VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Zo muje part din na ku”

Har lokacin kuka Hurriya take tana biye da yayanta dake rike da hannunta suka fice. Umm Khairi ta sauko da sauri tana murmushi ta dafa Hajiya Kaltume da ta kai zaune baki har kunne tana mamakin jin kalaman Hurriya.

“Hajiya Appa ya saki Amma kenan?”

“Ina kyautata zaton haka, domin dazun da safe shi ya kira ni da kansa ya ce min na dauke Bedsheets dinta na kawo masa abun karyawa, har na ce masa bana son ta ga kamar ina shigar mata hakki, sai ya ce min baya son digon zance zan karbi girki a yau”

Umm Khairi ta rumgume Hajiya Kaltume da sauri tana murna.

“Wayyo Allah na dadi, amman me yasa ba ta fadawa Hurriya gaskiya ba?”

“Waya sani? Toh ko ganin take zata dawo? Zama be gan ni ba ungo wannan kai min Kitchen bari na kira Hajiya Fatee”

Ta mike tsaye da sauri, daga ita har yarta Umm Khairi kallo daya zaka yi musu ka fahimci farinciki dake zuciyarsu, da rawa Umm ta karasa kitchen ta aje plate din ta fito ta shiga dakinta ta dauki wayarta ta fara kiran yan’uwanta da basa gidan tana musu albishir domin sun dadi ba su samu wani labari mai dadi da faranta zuciya ba irin na yau.

Hajiya Kaltume na shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta saka key dan tabbatar da ita kadai ce a dakin sannan ta nufi wayarta cikin nauyin jikin dake hana masu kiba da teba hanzari a duk lokacin da suka yi yunkurin yin haka. Sai da ta fara zaunawa sannan ta dauki wayar ta lalabo number aminiyarta Hajiya Fatee duk kuwa da kasancewar ta girme ta nesa ba kusa ba, sai dai friendship be duba age ko level idan jini ya hadu, cikin natsuwa Hajiya Kaltume ta aika mata da kira, zuciyarta har wani bugawa take irin na jindadi da farinciki da tun da aka auro Iyami rabonta da irinshi.

“Assalamu Alaikum Hajiya Kaltume”

“Na’am Hajiya Fatee ke kadai kike?”

“Ni kadai nake yanzu yar iskar yarinyar nan ta fita”

“Ba dai Afra ba?”

“Ita fa”

“Ikon Allah yaushe kuma ta fara zuwa gidanki?”

“Yanzu fa, ina zaune sai gata ta zo ita da yara wai an zo a gaishe ni, waya sani ko wani mugun abun aka kullo min a kawo min, ta mallake ni kamar yadda ta mallake min ďa”

“Tsab kuwa zata iya shi, indai magani ne wannan yarinyar babu inda bata sani ba, gashi ta tsaneki ko maganin mutuwa ma zata iya miki”

“Kamar an yi a gabanki, ai an sha fada min ta yi ta yi samun sa’a ne bata yi ba, shiyasa na tsaya a kafata bana wasa kar ta jedar da ni a zuciyarsa kuma Wallahi idan ina da rai sai Fadil ya kara aure”

“To ke Hajiya Fatee anya wannan shedaniyar surukar ta ki zata yarda ta bar Fadil yayi aure?”

Hajiya Fatee ta yi dariya.

“Hajiya Kaltume kenan kina magana kamar baki san wacece ni ba, ai idan ta kwana da shiri wani a hanya ya kwana, daga ita har uwarta sai sun kyale min ďana, komai shige shigensu da tsafe tsafe da yardar Allah sai hankalin Fadil ya juyo kaina ni ma sai na sarrafa ďana yadda nake so”

Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana kara yarda da zancen Hajiya Fatee.

“Na yarda da haka, domin a yanzu na sarawa lamarinki, ni yanzu ma kira na yi na yi miki albishir, dazun da safe Alhaji yake ce min na kawo masa abun karyawa na cire Bedsheets din da Iyami ta saka, ni tun a lokacin na san wani abu zai faru, kuma na tambaye shi lafiya be fada min ba, yanzu kuma Hurriya ta shigo tana kuka wai Hamad ya daketa a nan take fada mana Amma bata gidan wai ta tafi gidansu har sai ta haihu zata dawo”

Hajiya Fatee ta daki cinyarta da karfi ta kyalkyale da dariyar ƙeta da jindadi.

“Ke daga jin haka ai kin san abun da muke nema ya samu, ai duk wanda ya ci tuwo da mu miya ya sha, kuma gadon ari sai fanna, sirrin iya sai marɗibo, yanzu kam sama ta yi wa yaro nisa sai dai ya tada kai yayi kallo, ai na faɗa miki kowa yace zai iya haɗeye gatari to sakar masa ɓota, kuma idan ta sha mu ba mu karya ba, yaro baya ja da mu muja da ubansa…”

Haka Hajiya Fatee ta rika jero kirari da karin magana cikin alfamari da tinƙaho. Hajiya Kaltume ta miƙe tsaye ta fara yawo a ɗakin tana jin kamar ta taka rawa.

“Wallahi sai a yau na ji wannan ƙunci da nauyin da ya tsaya min a zuciya ya sauka, tun da Alhaji ya auri Iyami farinciki ya gagareni, duk wani abun da zan samu a duniyar nan farincikina raggage ne, saboda Iyami, yarinya daga zuwa aiki kin aure mai gida har da su ƴaƴa gashi ya murje ido ya nuna kamar ya fi sonta da kowa, ƴaƴanta ma kamar ya bude ciki ya saka su ya rufe haka yake ji”

“Toh daman ina ke ina kwanciyar hankali da farinciki Hajiya? Mai aiki ta aure miki miji? Ai haka suke shiyasa ake cewa ďan iska na birni shege na kauye sai tsoron ɗansa, ai da zarar sun yalla ido sun ga ana jindadi a gida to sai sun aure miki miji, ita wannan shegiyar gorar Afra da ta fahimci duniya kin ga duk bokonta bata son ko mai raino balle kuma wata mai aiki”

“Tana da gaskiya Wallahi, sai dai haka kuma ba zai hana ďan mu kara aure ba”

“Aure kadai? Ai sai ta bar gidan nan matukar ina raye, duk wata mallaka da ta yi ma ďana sai na kwance ta, kuma ki zuba ido ki gani ba dai wannan Malamin ya iya aiki ba zaki sha mamaki”

“Yanzu so nake ki shirya mu kai masa sallama kuma na sake fada masa bukatar domin ina gudun kar ya maida ita”

“Karki damu, bari sai kura ta laba zamu sake komawa, daman ai na fada masa duk abun da aka ba shi karin alkalami ne kawai, biya sai bukata ta biya”

“Lallai kuwa zan masa biya mai kyau, domin ya yaye min bakincikin da nake kwana na tashi da shi, a kullum burina Iyami ta tafi ta bar min miji, yau kuma wannan burin ya cika Alhamdulillah”

Dariya suka yi a tare sannan Hajiya Kaltume ta yi mata sallama ta sauke wayar tana jin kamar an mata bushara da gafara.
☆❁ ❁☆

4️⃣

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”

Shi ne abun da Hajiya Binta take ta nanatawa idonta a rufe domin danta be zo mata da labari mai dadi ba, a cikin matansa daga wanda ta rasu har wadanda suke a gidansa yanzu babu wanda take so irin Iyami, domin macece wadda ta san kanta take bata girma take rawar jiki da ita tana kyautata mata kamar uwarta.

“Subhanallahi Tsoho baka kyauta ba, ka yi gaggawa kuma daman gaggawa aikin sheidan ne, ina ma baka aikata ba ka dan daga mata kafa ko kuma na turata gidansu har sai ka samu natsuwa”

Cikin wani kalar rauni da rashin sukunin abun da ya aikata ya sake noce kansa kasa ya sauke ajiyar zuciya.

“Hajiya natsuwar ce ta gagare ni samu, ba yau na fara jin bana da sukuni idan bana tare da Iyami ba, ji nake kamar wani abu ne a saman kaina, sai a yanzu da na sauwake mata sannan na ji nauyi ya sauka, ni kaina ina son Iyami amman bana jin natsuwa a zamantakewarmu yanzu, kuma na yi ta addu’a ina fatan samun sauki abun amman hakan ya gagara wata kila sakin shi ne mafi alheri daman aure rai ne da shi”

“Har saki nawa ka yi mata tsoho?”

“Daya na yi mata Hajiya”

“To da sauki idan abubuwa suka daidai wata kila za a iya gyarawa, ko dan yan diyanta Tsoho, dubi Hurriyya da Hamad ga cikin dake jikinta yaran nan ba za su taba jindadin zama a gidan idan bata ciki ba, ko ma kallon iyayen kowa na nan ta su bata nan sai ya saka su jin wani iri”

“In Sha Allahu zan ba su duk wani jindadi da farinciki da yaya suke bukata a gurin uwa da uba, ban taba fadar maganar nan a gaban kowa ba sai yau a gabanki, Hajiya duk cikin yayana na fi kaunar Hurriya, saboda kokarinta ga kuma lalurar da take tare da ita, Allah ya saka min tausayin yarinyar nan, fitowa daga gida zuwa nan Wallahi yaran nan kawai nake ta tunani a raina”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected