum ya farko da ya labartawa Amma labarin an sace danta ba, ya san idan ya shiga gidan ta ga yarta a wannan halin sai ta tambaye shi shi kuma ba zai iya mata karya ba. Haka kuma ba zai iya barin Hurriya ta shiga cikin gidan ita kadai ba a wannan yanayin.

“Hurriya ko dai ki hakura mu koma? Ba zan iya shiga cikin gidan nan ba, bana son na daga hankalin Amma a yanzu”

Tana jin haka sai ta saka dayan hannunta ta kwance hannunsa dake rike da nata.

“Tafi zan…. Iya… Shiga… Daga… Nan”

Be san bata gani gaba daya ba, a zatonsa tana gani dishe-dishe kamar da, dan haka be musa mata ba ya bude mata gate ta lalaba ta shiga, ya maida kofar ya rufe sannan ya koma cikin motar ya fice daga unguwar. Hannu Hurriya ta mika tana lalaba hanya, tare da amfani da zuciyarta tana ayyana yadda hanyar take a lokacin da take gani.

“Ke Hurriya…”

Ta ji muryar Rukayya sai wani sanyi ya ziyarceta. Ta karaso kusa da ita ta rika hannunta.

“Waya kawo ki? Mun ji an bude kofar gate ba mu ga an shigo ba shiyasa na fito na duba”

“Yaya Yasir ne ya kawo ni, ya tafi Mama Rukayya kai ni gurin Amma na”

“Me ya same ki Hurriya?”

“Kai ni gurin Amma please, bana gani yanzu bana iya ganin komai sai hudu, gaba daya idon ya rufe, na daina gani dishe-dishen ma”

“Innalillahi”

Rukayya ta fada tare da jan hannunta suka shiga ciki, Amman dake zaune dakin Gwaggo tana kwadon zogale ta aje kwanon zogalen ta yunkura da cikinta wata tara ta mike tsaye da sauri ganin Hurriya da hawaye a fuska kacha-kacha har ya bata gaban hijabinta, gata sanye da uniform din makaranta da bata cire ba kuma babu gilashi a idonta.

“Hurriya me ya same ki?”

Kunne da jikin da yayi kewar uwa ne kadai zai iya fahimtar yadda ruhu yake ji idan ya ji ko yayi arba da uwa.

“Amma ina kike?”

Ta saki hannun Rukayya ta fara lalaben inda take jin muryar Amma. Amma ta mika hannu ta rikota sai Hurriya ta rumgume ta ta kwanta jikinta tana wani irin kuka da ya saka Amma ta kasa rike kanta ita ta fashe da kuka.

“Me ya faru Hurtiya? Me ya same ki? Waya kawo ki? Me ya samu idon naki ina gilashinki”

Har Hurriya ta bude baki ta yi magana, zancen da Yasir yayi a waje ya fado mata a rai. Shi ma kenan ya ce ba zai iya sanar da Amma ba balle kuma ita da take yarta. Kamar an saka allura da zare an dinki bakin Hurriya haka ta zama, ta kasa furta komai kuma ma sai ya koma mata cikin zuciya hawaye kawai take ita yi.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”

Amma ta furta gabanta na bugawa da karfi. Ta san ba lafiya zata kawo yarta a irin wannan yanayin ba, kuma gashi ta kasa fadar komai sai rumgume ta take kamar zata shige jikinta.

“Hurriya yi a hankali mana, kin san akwai kanenki a jikinta, ko kuma ki zo ni na rumgume ki idan rumgumar kike so”

Gwaggo ta fada, sai Hurriya ta girgiza kai tana kara kankame Amma.

“Hurriya dukanki aka yi?”

Ta girgiza kai.

“Wani abu aka watsa miki a ido?”

Ta girgiza kai.

“Fada kika yi da wani?”

Ta girgiza kai.

“Dan Allah ki bude baki ki yi magana mana minene? Ko dai fada kika yi da Hamad? Na san zai iya cewa yayi miki mugun duka saboda bana gidan?”

Maganar da Amma ta yi ta Hamad ta saka Hurriya fashewa da sabon kuka.

“Yasir ya kawo ta, ta fa yi magana dazun yanzu ne dai ta kasa cewa komai”

“Wata kila fadan ta yi da Hamad shiyasa ta kasa fada tana tsoron kar na yi masa fada ya kara mata”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected