Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Yayi kamar be ji ta ba ya cigaba da cin abincinsa.
“Ayi hakuri ranka ya dade a gafarci Kaltume, ban san abun zai zama haka ba, idan aure ne ayi ta yi kai zaka zauna da su ba ni ba, ita m Iyami Allah ya bata lafiya ka dawo da ita ta rike yaranta”
“Ameen”
Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, sai ta ji kamar ta dauki murfin kular da yake cin abinci ta buga masa a kai saboda bakincikin amsawa da yayi da amin. Sai dai tuna abun da ta taka ya saka ta yi murmushi ta kawar da duk wani bacin rai daga zuciyarta… Sai da ya gama cin abinci ya sha ruwa sannan Namra ta kwankwasa kofar karamin falon nasa.
“Waye?”
Hajiya ya tambaya tana harara kofar a zatonta ma yar makiyiyarta ce.
“Shigo”
Appa ya amsa mata da kansa yana gyara, ta turo kofar falon ta shigo, ganin Hajiya Kaltume ya saka ta ji babu dadi domin tana son magana da Appanta private ne. Ta zauna kusa Hajiya Kaltume dake kallonta tana raya abubuwan da za su faru nan da yan kwanaki kadan idan ta mallake mijinta.
“Appa barka da dare”
“Barka dai Namra, ya kike?”
“Lafiya Kalau Appa”
Sai ta yi shiru.
“Akwai wata matsala ne?”
Ta dan kalli Hajiya Kaltume ta kalli Appa.
“Daman ina son magana da kai ne, amman zan bari sai da safe sai mu yi maganar kamin ka fita”
“Privacy kike so?”
Ta daga kai. Appa ya kalli Hajiya Kaltume kai tsaye yace.
“Kaltume mu shiga bedroom mu bar miki nan ko kuma ke zaki shiga”
Hajiya Kaltume ta dubi Appa da mamaki sai dai bata ce komai ba ta yi murmushi.
“Aa bari ni na shiga, Namra a kebe lafiya”
Ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi bedroom din Appa ta shiga ta rufe dakin, a nan ta samu damar yin kwafa ta cize baki.
“Nan da dan lokaci komai zai canja, ke ma idan baki yi hankali ba sai kin fi Hurriya shiga matsala ke da uwarki duk sai kun zama abun tausayi”
Ta zauna kan sofa tana matsa kafarta dake dake gwada son yi mata ciwo kamar jiya.
“Wai ni Alhaji zai cewa na ba shi guri zai yi magana da Namra, da dane ko fadar haka da ta yi ai sai yayi mata fada, amman ba komai duk a tafin hannuna zaku dawo sai na juya ku kamar waina”
Sai da Appa ya gama maganar da zai yi da yarsa sannan ya shigo dakin cikin wani yanayi na rashin yabo da fallasa ya zauna bakin gadonsa yana kasa wayar hannunsa, kamin ya dago ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.
“Tun shekaranjiya nake wani tunani”
“Kamar na me Alhaji?”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Ina tunanin yaran nan ne da Iyami ta haifa, twins Hamid da little Hamad, tun da aka haifi yaran nan ban taba zuwa dubasu ba a matsayina an ubansu”
Hajiya Kaltume ta ji gabanta ya fadi irin faduwar da be taba yi ba, yau Appa ya fadi abun da bata kawo ran faruwar sa a nan kusa ba, lallai a yanzu ta yarda Malamin da yayi mata aikin ya fara karya shi saboda yana son ta ba shi kudi mai yawa ya mallaketa kamar yadda ya mallake Hajiya Fateee da bata ma son a fadi laifinsa. Babu wani abin da zata yi a yanzu da ya wuce ta boye komaia kasan zuciyarta, dan haka ta yi karfin halin murmushin da za a iya cewa ya zame mata na dole ne kawai ta ce.
“Toh Alhaji ai za a iya zuwa ka dubasu ai yaranka ne, ni zan iya raka ma sai mu tafi tare, ba wani abu ba ne”
Wannan karon ajiyar zuciyar da Appa ya sauke mai nauyi ce sosai.
“Ina jin nauyin hakan, saboda na juyawa yaran nan baya na ci amanarsu ba tare da sun min komai ba, ina tunanin zan dauko su amman me zan ce idan zan aika a dauko su? Kai….”
Ya busar da iskar data cika masa baki sannan ya tattare girarsa guri daya yana jin rashin dadin a abun da yayi ma yaran nasa da suka kasance jininsa.
“To ai ba abin kunya ba ne Alhaji, yaranka ne kuma idan acan baya ka yi kurkure yanzu ai gyara kake kokarin yi, karka dauki wannan a matsayin matsala dan Allah shirya ka je ka duba su ko kuma a dauko maka su”
“Ban gama yanke shawara ba tukuna, zan yi tunanin abun da ya kamata na yi”
Ya amsa mata sannan ya aje wayar ya hau saman gadon, ita kuma ta juyar da fuskarsa a dayan gefen tana kashe ido wani bakin kishi na cizon zuciyarta, sai a yanzu take jin ta yi daidai ta ya yarda a ayi ma Iyami halbin kasko domin bata san da wane irin zata sake dawowa gidan ta ba idan Appa ya maida ita gidan.
Kamin safiya ta waye Hajiya Kaltume ta matso saboda bokanta ya fada mata cewar idan yayi aikin da dare ya halba mata kamin safe bukata ta biya kuma ita ta yarda da hakan, sai da ta baro bangaren Appa ta dawo bangarenta take cin ciwon rashin karbo number wayar dan masani da bata yi ba, da yanzu sai ta tambaye shi ya samu yin aikin ko be samu ba. Kitchen din ta ta shiga ita da Ruma suna shrya abun karyawa, Khairy da Salma kam ana can wata duniya ana sharar bachi musamman ma Khairy da bata kwantawa sai ta sha abun da zai jefata a bachi mai nisa. Ita ma Ruma bata saba tashi da wuri ba saboda uwarsu bata koya musu tashin da wuri, sai dai yau ta tashi saboda tana da lecture 8 na safe. Suna shirya abun karyawar Hajiya Kaltume na tunanin kalaman da Dan masani yayi mata, kuma yanzu ta fara tabbatar da haka, domin a yanzu ta lura idan ta yarda ta fadi wata maganar akan Iyami Appa zai iya bata nata rai, balle kuma ace ya dawo, wata kila milkin da zata yi a yanzu zai fi an can baya, gashi yanzu ta haifi yara biyu maza ita kuma tana da daya ga son da yake yi ma Hurriya zai dawo, su ma kananan yaran zai fara nuna musu gata, sannan kanwarta ta aure danta dadi kan dadi, ga kuma wani auren da zai kara, above all ita ya saketa.
“Kam uban can kai….Gwuttt”
Ta yi kwafa har sai da Ruma ta kalleta.
“Hajiya lafiya?”
“Lafiya kalau je ki taso yan’uwanki su tashi haka mana, wata kila ma ko sallah ba su yi ba”
Ta juya ta fice daga kitchen din. Hajiya Kaltume ta bita da kallo tana tunanin zuci.
“Hmmm wato ya sake ni ko? Ai kara ma a kasheta idan aka kasheta iyayenta ma za su yi hankali tun da na gane kwadayi yayi musu yawa har suna son daukar wata yar au aurawa Yasir, zan koya musu hankali”
Tana maganar tana wani huci kamar macijiya, sanin mijinta baya karyawa da wuri a weekend days kuma today Saturday ya saka ta shiga dakinta dan ta kishingida, sai dai me tunanin yadda abubuwan suka soma sauyawa mata a lokaci daya ya saka ta kasa bachin na safe, ta dayan bangaren kuma idan ta tuna matakin data fara dauka sai ta ji ranta yayi fari. Kadan kadan bachi ya fara fisgarta saboda bata samun yin na dare ba yadda ta saba saboda tunani ganin take komai kamar mafarki ne.
“Hajiya ni kam na wuce”
Ta zabura ta bude idon da sauri sakamakon maganar da Ruma ta yi mata, tana cikin shirinta na na fita ta goya teddy bag dinta a baya.
“Kin yi breakfast?”
“Eh na yi”
“Khairy sun tashi?”
“Na tasheta daker ta tashi ita Kuma Salma na ta tashinta ta ki tashi”
“Toh Allah ya kiyaye”
“Amin”
Taja mata kofar dakin, kamin ta rufe Yasir ya turo kofar dakin ya shigo.
“Hajiya Ina kwana?”
“Idan ban kwana ba zaka gan ki, Alhaji Yasir mijin Rukayya”
Kalaminta be masa dadi ba ko kadan, fushin da ta yi da yi da shi da safe ma be jidadin haka ba balle kuma yanzu da abun ya biyo har da bakar magana.
“Ayi hakuri Hajiya”
“Hakuri daya ne, ka hakura da abun da uwarka bata so, shi ne mafita agareka, idan ba haka ba zaka janyowa kanka abun da ba zaka iya dauka ba”
“Toh Hajiya”
Ya mike tsaye ya fice daga dakin. Hajiya Kaltume ta taja uban tsaki.