Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ashe baki da hankali har yanzu? Ke yanzu duk wannan abun da ya faru har sha’awar auren Yasir kike…”
“Allah yana fitar da mai kyau daga mummuna gwaggo kuma yana fitar da mummuna daga mai kyau, ni ban ce sai na auri Yasir ba, ban zan iya auren mutumen da zuciyarku bata gamsu da shi ba, amman dai na sani farinciki ko wane ďa yana tare da uwarsa, idan aka kai Hajiya Gidan yari, Yasir ba zai sake farinciki ba, ni kuma nawa farinciki yana tare da Yasir, dan Allah Yaya Iyami karki saka a rufe ta Allah ya riga ya gama miki komai…”
Tassss Gwaggo ta wanke fuskar Rukayya da mari.
“Ke yanzu soyayya har ta isa ta rufe idonki ki ce kar a hukunta Kaltume akan abun da ta yi?”
Amma ta bata rai sosai tana kallon Gwaggo da alamar dake nuna bata jidadin marin da Gwaggo ta yi ma kanwarta ba.
“Da baki mareta ba Gwaggo, soyayya babu abun da bata sakawa, idan har so zai rufe idon mutum kamar Jamal ya yarda da Hurriya ya aureta a lokacin da take cikin tsananin rayuwa da damuwa, me zai hana so ya rufe idon Rukayya? Kuma gaskiya ta fada, ni Allah ya gama min komai daman idan mutum ya cutar da kai karka ce sai ka rama kawai ka bar shi da Allah sakamakon da yake zuwa daga gurin Ubangiji ga azzaluman mutane mai tsanani ne, irin wanda ruhi baya iya jurewa. Kuma Yasir ya cancanci ko wace kalar alfarma a gurina ko a gurin yayana, yana da kirki be taba nuna min banbanci da mahaifiyarsa ba ko sau daya…”
“Ko ma dai minene ba za a kyale ta ba, tun da na gane hankalinki da nata ya zama iri daya”
“Daman maganar ba a gurinmu take ba, tana gurin jami’an tsaro ne sai yadda suka yanke..”
Gwaggo ta ja tsaki tana jin haushin yadda Amma take da sanyi a wannan bangaren. Hurriya ta karasa ta zauna a kusa da Rukayya tana bata hakuri.
“Barta ta yi ta kukan, ta dade bata mutu ba yara ba su da kunya soyayya na rufe musu ido su kasa ganin daidai”
Cewar Gwaggo cikin tsawa. Hurriya dai bata ce komai ba ya ta tashi ta fice daga falon zuwa bangaren Hajiya Kaltume a nan ta samu kofar falon a bude bata yi tunanin babu kowa a ciki ba sai da ta shiga, tun ranar da yan’uwan Hajiya Kaltume suka tafi da ita suka tafi tare da Khairy da Ruma. Yayanta ta gani zaune ya hade kai da guiwa yayi shiru gwanin tausayi. Ta matsa kusa da shi ta zauna a kasa sai ya dago ya kalleta da karfin hali irin na maza sai ta yayi mata murmushi.
“Hurriya…”
“Yayana ka yi hakuri dan Allah na san baka cancanci haka ba..”
“Kaddara bata duba cancanta, hakuri kuma ya zame mana dole. Sai a yanzu nake kara jinjina kokarinki a lokacin da Amma ta tafi ta barki, yau ji nake kamar ba ni da kowa a duniyar nan, i Felt Empty, da zarar na tuna cewar Hajiya bata da lafiya sai ta ji komai ya tsaya min cak, and ba ma wannan ba taya zamu kalli duniya da abun da Hajiya ta aikata..?”
“Kowa yana kuskurea Yayana, na tabbatar da ace kana sane ba zaka bar Hajiya ta aikata haka ba, komai ai kaddara ne ka fada, ya kamata idan ta same mu mu rumgume ta da hannu biyu…”
“Haka ne Hurriya Allah ya ba mu ikon cinyeta…”
“Ameen”
Ta amsa tana kallonsa cike da tausayawa.
CAPTAIN POV.
Da zazzabi ya isa gidansa, har ya faka mota yana kokarin fita sai kuma ya tuna da wani abun da ya kamata yayi, hakan ya saka shi komawa motar ya sake yi mata key mai gadi ya sake bude masa gate. Unguwarsu Salim ya nufa ya shiga har cikin gidansu ya aika a kira shi, mai aikan yaje ya dawo ya sanar masa da Salim baya gidan. Captain ya sake juya kan motar yana tunanin a ina zai ga Salim a yanzu, ya kira shi a waya ko kuma dai ya gwada ziyarar gurin da yake dan taba zuwa da dare. Da shawara ta biyu zuciyarsa ta aminta dan haka ya nufi wani gurin da Salim yake yawan zuwa idan yana free da dare.
Captain ya faka motarsa waje ya fito ya shiga gurin yana duddubawa sai kuwa ya ci karo da Salim zaune shi kadai yana lasa wayarsa. Captain ya karasa gurin yaja kujera ya zauna, Salim ya dago ya kalleshi gabanshi na dan faduwa.
“Na dauka ka ce babu ni babu kai, me ya kawo ka nan? Zuwa ka yi ka ci min mutunci a gaban mutane?”
“Ba wannan ya kawo ni, zuwa na yi na buga maka warning na karshe, kuma na fada maka abin da baka san na sani ba…”
Captain ya bude wayarsa ya nunawa Salim duk wani evidence da ke nuna shi ya aikata abun da yake zarginsa.
“Ka cutar da Hurriya Salim, saboda bakar zuciyarka ka runtse ido ka yada ďan’uwanka da yarinyar da baka isa ka hana ni sonta ba, hakan duk be maka ba sai da ka sake aikata a karo na biyu bayan mun yi aure, wannan abun zai iya saka ka rasa aikinka ba wannan aikin Soja ba har wani aiki a nan gaba ma, kuma zai iya daureka a gidan kaso ka sani ko? Kuma zai iya lalata character dinta a idon duniya… Ina ka samu hotunan?”
Yayi shiru zuciyarsa kamar zata cire sabisa yadda take bugawa da karfi.
“Wata rana ne na dauki wayar Adam zan tura abu, sai na ci karo da hotunan, abun ya daga min hankali sosai kuma na yi mamaki amman a lokacin na yi tunanin da gaske Hurriya ta aikata hakan da Adam ne, ban ce masa komai ba na tura hutunan da abun da zan tura na goge na bashi wayarsa, har sai zuwa lokacin da muka tafi Ethiopia tare na ganka kana kallon hotunanta da ban san a ina ka samu ba, sai ya fahimtar da ni son Hurriya kake yi, kuma ka san ka yi betrayed dina tun da ka san ina son yarinyar nan be kamata ka so ta ba…!”
“Saboda ubana ne kai? Kamin na nuna ina son Hurriya kai baka nuna ta nuna bata bukatarka ba? And let me tell you something Wallahi ban fara tausayi Hurriya da taimakonta saboda na fada soyayya da ita ba, ban kawa wannan a kusa ba, sai tsintar kaina na yi abun kuma haka Allah ya tsara, me yasa baka karvi Kaddara ba ka hakura sai ka zabi cin zafinta…”
“Na yi tunanin ta aikata da gaske ne, shiyasa tun muna Ethiopia na saka aka yada hotunan, kuma na yi tunanin hakan zai canja alakarku”
“Ka bari zuciya ta yaudareka ka aikata amininka mummunan aiki na cin mutuncin Iyakinsa, a yau da na gane gaskiya idan ina so zan iya hukunta ka Salim ta ko wace siga, amman ba zan yi ba, kasan saboda me?”
Salim yayi shiru ya kasa cewa komai.
“Ba zan manta alherinka a gareni ba, kuma saboda mahaifiya zan daga maka kafa, amman dai alaka da ni da kai na yankata har abada, and duk lokacin da ka sake batawa Hurriya rai zaka rasa damar abubuwa da yawa”
Captain ya mike tsaye ya bar shi a gurin yana gumin tsoro da kunya a lokaci daya. Misalin Tara da rabi na dare Hurriya na zaune tare da Hamad da Amma suna hira kiran Captain ya shigo wayar Amma har ta yi kamar ta bawa Hurriya kai tsaye kuma ta amsa suka gaisa sannan ya tambaye matarsa.
“Amma Hurriya na kusa zan yi magana da ita ne…”
“Eh”
“Hurriya ga mijinki zai yi magana da ke”
Hurriya ta tashi ta karbi wayar ta koma ta zauna.
“Ke shiga ciki mana idan magana ta sirrin yake son yi dake fa?”
Ta tashi ta nufi stairs domin cika umarnin Amma. Sai da ta shiga dakin sannan ta rufe kofa sannan ta ce.
“My Noor ya jikin?”
“Ba dadi har yanzu zazzabi nake ji, i just call to say Hi and kin ci abinci?”
“Na ci, kai fa ka ci…”
“Na sha tea shi kadai na ji ina so, ya kike..?”
“Lafiya kalau”
“Ya Baby na?”
Ta bata rai kamar yana gabanta.
“Ba kyau ka daina”
“Me ye ba kyau? Tambayar babyn nawa?”
Ta masa banza sai yayi dariya.