Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Nawa ne kudin maganin?”
“Toh Hajiya dubu talatin ne, amman dai ko dubu biyu ko biyar aka taimaka min da su duk taimako ne”
“Kana da account”
“Akwai account Hajiya amman bana da shi aka Wallahi, kwanyar ce mun sha miyar kuka, daddawa duk ta kwashe basirar, tuwon dawa ma haka ake baza mana shi a ture, kai mun ci wuya Wallahi ga talaucin nan har yanzu be bar mu ba”
Hajiya Kaltume ta yi dariya har lokacin tsoro be fice ta ba, domin muryarsa ma abar tsoro ce balle kuma ka kalleshi.
“Kana da waya?”
Ya dan sosa kansa ya shafa aljihu.
“Wayar ce Hajiya ko an siya idan ka ji eh ya ne tana damun cikinka dole mu siyar mu siye abinci, line ma dari da hansi na siyar da shi shekaranjiya”
“Toh yanzu idan ina son magana da kai za mu yi kenan?”
“Ki fada min gidanki kawai zan zo na sameki har dakinki”
“Aa ni da Hajiya Fatee duk ba mu gama warkewa daga damuwar da muka shiga ba, baka san yan ta’adda suka kama mu ba?”
“Kai na ji Hajiya, zuwana talatin gidan nan sai ace min bata nan, wai wasu ne suka kamata, da an fada min ba za a biya sisi ba zan karbota ni sai a ba ni kudin, akwai mutanenmu fa masu harkar kuma ni Wallahi jan wuya ne, bana inda bana iya shiga, karfe be fasa ni bundiga bata kama ni sai dai ayi min tambo, danjar nan da kika ji ance Hajiya ni fa danja ne, uban fitina kuma bana tsoron kowa”
“Kai zaka iya aikata komai kenan Danja?”
“Zan iya komai Hajiya mun zubar da hannaye mun cire kafa, rai ma mun wulgar da shi barzahu, Allah dai ya shirya mu kawai”
“Shiyasa Hajiya take tsoron ka, ni ma ina gudun na janyo ka jiki na jawa kaina matsala”
“Kai… Kuturi”
Ya rike baki.
“Wai Hajja Fatee tsorona take? Ita din ai uwa ce ba za a mata komai ba, wani ma be isa ya mata ba balle kuma ni, ba dan ita ba da yanzu na barar da hanjin masu aikin nan nata, alkur’ane da yanzu ka ga hanta ya lilo shushushushushuuuuuuu”
Ya nuna yadda hantar zata rika raea idan ya sareta.
“Toh yanzu dai zan shiga gida, zan aiko mai aiki da number wayata idan ka samu waya sai ka kira ni mu yi magana, amman dan Allah ka daina damun Hajiya Fatee da yawan zuwa”
“An gama amman Hajiya yanzu akwai wani abu nan? Ina fatar ke ma kina da yan abubuwa yan timatinmai eh… Eh.. Kin dai gane”
“Zan aiko mai number tare da kudin da zaka hau babur ka koma”
Tana fadin haka ta yi gaba tana nufi gate zata koma ciki, shi kuma ya bita da kirari yana daga mata hannu.
“Chau chau chau chachachau lafiya lau ne Hajiya, Allah dai ya kara miki kwanciyar hankali ya kara miki ƙiba kai kana ganin Hajiyar nan ka san akwai manyan kaya, Allah ya kara sutura”
Cikin gidan Hajiya Kaltume ta koma ta shiga dakin Hajiya Fatee ta samu biro ta mikawa Hajiya Fatee domin ita bata iya rubutun ba.
“Rubuta masa number ta a nan”
“Numberki kuma? Me ya faru? Karki jawa kanki matsala fa irin wadannan ba su jin magana”
“Ke dai rubuta babu komai, ke na ke yi ma jihadin ai, wayo yake masa”
Hajiya Fatee ta karba ta rubuta mata number ta mika mata. Hajiya Kaltume ta bude jakarta ta dauko 3k ta hade ta takardar ta fita falo ta bawa mai aikin ta umarce ta da ta kai masa. Sannan ta juyo ta dawo dakin tana tambayar Hajiya Fatee ya aka karkare da Salame.
“Na kirata na mata bayani, ta ce ai ya canja line saboda rufe masa wacan da masu gidan line suka yi, amman yanzu zata turo min sabuwa numbersa kuma zata kira ta masa bayani”
“Haka nake son ji, to yanzu ki kwnatar da hankali ki kira ki fada masa ya shirya komai na sa ya zo garin nan zamu aika da mota a dauko shi a kawo mana har gida, daga nan sai mu gabatar masa da matsakarmu”
“Amman kina ganin zai yarda ya zo?”
“Hajiya Fatee miye kudi ba zai yi ba? Muradi dai abashi kudi shi kuma ya biya mana bukata kawai”
“Ni dai Allah yasa cikin nan ya tausu, idan ba haka na zan shiga uku ga shegiyar suruka zata ji dadi”
“Komai zai wuce Hajiya Fatee ki kwanatar da hankali”
Cewar Hajiya Kaltume ga aminiyarta tana murmushi.
IYAMI POV. .
“Iyami ba a zama haka, ke kanki kin san mijinki yana sonki, ga yaya yanzu kuma ga cikin nan da kika shiga watan haihuwa, kamata yayi ki nemi taimako idan ma wani asirin aka yi masa aka rabaku a karya shi, ki koma dakinki bana son ki haihu a gida Wallahi”
Amma ta yunkura da katon cikinta ta tashi zaune daker tana kallon Hindu dake maganar.
“Hindu, Wallahi ban taba yi ba, su kansu da suke ganin kamar asiri na yi ma Alhaji yake ta so na ko na malleke shi, ban taba bada naira biyar na ce a mallake min Alhaji ba, tsantsar biyayya ne kawai da kawar da kai da kuma jin maganar duk abun da ya fada, ni yanzu ko zaki dora wuka a wuyana ba zan iya fada miki sunan Malami daya da na sani ba a garin nan, ban taba yi ba, Gwaggo ma bata taba ta yi ba mu ba mu da kowa sai Allah”
“Na sani, to ai tambaya ake kin ga har na tsarin jikinki sai ki sha kuma ki bawa yayanki, domin su ma ba barinsu zata yi ba”
“Ni dai ba zan iya ba, na kai kukana ga Allah shi zai min magana, ko yanzu ai ba yadda suke so suka samu ba, duk wata sai ya aiko min da abinci da kudi saboda cikin nan, yanzu kuma kina ganin yadda aka cika harabar gidan nan da itace saboda na shiga watan haihuwar, na san idan ra’ayinsu za a bi ba zasu so haka ba, yarana kuma idan ya auna lokaci ya kan aiko da su su gan ni na gansu, an rabu ne kawai amman kamar ana tare, idan Allah yayi zan koma sai ki ga na koma kamar yadda ban saka ran auren Alhaji ba Allah yayi kuma aka yi auren”
“Toh Allah yasa haka shi ya fi alheri, amman dai da kin tafi ba a san inda za a dace ba”
“Allah ya hada mu da dacewar”
“Ameen”
Ta amsa ba dan ta jidadin yadda Iyami ta ki amincewa da zuwan ba.
☆❁ ❁☆
Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy
https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy
1️⃣5️⃣
Salame na turo number Malamin Hajiya Fatee ta kira shi a waya, suka gaisa ta fada masa abubuwan da suka faru ya jajanta mata, ya kara mata da cewar shi ma layinsa aka rufe shiyasa bata ji shi ba. Hajiya Kaltume ya karba suka gaisa sannan ta dora masa da banin abun da ya sami Hajiya Fatee, daga karshe suka yanke ranar da zai shigo garin. Sannan Hajiya Fatee ta iya fita dakinta ta samu ruwan tea ta sha domin bata iya cin komai. Hajiya Katume bata jima a gidan ba Fadeel ya shigo gaishe da mahaifiyar, da zai fita Hajiya Kaltume ta bukaci ya sauke ta gida.
*** *** ***
Ba kadan ran Momy ya ba ce ba, jin cewar Captain ya zo gidan tana bachi, kuma ya fita da bacin rai saboda Hurriya.
“Oh to wai miye na siya mata gilashin ma?”
Namra ta aje spoon din hannunta.
“To nidai ranar da ya zo last na ganta da shi cirko cirko, gilashinta a kasa tana lalabe to shi ne yau take fada min ai marinta yayi saboda sun yi karo”
“Ai gara da mareta ma, yarinyar nan bata da hankali, sannan yanzu ya zo ta ki ta karbi box din wata kila ba zai sake dawowa gidan nan ba kuma, ta ja min ya fara fushi da ni kenan”
“Shi ma fa Captain din nan ya cika zuciya ga zafin hannu, amman dai bata kyauta ba da bata karba ba”
“Bar yar iska bata san su waye iyayensa ba ne shiyasa, shi ma dai miye na kawo mata glass ko makancewa ta yi iya ruwansa”
“Kila ya ga be kyauta ba, ko kuma…”
Momy ta kalleta da duba kyama.
“Ko kuma me? Allah ya kiyaye ai ko mata sun kare duniya Captain ba zai yi komai da wannan yar tatsitsiyar yarinyar na duka ma nawa take shekaranjiya ta yi 16yrs fa, kuma shi da yake da matar da zai aura”