Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Kai miye haka?”
Sai a lokacin Hamad ya fashe da kuka yana maida magana.
“Ya Musib ya yi min mari hudu, kuma gashi can yana dukan Hurriya, wai ya ce mun yi munafurci mun hada Momt da Appa fada”
Appa da ransa ya bace saboda abun da Hamad aikata, a take abun da ya fada ya gusar da bacin ran abun da Hamad yayi. Ya nufi falon fuska a hade Yasir dake rike da Hamad har lokacin yana ta zillo sai ya sake kwaso wasu duwatsun ya fasa motar ya bi bayan Appa. Da karfi Appa ya tura kofar falon ya shiga sai ya samu Hurriya duke kusa da kofar ta rufe fuskarta tana kuka marar sauti.
“Musib…!”
Appa ya aika masa da wani irin kira da karfin murya mai razanarwa. Musib dake boye kitchen ya fito baki kofar kitchen din yana amsa kiran muryarsa na rawa.
“Na’am…”
Appa ya taka ya karasa har inda yake ya dauke shi da mari. Daidai lokacin da Momy ta sauko tare da Namra.
“Akwai wanda na taba duka cikinku? Akan wani dalili zaka dokesu? Kai da ya kamata ka ga wasu musguna musu ku shigar musu kai zaka saka hannu da kanka ka dokesu? Karka sake! Ina gargadinka ba su ba Hurriya da Hamad kadai ba duka yayana kar ka sake saka hannu ka dake su”
Appa ya juyo ya kalli Momy dake tsaye kamar hoto tsabar mamaki ya ce.
“Na rantse da Allah idan wani ya sake dokar min ƴaƴa sai na masa abun da zai yi bakinciki da na kasance ubansa, ban doka ba ba zan yarda wani ya dokar min ba”
“Saboda ƴaƴan Iyami ne?”
Momy ta tambaya tana jin wani tuƙuƙi a zuciyarta, shi kuma ya amsa mata ba dan suna ƴaƴan Iyami kaɗai ɓa sai dai baya daukar a zalinci kowa, amman saboda ta ji haushi sai ya amsa mata da haka.
“Eh saboda suna Ƴaƴan Iyami…”
Yana fadar hakan ya juya ya fice daga falon, a nan ma Yasir da har lokacin yana rike da Hamad dake ta jan numfashi da karfi saboda zuciya, ya rufa masa baya tare da Hamad din, Hurriya kuma da ta tuni kuka yayi mata bankwana ya tafi ya barta tsaye tana kallon dramar da ake ta bi Appa da kallo kamin ta juyo ta kalli Momy.
“Ba hakka, haka ne… Daman ance maza ke bude wata kofar wani lokacin yau na gani, kuma ya bude muku kofa, za ku wahala a gidan nan. Musib yi hakuri”
Ta juya ta fara hawan stairs din daman bata sauko gaba daya. Musib ya watsawa Hurriya wani mugun kallo ya dauke ido ya bi bayan mahaifiyarsa. Zaunawa Hurriya ta yi a gurin ta rafka uban tagumi, gaba daya kwakwalwarta ta rike ce ji take kamar ba zata iya dauka ba.
*** *** ***
BAYAN WATA UKU….
Tun daga lokacin sai Hurriya da Hamad suka samu salama, ta duka Hamad kuma ya samu ta magana, ba a dukansa ba a fada masa magana marar dadi, saboda ana tsoron ya fadawa Appa, Musib da Miwan ma sai duk suka shafa musu lafiya, sai dai tsanar da Hajiya Kaltume take mata sai ya karu, har ta kai a gaban Hurriya Hajiya Kaltume take zagin Iyami sai dai ba zata yi a gaban Hamad ba, Hurriya tana jin zafin abun sosai sai dai bata taba fadawa kowa ba sai dai ta bar abun a zuciyarta. Hurriya na tsaye ita da Hamad suna wanke motar Yasir Hajiya Kaltume ta fito rike da jakarta Yasir din yana bayanta rike da makullin mota.
“A gaishe da ku, amman idan Appa ya gani karku ce ni na saka ku ku ce ku kuka saka kanku dan kar ya fara fada ya ce ban kai wankin mota ba na saka ku yi”
“Hamad ya fada masa zamu wanke maka mota ai kamin mu fara, ya ce mu je mu yi Allah ya mana albarka”
Hurriya ta amsa tana watsawa motar ruwa, domim wankin mota yana daga cikin abun da yake matukar burgeta, kuma ta taba yi sau daya a motar Appanta tun a lokacin da Amma take gidan. Hajiya Kaltume ta kallesu irin kallon nan na rasa ya zan yi da ku ta dauke kai ta nufi motar da za su shiga, tana nufar motar gabanta na kara tsananta faduwa har sai da taja ta tsaya.
“Yasir anya ba za mu fasa tafiyar nan ba? Gabana sai faduwa yake Wallahi tsoro nake ji ganin nake kamar wani abun zai sake faruwa”
Yasir ya ce.
“Babu abun da zai faru Hajiya dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi imani da Allah, kuma kin ga tun da abun nan ya faru baki sake fita ba, yau kusan wata uku kenan dole ki ji haka”
Ta girgiza kai domin bata gamsu da kalaman Yasir ba.
“Ko dai mu hakura har wani lokacin?”
“Hajiya idan baki kawar da komai a ranki ba, babu ranar da zaki sake fita, rasuwa nawa aka yi baki je ba, ga haihuwa ba an yi ba daya ba amman baki fita ba, Hajiya Fatee ma tare abun nan ya same ku amman zuwanta biyar gidan nan, dan Allah ki daina tsoro babu abun da zai faru da yardar Allah”
“Toh Allah yasa”
Ta amsa tare da bude motar ta shiga ba dan ranta ya so ba, sai dan fitar ta zame mata dole ne saboda kiran da Hajiya Fatee ta yi mata tana kuka ba zata fita ba, balle kuma da ya kasance gidanta na farko da zata fara zuwa tun bayan da aka yi kidnapping dinsu, sai take ganin kamar hakan zai sake faruwa ne. A hankali Yasir ya rika jan motar suna tafiya yana dan taba mata hira, ita kuma ta kasa cewa komai sai kallon gari take har lokacin tsoro be fice ta ba, garin kuma tana ganin kamar ya sake saboda dadewa da ta yi bata fita ba.
“Bismillahi”
Ta furta yayin da ta bude motar zata fita, zuciyarta nata rawa, Yasir ya rakata har cikin falon Hajiya Fatee, yan aikin Hajiya Fatee suka fara gaisheta.
“Lafiya Kalau Ina Hajiya Fatee”
“Tana dakinta”
Hajiya Kaltume ta juya ta kalli Yasir.
“Bari na kirata ku gaisa”
“Okay”
Ya nufi kujera ya zauna, Hajiya Kaltume kuma ta nufi dakin Hajiya fatee ta tura kofar ta shiga da sallama. Kuka ya hana Hajiya Fatee amsawa sai dagowa da ta yi ta kalleta da idanuwanta da suka gama kumbura.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, Hajiya Fatee abun har ya kai haka”
“Ya wuce, Hajiya Kaltume ina cikin bala’i da tashin hankali”
Hajiya Kaltume ta juya ta leka falon saitin da yasir yake zaune.
“Yasir ka tafi kawai idan zaka dawo daukata sai ku gaisa, amman fa da zarar na kiraka ka zo da sauri”
“Toh Hajiya”
Ya tashi ya fice cike da ladabi. Sannan Hajiya Kaltume ta koma dakin ta zauna kusa da kawarta da rabin kibar jikinta ta zube saboda tashin hankali.
“Wannan abu be yi dadi ba, yanzu miye abun yi?”
Hajiya Fatee ta share hawayenta ta kalli aminiyarta.
“Ban sani ba Hajiya Kaltume, wannan shi ne likita na uku da ya fada min haka”
“Hajiya Fatee duk laifinki, da tun farko kin yarda anje asibitin an duba lafiyarki da duk be kai ga haka ba?”
“Haba Hajiya, ina zan yarda aje asibiti a fadawa ďana abun da mutanen nan suka min? Tsoron kar ya kalleni da abin kuma kar bakinciki ya zauna masa a zuciya ya saka na ki amincewa da zuwa asibitin, kuma ni ma na san idan har ya sani ba zan samu salama ba”
Hajiya Kaltume ta rafka tagumi.
“Wallahi duk wannan Iyamin ce ta ja mana, ba zan tana yafe mata ba, ni kaina yanzu sanadinta har tsoron fita nake”
“Ni yanzu ba ta Iyami nake ba Hajiya ta kaina nake, kar asirina ya tonu, ga ni ta surukar da bata kaunata, ga makiyi babban tashin hankali kuma rashin auren nan, yau shekara goma da rasuwar Alhaji me zan fadawa duniya idan abun nan ya fito da shekaru na haka har da jikoki”
Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya.
“Hajiya ko dai daurewa zamu akara yin allurar nan ne? Ko Allah zai saka abun ya zube”
Hajiya Fatee ta dauki robar yawu ta tsargar da yawunta cikin ta aje ta kalli Hajiya Kaltume.
“Likita nan fa ya fada min, ta farko ma da na auna arziki ne, da yanzu na wuce, ni kadai na san azabar da na sha lokacin da aka min allurar nan kuma gashi bukata bata biya ba, kuma cirewar sun ce ko na mutu ko na yi rai ne”