Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Hurriya ta kalli Captain tana murmushi kamin ta maida dubanta gurin kofar da Dr Nyala ta bude. Wani matashin yaro ne ya shigo sanye da lab coat fuskarsa da idonsa sun yi ja sosai kana ganinsa ka san ba karamin kuka ya sha ba, domin har a yanzu ma hawaye zuba suke a idonsa. A take murmushin dake fuskar Hurriya ya gushe ta kalli Captain da sauri ta sake duba yaron dake tsaye gabanta sai jikinta ya fara rawa kamar zata kamkame guri daya ta rufe ido da sauri tana shisshika da karfi….
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…
Captain yayi saurin rike matarsa da sauri yana leka fuskarta.
“Hurriya…”
Ta kama rigarshi da karfi ta rike har lokacin idonta a rufe yake jikinta kuma rawa yake. Ta kasa yarda ba mafarki take ba, kamar yadda take jin kamar tsananin son rayuwa da ďan uwanta yana neman haukata a yanzu da yake mata gizo, to amman kuma kalaman da Captain ya furta fa? Wani hannun ta ji a jikinki wanda ya banbanta da na mijinta, dumin hannun ya fahimtarta da alakar jininta da jinin mai taba ta, shi ma dai sunanta yake kira kamar yadda Mijinta ma yake kiranta, wata kila ta yi dagon zango ne ko kuma kokarin farkawa take da daddadan mafarki. Hakan ya kara mata kuzarin bude idonsa sai ta sake arba da wani mai irin fuskar dan’uwanta mai irin hanci da idonta mai hasken fata kamar nata, sai dai ya girmi Hamad fuskarsa ya sauya sosai. Hannayenta sake rawa ta dago zata murza idonta Captain yayi karaf ya rike
“Karki murza ido”
“Gizo suke min”
Ta amsa a cikin wani sauti mai kokarin gauraya da kukanta.
“Ba gizo ba ne, da gaske ne wannan ma…”
Ta sake bude idon a karo na uku ta kalli matashin yaron dake a yanzu yake dukushe gaban gadon da take zaune yana kuka har lokacin hannunsa ya kan hannunta ya rike ta gam. Ta kalli Captain hawaye na sauko mata.
“To waye wannan?”
Captain be ce komai ba sai da yayi magana da Doctors din suka fada masa dokokin abubuwan da zata kiyaye da kuma abun da da zata ci sannan yayi musu godiya suka fita.
“Hurriya…”
“Na’am”
Ta amsa da sauri domin amsarsa kawai take jira.
“Ba kin ke kika fada mim dan’uwanki yana raye ba? Shim ba ke kika kasa yarda cewar Hamad ya tafi ya barku ba? Kowa ya karbi mutuwar Hamad amman ban da ke haka ne?”
Ta daga kai tana kuka ta kalli Hamad din da shi ma kuka yake sosai.
“Saboda jikinki yana baki dan’uwanki wadda ya fi kowa kusanci da ke yana raye, jikinki be fada miki karya ba tabbas Hamad yana raye, kuma shi ne a gabanki yanzu”
“Taya wannan karyar zata zama gaskiya? Ji yanayin yau nake kamar ba ni ba, tsoro nake kar na farka daga wannan bachi na ga komai ba gaske ba”
Hamad ya kalli Captain cikin wani yanayi marar misaltuwa da wata murya ta samari masu tashen balaga ya ce.
“Me yasa ka yi min karya? Why? Ka ce min kowa ya mutu bana da kowa a yanzu why? Ko kuma kowa ya mutu Hurriya ce kadai a raye?”
Cikin tashin hankali da ba a sakawa rana Hurriya ta dubi dan’uwanta muryarsa ta sauya kamar yadda siffarsa ma ta sauya, ko a can baya daman wasu shi suke dauka yayanta ita kanwa saboda girman jikinsa.
“Dan Allah ya zan yarda Hamad ne…? Ya zan yarda? Ki kira Amma.. Kira min Mama Rukayya… Dan Allah”
Ta rike Captain da karfi kamar zai tsere mata, taya idanuwanta za su bude a yau kuma ta yi arba da wani mai kama da Hamad yace mata Hamad din ne.
“Amma tana raye? Daman Amma tana raye?”
Hurriya ta kalleshi kamar yadda yake kallonta da tsananin mamaki da al’ajabi.
“Magana kake kamar ka san kowa…”
“Na san kowa mana Hurriya, Hamad ne Hamad dinki mai yawan dukanki mai yawam fada dake mai saka ki kuka, Hamad yaron Amma da Appa ni ne Hurriya”
Hurriya ta rike baki tana kallonsa hawaye na sauko mata sharrr. Captain ya zauna kusa da ita ya rumgumeta.
“Abu ne mai wahala dukanku ku yarda da wannan”
Ya dago hannun Hurriya ya nunawa Hamad.
“Awarwaron da ka taba bani as a gift ka ce na bawa budurwata, shi ne nan, Hurriya kin tuna lokacin da na baki kyautar wannan na ce miki wani ne wanda ya dauke ki d
Ƴar’uwanki ya baki?”
Ta daga kai fuskarta na kirjin Captain tana kuka kamar ba gobe.
“Shi ne ya ba ni”
“Me yasa ka bar ni na yi rayuwa a cikin duhu? Why? Me yasa ka ce min kowa ya mutu?”
Hamad ya tambaya da karfi yana wani nishi sai kallon Captain yake cike da bakinciki yana jin kamar ya shake shi.
“Na rayu da wasu mutanen da ba jinina ba, a kasar da ba tawa ba, na rayu akan cewar kowa nawa baya raye, recently nan Salim take yake fada min cewar akwai gaskiyar da kake boye min ashe da gaske kake”
“Shiyasa na saka aka canja maka gida ai, wata kila da ban maka wannan karyar ba da baka samu lafiya ba, da ban maka wannan karyar ba da baka rayu ka kawo yau ba, da ban maka wannan karyar ba da baka natsu ka yi wannan karatun ba, gashi kuma saboda shi ka cika burinka tare da kai aka yi aikin idon da ka taba fada min cewar ka yi yar’uwarka alkawari”
Hurriya ta dago ga kalli Hamad ta mika masa hannayenta so take ya taba ta a karo na biyu ta ji idan da gaske dan’uwanta ne. Hamad ya kama hannun yar’uwarsa da ya fi Marmari fiye da kowa ya rike. Sai ta fashe da sabon kuka.
“Ni dai ina so ko da waninka ne aka kawo min a matsayin kai, zan karba kai ne kadai ka rage min farincikina ya cika, ni kadai ce na yarda baka mutu ba Hamad, amman duk haka ganinsa nake kamar ba gaske ba”
“Tun a ranar da da Captain yace min za’ayi wani aiki da yake son ayi tare da ni amman ba zai kawo aikin ba sai a lokacin da zan fara koyon aikin a wannan asibitin sai na kagara na ga haka, da na zo na ga fuskarki sai na ji kamar wata rayuwa ce ta same ni da ba zahiri ba, kuma ya hana ni magana a ranar har sai yau… Kuka nake Captain ya cutar da ni”
“Ban cutar da kowa ba a nan, ni kawai taimako na yi, kuma ba zan amsawa kowa tambaya ba sai a gaban iyaye”
Captain ya fadawa Hamad a tsawace, kamin ya rika fuskar Hurriya ya share mata hawayenta.
“Ya isa haka, yau aka bude idonki i thought hakan zai saka farinciki ba kuka ba, karki janyo min wata matsala please”
Ya rumgumeta a kirjinsa, ita kuma kamar ya karawa kukanta fetir haka ta ji sai ta kara fashewa da kukan sosai.