Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Hajiya ta daki cinyarta
“Wallahi ba zan hakura ba, sai ta dandana kudarta, kuma Wallahi na fi karfinta bokanta yayi karya Wallahi, Iyami ma ta kara da ni ta bar ni balle ita bukkar banza, mai karyar arziki sai ka ce kanta farau arziki duk ta fi ta cikawa mutane gida da bakin kuri da iyayi ita diyar mai kudi, mun ji karuna duk arzikin ubanta be kai karuna ba, ni kuwa sai na zame mata fir’auna a cikin gidan nan”
“Subhanallahi Hajiya dan Allah ki daina irin maganar nan haba”
Yasir ya fada cike da damuwa, domin baya jin yadda matan ubansa suke samun tsabani a gidan.
“Babu ruwanka babu ruwanka idan ba zaka taya ni yaki ba karka sake shiga tsakanina da kowa, dan iya. Ke kuma yar gadon munafurci bace min da gani”
Ta karasa tana watsawa Hurriya dake tsaye tare da Hamad harara, babu bata lokaci Hurriya ta juya ta fice daga falon, Hamad kuma ya tsaya a gurin kamar ba zai tafi ba, irin yadda yara masu fama da rashin kunya suke yi, sannan ya fice yana wani tukuki saboda saka sunan uwarsa a fadan da Hajiya Kaltume ta yi kuma ta kira Hurriya da yar gadon munafurci.
____________________
Masu karatun suna hango abun da nake hangowa?
Akwai Bomb fa ba karami ba? Fatan dai kun shiryawa tafiyar?
Idan kun karanta ku yi sharing
☆❁ ❁☆
Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy
https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy
1️⃣3️⃣
Da kallo ya bi Hurriya da Hamad har suka fice sannan ya kalli Hajiya Kaltume ya dauke kai ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa abun da ya fara yi shi ne duba gurin da ya aje gilasan Hurriya, amman be ga ko daya ba, a nan ya fara tunanin ko ya canja musu gurin ajiya ya manta, haka ya bi komai na dakin ya duba ba gilasan babu alamarsu, fitowar yayi mamaki duk ya cika fuskarsa ya sauka kasa sai ya samu mahaifiyarsa a gurin da ya barta zaune sai dai wannan karon waya take amsawa, gefenta ya zauna a hannu kujera har sai da ta gama wayar sannan ya tambaye ko ta dauka.
“Me zan yi da gilasai kuma? Komai dai ni, ubanka ya dora min laifi matan ubanka su adabe ni kai kuma yanzu ka zarge ni da satar gilasan Hurriya saboda ga Kaltume makiyiyarta ko?”
Maganar Hajiya bata masa dadi ba kuma ya san duk wani kalami da zai dora bayan nata a yanzu ba zai fahimtar da ita. Dan haka ya tashi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi dakin yan’uwa daya bayan daya ya bi yana tambayarsu kowacce tace masa bata dauka ba, Khairi har da hadawa da rantsuwa saboda ta fi kowa rashin tsoron Allah.
‘Toh ko Hurriya ta zo ta dauka ko Hamad ban sani ba?’
Ya tambayi kansa, sai dai ya san ba su taba masa haka ba, idan tana bukatar abu zata yi masa magana kuma idan ma ta dauka zata fada masa. Fitowa yayi daga bangaresu ya nufi bangaren Momy, kamar ance masa juya ka gani, yana juya ya kalli bangaren Appa sai ya hango Hurriya tsaye tare da Appanta ta rike hannunsa tana ta bata rai da alama makiya take masa kan wani abu. Fasa nufar bangaren Momy yayi sai ya nufi bangaren mahaifinsa domin tambayarta ko ta dauko gilashin be sani ba.
“Appa dan Allah daga wannan ba zaka sake yi ba”
Ta fada cike da shagwaba tana kara rike hannunsa.
“Haramun ne, ba kyau Hurriya ni bana sha’awar irin abubuwan nan”
Appa ya fada yana kallon Yasir da ya iso gurin fuska a sake.
“Me take so Appa?”
“Birthday kuma ka sa be da kyau ba al’adar mu ba ce hausawa wannan dabi’un turawa ne”
“Oh Appa yanzu kai ya waye fa, ba wani abun ba ne kawai dai ana samun tsabanin fahimta ne ga mutane, kuma yanzu zamani ya canja ba kamar lokacin baya ba”
“Ko zamani ya canja ni ban canja ba Yasir, abun da duk ba tarbiya ba bana sha’awar”
“Appa sau daya zamu yi fa, daga wannan ba zaka sake ba? Appa please kawaye na duk ana musu sai ni”
Tana maganar tana son yin kuka Appa yayi murmushi.
“Shi ke nan na ji, za a dafa shimkafa fara ayi sadaka”
Ta buga kafa daya a kasa tana kukan da babu hawaye, Yasir kuma ya saka dariya.
“Appa dan Allah dai Appa”
Ba kasai Hurriya take zuwa masa da bukata ba, kusan duk wata bukata da take gabatar masa da ita kidayayyyiya ce, hakan ya sak idan ta zo masa sai ya biya mata ko dan tausayinta da yake na lalurar dake tare da ita, balle kuma yanzu da tausayinta ya ninku a zuciyarsa saboda rashin Amma a gidan, sai yake ganin yaransa kamar wasu marayu da uwarsu ta mutu ta bar su.
“Na ji amman daga wannan ba za’a sake ba?”
Ta amsa da sauri tana tsalle.
“Na yarda Appa na yarda Allah ya saka da alheri, Appa Allah ya biya maka bukatunka na alheri ya rabaka da Hajiya Lafiya ya kara buda maka a kasuwanci ya kyautata karshenka”
Ta masa kwatankwacin addu’ar da Amma take masa idan yayi mata wani abun kyautata da ta ji dadi. Appa ya shafa kansa yana jin zuciyarsa da tausayin da be san na minene ba. Yasir ma murmushi yayi yana taya ta murna yadda Appansy ya amince da wuri.
“Bari mu fara neman Gift din da zamu bawa mai birthday”
“Har da kyauta ake badawa?”
Appa ya tambaya sai Yasir ya amsa masa.
“Eh Appa idan mutum yayi birthday ana ba shi kyau sosai ma, kowa da kalar abun da yake ba shi”
“Oh toh saboda ki ci kudinmu kike son yi birthday kenan?”
Cewar Appa yana kallonta da zolaya, sai ta saka dariya kamar ba ita ta rufe idonta.
“Appa ba da kai ba an yafe maka”
Shi ma dariyar yayi, ya bita da kallo domin tuni ta nufi bangaren Momy domin labartawa Hamad cewar Appa ya yarda zai mata birthday kamin ya isa gurin hawaye ya cika idonta domin ta saba idan aka mata albishir Amma take fara fadawa sai dai a yau babu Amma a gidan kuma ta san babu wanda zai taya ta farinciki da murna sai dan’uwanta. Tana ahiga falon sai ta ja ta tsaya tana kallon Musib da ya hada hannayen Hamad ya rike yana zabga masa mari.
“Ba zaka yi magana ba? Waye yaje ma fadawa Appa karya da gaskiya ya zo ya rufata ta fada? Tsakanin kai da Hurriya”
“Ni ce”
Ta amsa kai tsaye domin ba zata jure ganin ana duka dan’uwanta ba da yaki yayi magana kuma ya ki yayi kuka sai dai idanuwansa sun kada sun yi ja sosai sai wani cika yake yana batsewa alamar zuciyarsa ta gama kawowa.
“Okay zo nan bakar mufuka wato daga dawowarku za ku fara hada Momy fada da Appa ko?”
Bata zo ba kamar yadda ya bukata sai dai kuma bata matsa daga inda take tsaye ba ssi hawayen da ta shigo da su suka fara sauko mata, Hamad ya juya ya kalleta har lokacin be ce komai ba, daman tun shigowarsa falon Musib ya rike shi wai sai ya fada masa waya fadawa Appa gulma har ya shigo yana mata fada ta yi kukan, Hamad ta kafiya ya ki magana hakan ya saka Musib dukansa. Musib ya saki hannun Hamad ya nufi gurin da Hurtiya take tsaye ya fara kai mata duka sai ta boye fuskarta ta fara kuka, yadda Hamad ya nufo gurin da suke tsaye sai ka dauka zai yi dambe yayansa Musib ne, ficewa yayi daga falon Musib na kokarin rikoshi ya fisge ya fice da gudu, be zame ko’ina ba sai gurin da Garden din gidan yake ya samo manya manyan duwatsu ya dauko har uku ya fito da su ya nufi gurin da Motar Momy take ta fara jefan gilashin a take ya fasa mata gilashin mota ya koma dayan bangaren ya sake jefawa. Kamin yayi na uku Appa da Yasir da suke tsaye a gurin da Hurriya ta bar su, suka iso gurin da sauri domin sun lura da lokacin da ya dauko duwatsu sun san ba za’ayi mai kyau ba, Yasir yayi saurin rike Hamad.