Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ni ma ban sa ran zan dawo yanzu ba, tafiya ce ta kama ni gobe da safe zan bar garin nan?”
“Lafiya dai?”
“Yanayin aikin ne, zan yi 1 week a Kaduna”
“Da sauki ai, gida zaka je”
“Da can nafi son Kaduna, yanzu kuma na fi son nan”
Namra ta yi murmushi.
“Gashi kuma ka kusan gama aikinka na nan ai, ka koma KD gaba daya”
“Ina tunanin Daddy zan yi ma magana, a san yadda za’ayi a bar ni garin nan, domin idan na koma Kaduna ba zan samu zuwa nan ba. Ina Hurriya?”
Momy ta sake dubansa bayan kallon da take masa da dan mamaki ta ce.
“Hurriya kuma?”
“Yea na siyawa twins dinta abu ne, kin san yadda nake son yara”
Ya amsa yana murmushi acting like bakin gaskiyarsa yaran ya kawo wa.
“Yaran ma ta tafi ta kai gida ai, ba nan suke zama ba”
“I know tsaraba ce bari na aje a dakinta”
Ya dauki ledar sai Namra ta mike tsaye.
“Let me help you”
“No please ajewa kawai zan yi na fito”
“To ai bata nan kuma yaran sun riga sun tafi”
Cewar Namra tana kallonsa da shakku a idonta. A take ransa ya bace ganin tana kokarin kure shi.
“That’s right idan ta dawo sai ta zuba ashara”
Ya dauke kansa ya nufi stairs rike da ledar, har dakinta ya shiga ya aje mata ledar kan gado ya juyo zai fito sai kuma ya juya yana karewa dakin kallo, karamin gado ne daidai ita sai mirror da closet dinta daga gefe. Ya taka ya isa closet din ya bude yana kallo, can kuma ya rufe ya dawo gurin mirror yana duba kalolin mai da turare dake gurin, ya kai hannunsa ya bude durowar dake jikin mirror a nan kuma yan kunne da sarka ne sai agogo daga kasa kuma hotuna ne. Hotunan ya dauka ya shiga dubawa, wani gurin ita da Hamad ne wani da Amma wani kuma family pictures ne su hudu, wani kuma ita da Appa babu wanda take ita kadai sai wanda take karama, inda take rarrafe wani kuma ta fara tashi dayan lokacin da ta kare primary. Murmushi yayi ya juya ya kalli kofar dakin dake bude sannan ya dawo da idonsa gurin mirror ya sake dauko wasu hotunan dake aje gefe daya, su kan nata ne inda take ita kadai sai kuma wandanda ta yi ranar birthday ta sun yi kyau sosai ko’ina kuma tana sanye da abokin rayuwarta ne wato glasses. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya dora hotunan yana ta dauka hoto sai da ya gama sannan ya maida su a muhallinsu ya dauko awarwaronta ya duba ya dauki zoben dake tare da sarka ya duba sannan ya aje ya rufe mata gurin ya maida wayarsa aljihu ya fice daga dakin ya ja mata kofa. Da sassarfa ya sauko stairs din kana ganinsa ka san a hanzarce yake.
“Momy zan tafi sai mun yi waya, sauri nake akwai mai jirana”
Mamaki ya hana Momy ce masa komai har ya fice. Namra ta daki hannun kujerar.
“Me na gama fada miki yanzu Momy? Kin ga gani ko?”
“Toh ni ma dai abun ya daure min kai, amman kin san Captain yana da son yara fa”
“Maganar ba ta son yara ba ce kawai, ko last time da ya aike ni siyo masa a Mall na je office dinsa na samu glass din Hurriya and he was telling me wai ya bata wani gilashin ne, kin tuna ko ranar da ya saka ta girki, and dazu da safe karki ga yadda ya damu saboda ya same ta tana kuka”
“Kuka me?”
“Na munafurci da neman jan hankali mana, ni ma ban san dalilin kukan ba kuma kin ga ko lokacin da ya tarar ina fada da yarinyar ita ya goyawa baya, saboda ita har marina yayi fa”
Momy ta dan yi dariya kamin ta yi murmushi sai kuma ta sake yin murmushi abun kamar zai kama kanta sai kuma ta ji be kama kanta ba.
“Amman Captain yafi karfin wannan yarinyar ai, beside idan ma zai so wata a gidan nan ai ke ce kuma ina jiyo kamshin hakan”
“Babu macen da tafi karfin namiji Momy, yarinyar ta san yadda take ta sace zuciyar maza, haka ta yi min a Salim har yanzu idan na tuna sai na ji wani iri, and now Captain”
“Idan ma haka ne ke kike yin saka, kuma idan har ta dauki hankalin Salim ba zata sami Captain ba”
“Na yi sake? Momy ni fa mace ce i don’t run after a men, idan su ba su nuna suna ra’ayi ba, ni ba zan iya zubar da ajina na yi kasuwanci kamar yadda take ba”
Namra na rufe baki Hurriya ta turo kofar falon ta shigo cikin yanayi na damuwa sallamarta ma can ciki ta yi, Momy da Namra kuma babu wanda ya amsa mata, ta iso kusa da Momy ta risina.
“Momy sannu da gida”
Ta mike tsaye sai Momy ta bita da kallo kamin ta ce.
“Ke…”
Hurriya ta kalleta tare da amsawa a hankali
“Na’am”
“Tafi ki dauko min ruwa a kitchen”
“Toh”
Ta juya sai Momy ta ce.
“Cire hijab din ki aje a nan”
Ba musu ta cire hijab din ta aje ta nufi hanyar Kitchen, Momy ta bita da kallo da ta fito ma Momy kare mata kallo take tsab sannan ta karbi ruwa.
“Toh tafi dakinki”
Hurriya ta dauki Hijab dinta ta nufi hanyar stairs, sai da ta haye sama gaba daya sannan Momy ta kalli Namra ta ce.
“Na ga dai idan farin nan ne ke ma kina da shi, kuma ko mazaunai kin fita ban san wani abun ja mata hankali a jikinta ba”
“Tana da kyau Momy kuma munafuka ce ta iya kisisina kala kala”
“Ko dai minene ki cire wannan a ranki, ni da Hajiya Turai babu wanda muke so Captain ya aura sai ke, idan ma be aureki ba ai ba zan bari ya auri yarinyar da ba ajinsa ba irin Hurriya”
Namra ta mike tsaye tana rike da wayarta.
“That’s mean idan Hurriya tana gidan nan wani ba zai taba cewa yana so na ba”
“Ki bude idonki Namra yanzu lokaci ya wuce da zaki ce sai anyi yaki a same ki, idan kina son Captain to ki takawa yarinyar nan birki, ko da ma baki son shi ya kamata ki hana alakarsu ko dan abun da ta yi miki amman idan kika kyale kin bata dama kenan, sannan ni da ke mun san Captain ya fi karfin yarinyar nan waya sani ma nan gaba kadan zata iya makancewa gaba daya, kuma yadda uwarta ta zo ta yi mana milki a gida yarta ma tace zata auri Captain ta yi yadda take so, abu ne da ba zan dauka ba, idan Khairy ce ko wata a cikin yayan Kaltume kina ganin zata kyale Hurriya ne?”
Fada sosai Momy take ta wani bangaren tana ganin kamar har fa laifin Namra na saken da take yi har Hurriya take son damar yi mata. Namra ta sauke ajiyar zuciya ya nufi stairs ta sani tana son Captain fiye da yadda ta ji tana son Salim da farko, har tana murna tana ganin kamar sauyi ne Allah yayi mata saboda ta rasa Salim yanzu kuma Hurriya na son sake jefata a cikin wata damuwar, idan har bata auri Captain ba to be kamata ace ya auri kowa daga familynsu ba sai dai daga wajen familynsu balle kuma ace cikin gidansu kuma kanwarta da suka hada jini daya. Ko da soyayya ce kadai be kamata Hurriya ta yi da Captain ba balle aure, sai dai yadda ta san halin Captain wata kila ko da wata alakarce ba zata dade ba saboda yanayin fushinsa da saurin daukar zafi kamar kofin tasa, sai dai duk da haka Momy tana da gaskiya be kamata ta zuba ido Captain yayi soyayya da Hurriya ba ko da be aure ta ba, hakan zai lalata alakarsa da gidan idan suka samu tsabani kuma zai juya mata baya ba zai yi tunanin ya aureta ba. Jingina ta yi da kofar dakinta bayan ta rufe, abu ne mai zafi da ba zata iya rike hawayenta ba, ko da tafiya kuke a hanya wani yace yana son kawarta ba ita ba zata ji babu dadi balle kuma ace cikin gidansu. Bayan kuma duka mazajen nan biyu sun nuna ita suke so amman gashi yanzu Hurriya tana dauke hankalinsu, ta saka hannunta a baki tana ciza kumbarta, gaba daya ta ma rasa me zata yi, ta wank bangaren tana ganin kamar yunkurin yin wani abu zubar da kimarta da martabarta ne ne mace.