Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Toh Allah dai ya sa lafiya wannan kira haka tun da safe?”
“Lafiya kalau sai alheri, Hajiya Fatee yau bana da inda zan saka ki, bani da wanda ya fi min ke a duniyar nan, Hajiya Fatee kin biyani Allah dai ya bar zumuncinmu”
Cikin mamaki da farinciki kawar tata ta amsa.
“Toh Ameen, amman ba ni an sha me ya samu?”
“Komai ma ya samu Hajiya Fatee yanzu zan fara samun kan mijina, abun da na kwashe shekaru ina nema ban samu ba, Hajiya Fatee yau Alhaji da kansa yake ta fada saboda Iyami da mahaifinta sun kira shi a waya, har yake fadar shi yanzu baya son wani abun da ya shafi iyami ya hada shi da ita”
Hajiya Fatee ta saka dariya irin mai ruguzawar nan.
“Hajiya Kaltume ni kaina na gasgata aikin Malamin nan, kuma na yarda ba da wasa yake aikinsa ba, domin ni na fi kowa shaidar hakan tun da ga ciki ya kwanta lafiya kamar babu shi, wata kila ma cireshi yayi gaba daya, amman har asibiti na tafi an auna babu ciki babu labarinsa”
“Ni Wallahi da farko nan na dauka ko aikin be yi ma, kwana nawa aka dauka amman shiru sai yau na fara ganin ikon Allah”
“Ai daman wani abun haka yake, kin manta yadda muka yi na auren Iyami? Shi ma ai sai da kika fara korafin be yi be yi ba, har ya ce kin yi gajin hakuri, yanzu ba gashi ta tafi ta bar miki idan ba”
“Na yarda, tabbas ni kuwa zan saka masa da sakamako mai kyau, sai yayi alfahari da ni”
“Ni ma ai na fada masa idan yayi abun da zai raba auren Fadeel da Afrah sai na masa kyauta mai tsoka da sai ya kasa mantawa da ni, kuma ya ce zai yi, sai dai ta inda lamarin ya sanyaya min guiwa cewar da yayi idan yayi mata aika dawo masa ake da ita”
Hajiya Kaltume ta rike baki. “Ai kin san bata tsawaya kanta ba, ita ma shigen shigen take”
“Ai na sani, shiyasa ta mallake min da komai sai Afrah gaba daya baya jin maganar kowa sai nata, kuma bana da ikon zaginta a gabansa sai ya fara masifa, ni daman tun farko bana son aurenta da yaron nan Wallahi, Allah dai ya riga da kaddara ne kawai”
“Ki sa ido ki yi kallo kamar yadda Iyami ta bar gidana, Afrah ma sai ta bar gidan danki da yardar Allah”
“Haka nake fata Hajiya Allah ya amsa”
“Ameen”
Hajiya Kaltume ta aje wayar tana murmushi kamar wadda aka yi ma bushara.
“Hmmmm Iyami…. Lallai kin zama labari a gidan nan, yaranki ma da yardar Allah sai sun zama su da babu duk daya a gidan nan”
Ta nufi bakin gadonta ta zauna tana kokarin sake yin wani kiran Khairi ta shigo dakin ta zauna kusa da ita ta kwanta jikinta.
“Hajiya yaushe Ruma zata dawo ne?”
Hajiya ta yi saurin saka wayar key tare da gefenta.
“Babu jimawa Khairi, mahaifinki ne yace a bashi lokaci zai nemi ragi, kuma kin ga ai ana neman ragi a komai”
“Toh Hajiya da zai yarda da sai ya bada kudin ya karbo Ruma, albashi Hamad din a barsa sai an shirya daman ya fitini kowa a gidan nan”
“Ai kin san ba zai yarda ba, kuma mutane ma sai su saka mana ido, ace saboda uwarsa bata gidan ne, kara dai a karbo su tare gaba daya”
“Allah sarki Ruma, Allah dai ya tsare ta”
“Ya ma tsare In Shaa Allah ba za su mata komai ba, ai yarinya ce kuma kin ga ba ita kadai suka dauka ba ko dan ganin idon Hamad za su raga mata tun da dan’uwanta ne”
“Allah yasa”
“Ameen tashi kuje ku karya, ni wanka zan yi yanzu”
“Na karya ai”
“Yayi kyau Maama da Salma duk sun karya? Yayanki fa?”
“Ban sani ba gaskiya”
“Je ki fada masa ya fito ya karya”
Khairi ta tashi ta fice daga dakin, sai da Hajiya Kaltume ta tabbatar ta rufe kofar dakin sannan ta fiddo wayarta ta fara danne danne. Misalin sha daya na safe Bappa da Gwaggo suka dira a gidan, Bappa ya faka a harabar da ya saba fakawa duk lokacin da wani abu mai muhimmanci ya kawo shi gidan, duk kuwa da kasancewar Iyami bata gidan. Shi ya fara fita sannan Gwaggo ta fito tana sanye fa farin hijabinta.
“Ki fara shiga ki yi magana da Hajiya Kaltume a sallamo mana Alhaji mu yi magana da shi”
“Ko kuma dai ayi mana iso ba”
Gwaggo ta gyara masa domin a ganinta ba bara ko roko suka zo gurinsa ba da za ace a sallamo musu shi. Bappa dai be sake cewa komai ba domin be shirya musu da Gwaggo a yanzu ba, ya san duk gyaran da zai mata ba zata fahimta ba. Gwaggo ta daga kai ta kalli apartment din Amma da kyau sai ta ji ranta ya bace, domin a yanzu yarta bata cikin gidan ba kamar da ba. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fito ta nufi bangaren Hajiya Kaltume, ba dan zuwan ya zame musu na dole ba ba za su zo a gidan ba, musamman ma ita da Hajiya Kaltume har Hajiya Nafisa basa girmamawa, Hajiya Nafisa na yi musu kallon matalauta masu kwadayi Hajiya Kaltume kuma na yi musu kallon maciya amana wadanda suka hanata zaman lafiya da kwanciyar hankali, Appa ne mai girmamata idan yaje mata ko kuma ita ta zo gidan ya rasa ina zai dauke ta ya dora tsabar farinciki da girmamawa. Ta murda kofar falon ta shiga da sallama fuskarta dauke da damuwar data kasa boyuwa.
Salma da Maama suka amsa mata ba dan sun ga fuskarta ba, domin su ma ba girma suke bata ba. Yasir ya aje cup din hannunsa da sauri ya baro dinning din ya nufota yana mata sannu da zuwa har da dan risinawa.
“Sannu Yasir ya hakurin lamarin nan?”
“Alhamdulillah Gwaggo Bismillahi zauna”
Ya nufi kujerar da sauri ya dauke pillows din da suke kai ya mata mazauni.
“Ya gida ina Rukayya?”
“Gida Lafiya kalau, Rukayya ta tafi makaranta tun safe”
“Ya Hurriya da Amma?”
“Toh Alhamdulillah Hajiya Kaltume na ciki? Tare muke da Malam ai”
“Oh… Ya tsaya a waje?”
“Eh ai ba jimawa za mu yi ba, magana kawai za mu yi da Mahaifinku”
“Okay Salma shiga ki kira Hajiya bari na tafi gurin Bappa”
Salma ta motsa hanci ta mike tsaye ba tare da ta gaishe da Gwaggo ba ta nufi upstairs, Maama tun da ta kalli Gwaggo sau daya bata sake juyowa ba balle har ta gaishe ta. Ba abun mamaki ba ne a gurin Gwaggo domin sun saba yi mata haka kishi suke taya uwarsu. Daga kiran Hajiya Salma bata sauko ba balle Gwaggo ta san halin da ake ciki haka ta zauna a gurin har kusan minti ashiri sannan Hajiya Kaltume ta sauko tana sanye da wata gizna mai fari da baki irin ta mutanen nijar ta irin aikinsu a gaban rigar da ta sauko mata har guiwa.
“Gwaggo ce yau a gidan na mu”
“Ni ce, halan Salma bata fada miki na zo ba Hajiya Kaltume”
“Ta fada min ba shi na sauko ba? Ina dan abu ne shiyasa Allah yasa dai lafiya”
Gwaggo ta tabe baki ta girgiza kai.
“Ba lafiya ba kan, tun da kowa ya san abun da ya faru, tare muke da Malam muna son magana da Alhaji ne”
Hajiya Kaltume ta zauna tana yamutsa fuska irin an takura musu din nan, kamin ta fara magana da izza.
“Oh Allah sarki, dazun ma ai na ga Bappa ya kira Iyamin ma ta kira, Alhaji sai fada yake Gwaggo ba a haka, ku baku san shirinsa ba, kuna son daga masa hankalin ne kawai shi ma fa ya damu da yaran nan kuna neman ku daga masa hankali”
Gwaggo ta nuna Hajiya Kaltume da yatsa.
“Ke Kaltume ke kin sani ko ban haife ki ba, na yi kanwa da ke, dan haka na cancanci girmamawa a gareki ko dan Iyami”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi da ya fi kama da yar siririyar dariya.
“Wannan kuma ai da ne Gwaggo, yanzu babu wannan alakar, kuma da kuke neman daga mana hankali ni ma fa tawa yar tana can tare da Hamad aka sace su, ko kuma ita ba mutum ba ce?”
Gwaggo ta mike tsaye.
“Kwarai kuwa mutum ce, shiyasa ai na ganki kin sha wanka kina ta far’a da jindadi an sace miki auta, gashi nan ai ya nuna a fuskarki”