Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ai na sani, uwar Manal da Haidar sarakuwar AA Turaki in-law din Hajiya Turai, yar gatan Jamal farincikin Amma, sanyin idon Appa, aminiyar Hamad”
Ya sumbanci bakinta yana shafa jikinsa kusan a kullum kamar amarya take a gurinsa, saboda sonta da yake mata ya fi wanda take masa, ita kuma tana kokarin ganin ta kyautata masa ta rike kambunta a gurin mijinta.
“Dadadadadada..”
Yana jin muryar Manal yayi hanzarin dauke bakinsa a na ta ya kauce daga shu’umin rikon da yayi mata ya kalli kofar dakin da aka turo. Yarinya ce yar shekara biyar rike da pen da ipad ya raba gashin kanta gida biyu an mata two babys da pink ribbons. Kusan fuskarta gaba daya fuskar Captain ce kadan ta debo daga Hurriya. Captain ya rage tsayu ya duka daidai yarsa yana gyara mata gashin kanta.
“Ammyna ina ta tambayarki…”
“Ina daki ina drawing, Dada na zana ka look”
Ta nuna mishi zanen dake ipad dinta sai ya karba yana yabawa.
“Wow Ammyna kin yi kokarin excellent”
Manal ta yi dariya ta yi tsalle tana jindadi. Captain ya sumbance ta sannan ya daga ta sama ya dauke ta ya fice daga dakin.
*** *** ****
An yi bikin auren Musib da Ruma da aka hade lokaci daya, cikin jindadi da barin naira, domin Musib shi ne dan Momy na karshe da zata aurar a yanzu, bayan Miwan da ya auri wata Abokiyar karatunsa da kuma yar gudaliyarta Namra wadda ta auri Dr Sadiq abokin Yayanta Miwan, hakan ya saka Momy ta fitar da kudi ta yi hidima sosai kamar yadda ta yi a sauran bikin yayanta ko ma fi.
Amma ta zage dantse wajen ganin ta zamewa Ruma uwa duk kuwa da irin abubuwan da Hajiya Kaltume ta yi mata a lokacin da take gidan, Amma bata duba wannan ba daman hali ba daya ba, dan haka ta rike Ruma kamar yarta, duk wata siyayya da za’ayi ta auren Amma ce ta yi domin Momy tana can tana fama da nata hidiman na auren danta.
Duk wata hidima da ya dace uwa ta yi Amma ce take yi, domin bayan komawar Ruma da Khairy a gurin yan’uwan mahaifiyarsu sai zaman yake yi musu dadi, bakinciki sai ya taru yayi musu yawa, suna kallon mahaifiyarsu da bata iya komai sai tona asirin kanta har ta kai ana rufe ta a daki sai idan za a bata abinci ko abin sha ko gyara mata jikinta sannan za a bude ta, ko kuma idan wani ya kawo mata ziyara. Gashi kuma ba sa jindadin zaman gidan, Ruma da kanta ta zabi dawowa gidan mahaifinta a karkashin kulawar Amma ta san ko ba komai zata fi rika ta da daraja fiye da Momy da har yanzu take nuna musu banbanci. A lokacin da ta dawo sai Amma ta saka hannu biyu ta karbe ta kamar komai be faru ba, har zuwa lokacin da ta kammala karatunta ta samu Miji Amma ta yi mata komai da ya kamata tare da taimakon Sapna da Amma take janyowa a duka al’amurran gidan kasancewarta babbar yar Appa gashi kuma yanzu ta dawo kusa da su da zama saboda Appa ya siya mata gida a cikin garin Gusau.
An yi biki cikin farinciki da jindadin yan’uwa da yawa sun samu halarta ciki har da matar Fadeel da zumunci ya daure tsakanin Yasir da Fadeel din kamar wasu yan’uwansu, matansu ma suka kulla, waton matar Yasir Rukayya da ta zame ma Ruma, kamar babban yaya gurin shawarwari da wasu abubuwan na rayuwa. Yasir ya tsaya kamar Appa idan ana bukatar wani abun shi ake yi ma magana ba Appa ba domin ya dauko girman ya rayata a wuyansa tun kamin yayi aure ma balle kuma yanzu da yake da yara biyu da matarsa. Kusan kowa tambaya Khairy yake yaushe zata yi aure ganin ita ce Babba amman shiru har yanzu ko mashinshi babu, Yayarta Maama ce take dan tare mata wani lokacin tana cewa ai aure lokaci ne ita ma zata yi idan lokaci yayi, gashi kanenta Hurriya da Ruma sun yi sun barta, abun ya taba ta sosai domin tambayar mace yaushe zata yi aure ba abu ne mai dadi ba balle kuma ita da kaddara da fadawa. Har aka ci aka shude bakin Namra be hadu da na Hurriya ba, har yanzu da kowace ta yi aure take da Yaya Namra bata shiga safgar Hurriya ta riga ta tattara lamarinta ta aje gefe daya.
Ko a lokacin bikin aurenta ma haka ta yi mata kamar ba yar’uwarta ba, zata yi magana ko mu’amala da kowa ban da Hurriya da zarar sun gaisa bata sake tambayarta komai. Tun abun yana damun Hurriya har ya daina domin ta san babu ta inda take da laifi, abu ne da Allah ya riga sa ya tsara shi babu yadda za a canja.
Amaryar Musib ta tare a garin da mijinta yake wato a Zamfara, Ruma kuma ta tare a gidan nata mijin dake Kano. Duk da rashin lokaci da takurarwa aiki da Captain yake samu haka ya cije ya zo daurin auren na dan’uwansa da kuma yar’uwar matarsa. Sai da Hurriya ta yi da gaske sannan ya barta ta fi kai Amarya Kano, daga can yayi mata booking flight zuwa garin da yake aiki a yanzu. Sai bayan biki da kwana biyu sannan Hamad ya shirya ya kai musu Manal da aka bari a gurin Amma, yayi kwana biyu a garin sannan ya dawo gida.
*** *** ***
Manal na ganin Daddynta a kwance ta zo da gudu ta fada a faffadan kirjinsa ta kwanta.
“Dada baka da lafiya”
Ya daga idonsa kadan ya kalleta.
“Yes Manal”
Hurriya ta kai hannu ta taba wuyansa.
“Jikinka yayi zafi, bari na kawo maka magani”
Ta mike tsaye ta fara tafiya kenan ta ji yayi mata wata magana da ta saka ta juyowa da sauri tana tofar da yawu.
“Wata kila dai ba a banza nake fever nan ba, duk a karkare daga karshe ba zai wuce ace akwai ajiya a cikinki ba”
“Allah ya kiyaye, yaushe aka haifi Haidar din ma to, yaron da yanzu yake koyon zama”
“It doesn’t matter, ni dai na san irin wannan fever dake sani kyamar abinci da zafin jiki sosai bana yinta sai da dalili”
“Wallahi aa Allah ya tsare Malaria ce kawai, ko kuma gajiyar aiki”
“Zamu gani ai sai a gane mai gaskiya, ni na san yanayin da nake ji ba irin na rashin lafiyar mutane ne ba ne”
Ta daga kafadunsa tana murde baki.
“To wata kila aljannu suka shafe ka”
Ya kyalkyale da dariya sosai kamar ba shi ba ya daga Manal daga jikinsa ya zauna ya zaunar da ita. Hurriya kuma ta shiga ciki ta dauko masa magani da ruwa ta balla ta ba shi ya sha.
“Thank You Allah ya miki albarka”
“Ameen Allah ya baka lafiya”
“Dada Allah ya baka lafiya”
Manal ma ta fada sai ya amsa da Ameen yana murmushi.
“My Ammy rabin raina”
Hurriya ta tabe baki.
“Hamad na yi aure zan bada ita”
Manal ta lake kafada kamar ta san abun da ake fada, Captain kuma yayi dariya mai sauti.
“Da kin jawa janki wahala ko ya dauki yarana ai sai ya dawo da su zai samu salama, ko da Nigeria ne kuwa balle wata kasar”
“Ni ma dai bana son zaman shi a can”
“To ya za’ayi tun da ya zabi cigaba da masters dinsa a can”
“Wallahi duk saboda yarinyar nan ne, ni bana son ma ya aureta saboda Salim”
“Ina ruwan Salim da soyayyarsu? Ita dai tace Hamad take so, shi ma kuma yana sonta sai kawai a musu fatan alheri”
“Ai Amma ba zata bari ayi auren yanzu ba sai ya gama masters dinsa”
“Kamin lokacin ita ma ta gama makaranta ai, sai ayi daidai a dauko muku yar Ethiopian amman al’adunsu daban da na mu”
“Wai Salim yana duniyar nan ma?”
“Yana nan mana, kin san an watsar da lamurransa shiyasa ba ni da labarinsa yanzu, yayi ta kamun kafa a kamin yayi aure yana son dawowa gurin Namra ya nuna masa ba ma bawa marar tunani da mutumci auren zuri’armu, yaje can ya samu daidai shi”
“Amman baka kyauta ba, ka sani ko tana sonshi har lokacin?”
“Ko tana son shi be cancanci aurenta ba, kuma ita ma bana jin zata iya aurensa gaskiya, ke ce dai take ta kishi har yanzu ta bari shedan ya shiga gabanta”