VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Toh ba sai idan anyi auren ba, wannan me bakar zuciyar? Ba kowa ce zata iya zama da shi ba”

“Ai ko fasawa aka yi sai dai ya aureki, daman Hajiya Turai ta so a hada wannan zumunci shi din ne ya ki, kuma kin san basa masa dole ”

“Ni”

Namra ta nuna kanta domin bata taba jin makamacin haka daga bakin Momy ba.

“Ke fa mun sha yin maganar da Hajiya Turai ai, amman shi Jameel din ne be yarda ba, yanzu dai ya samu wadda yake so an huta”

Namra bata ce komai ba ta maida idonta kan abincin da take ci tana motsa shi a hankali kamar mai tunani. Momy kuma ta tashi daga dinning din tana ta masifa saboda Namra bata tasheta daga bacci ba.

“Kiransa zan yi yanzu Allah yasa ya daga, kar wannan yar filfilwar ta jazamin masifa ni Nafisa”

Nan ma Namra bata ce komai b ta cigaba da motsa abinci tana tauna wanda yake bakinta ta kasa hadewa sai tunani take. Kamin ta juyo ta kalli falon da aka bude, Hurriya ce ta shigo kanta ba dankwali rabin kan nata a tsire.

“Yi sauri ki dauki abun da zaki dauka ki fice kamin Momy ta fito, dan na san sai ta miki fadan kin karbar box din da Captain ya baki”

“Abinci zan zuba”

Ta nuna abinci tana kallon stairs gabanta sai tsananta faduwa yake.

“Zo ki zuba”

Ta nufi dinning din da sauri ta dauki plate ta zuba abincin mutum biyu ita da Hamad ta saka naman kaza a sama ta dauki spoon biyu ta saka.

“Ke da Hamad zaku ci?”

“Eh”

“Dazun shi ya hana ki karbar glass din ko?”

“Na ga ya bata rai yana hararata, na san idan na karna zai iya min masifa kuma yayi fada ni, ko ya dukeni”

“Ke dai Hamad ya raina ki ya maida ke kamar kanwarsa, ko dan ya ganshi babba ke kuma ba ki ba”

Hurriya ta yi dariya mai sauti ta shiga Kitchen ta dauko tray ta dora ruwa da lemu a kai sannan ta fito ta dauki plate din abincin ta dora a tray ta dauka ta fice da sauri. A harabar Apartment din Hajiya Kaltume ta dawo ta zauna a balcony kusa da Hamad ta aje tray.

“Hamad zo mu ci abinci”

Ya kalli abinci sai ya bata rai.

“Waya ce ki hade? Waye zai ci abinci da ke to?”

“To ai ni ina sauri ne, Yaya Namra ta ce Momy nemana take zata min fada saboda ban karbi abun da bakonta ya ba ni ba”

“Toh ina ruwana ki je ki zuba wani”

Ya saka hannu ya dauke abincin da ba zai iya cinyewa shi kadai ba ta dora a cinyarsa.

“Idan ba zaka ci da ni ba, ba sai ka je ka debo na ka ba?”

“Ba zan ce ba, ni ki daina ba ni umarni”

“Wannan dai nawa ne ka ba ni abinci na Hamad”

Yayi mata kunne ne shege yana ta cin abinci ko kallonta be yi ba. Har ta tashi zata tafi debar wani sai kuma wata zuciyar tace mata Momy na nan falo, sai ta koma ta zauna ta dauki lemun ta sha tana ta kallonsa yana cin abinci. Ita ma dai kamar mantawa ta yi Hamad be cin abinci da kowa kuma be cin ragin kowa har da na Appansa da na Amma. Hakura ta yi ta saka masa ido ta can kuma ta ji ba zata iya ba tunawa da ta yi baya son gashi idan yana cin abinci sai ta cigaba da sifar kan tana kallonsa wai ko zai ji kyama ya aje abinci. Instead of yayi haka sai ya kifar da plate din ya riko gashin kan nata a daidai lokacin da Mota ta faka harabar Hajiya Kaltume. Da wani irin karfi yake fisgar gashi da karfi bata san lokacin da ta fara ihu tana rike hannunsa ba. Da sauri Fadeel ya bude motar be ko tsaya kashewa ba ya fito ya nufi inda suke daker ya banbanre hannun Hamad Hurriya ta koma bayansa da sauri tana kuka.

“Kai wannan ai sai ka tsinke mata gashin ka rage mata sadaki, miya hada ku?”

Hurriya bata iya magana saboda kuka, Hamad kuma ba gwanin maida magana ba ne daman sai cika yake kamar wani zaki. Hajiya Kaltume tana kawowa kusa da su ta ce

“Ai haka suke, uwa daya uba daya amman baya raga mata, basa zaman lafiya kamar Annabi da Kahiri suke”

Cikin mamaki Fadeel ya kalli Hamad.

“Wai kanwarsa ce yake mata wannan jan gashi haka?”

“Ita ce yayar ai, dan ka ganshi da girma shi ne kanen ai, baya ragawa kowa a gidan”

Hamad ya juyo yana watsawa hara Hajiya Kaltume dake korawa Fadeel bayani saboda ta tabo shi tun da ta ce be ragama kowa.

“Idan ba kai ba, wake fada da mata? Ba yayarka ba ce?”

Ya juyo ya kalli Hurriya da ta boya bayansa.

“Ke kuma ki rika kiyaye, yi hakuri ki daina zama babu dankwali ba kyau”

“Ai Allah yasa ma aljannu da ifiritai da shaidan duk su tattara su shige a cikin kan nata, ita ma ai ba karamar marar jin magana ba ce”

Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume dake fadar haka tare da yin gaba da bar su a gurin. Ta share hawayenta ta kalli Hamad sannan ta kalli Fadeel.

“Ina wuni”

Dariya yayi.

“Lafiya Kalau, Allah ya tsare gaba Hurera ko?”

“Hurriya”

Ta gyara masa.

“Yeah ki rufe kanki”

“Toh”

Ya juya ta sauka balcony din ya nufi motarsa dake kunne har lokacin sai da ya shiga motar daga mata hannu sai kallonta yake sannan yayi reverse ya fice.

Two Week Later….

Hajiya Fatee ta gyara zama ta kalli kawarta kamin ta kalli Malamin da suka sauka a garage din gidan.

“To yanzu Malam akwai yadda za’ayi a danne cikin nan kar ya bayyana? Kuma wannan tofe tofen yawun da kin cin abinci da nake ga kasala duk na daina shi?”

Malamin dake sanye da babbar riga ya kalli Hajiya Fatee yana murmushi.

“Za’a iya sosai kowa, ba yau na saba ba, za a iya danne cikin nan har tsawon shekarun da kike so”

“Alhamdulillah, ina son a danne min shi har nan da shekara dari, na san dai ba zan yi shekara dari a duniya ba”

“Ko kuma nan da lokacin da zaki yi aure ba, Hajiya yadda kike da surar nan Maa Shaa Allah, ai sai idan mutum be samu dama ba, shekarunki ba ba za a ce kin yi ba, ai na san ba za a rasa namema ba ko?”

Maganar yake yana dariya kamar wata abokiyar wasarsa.

“Aa kai aure kuma? Wake ta aure yanzu? Aa mun bar wa yara, ni dai yanzu bukatata a fara danne cikinki, idan an samu nasara hakan yayi sai a shiga yi Farraqu tsakanin yaron nan Fadeel da Matarsa Afrah domin ina kwana da bakincikinta a kullum Wallahi”

.“Babu Matsala Hajiya, za a danne ciki, matukar ba a daga dutsen da zamu saka layar mu rufe ba, cikin nan ba zai taba tashi ba har abada, amman fa zaki zuba kudi kam”

“Karka damu zan biya ka ko nawa ne, ammam dan Allah a saka dutsen a inda ba za a iya dagawa ba”

“Aljannu za mu saka su yi aikin, karki damu”

Hajiya Fatee ta kalli Kaltume suka yi murmushin jindadi sannan Hajiya Kaltume ta kora da nata bayanin.

“To ni Malam na ji shiru, kasan na baka kudi akan za ayi ma Iyami aiki ina son komai nata ya lalace amman har yanzu ba labari, kuma ni yanzu so nake a mallake min kowa a gidan nan daga mijina har Nafisa ikon kowa ya dawo karkashina, ina son Alhaji ya zama be iya aiwatar da komai sai abun da na fada masa, kuma ina son a shiga tsakaninsa da yaran nan, ya maida su banza a cire masa su a rai, ya ji baya bukatar ganinsu ma, domin na ji yana zancen fitar da su waje karatu, kuma ko be fitar da su ba, ita wannan da take da kokari na san gwanati ko wasu za su iya kaita waje karatu, so nake a lalata karatun nata, kai ni duk wani abu da zai saka Iyami farinciki bana sonshi a toshe komai Malam”

“Hajiya, aiki ai mun aiwatar jefa muka mata kuma yana nan yana tafiya kin san jifa wani lokacin tana dauka lokaci kamin ta isa, amman kuma da zarar ta isa zaki sha mamaki ba dan karami ba, sai kin tabbatar da ba ki min biyan banza ba, mijinki kuma zaki mallake shi a hannu, sai dai wannan Nafisa kishiyar taki fitinanniyar mace ce akwai yan ƙwanƙwanmai a kanta, kin san mai yawan masifa da mai addu’a asiri be cika saurin kama su ba, amman zamu gwada”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected