Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Ta girgiza ma Hajiya Kaltume kai tana fashewa da kuka.
“Aa Hajiya dan Allah, bana son kowa ya ji, kuma abun be kai ace za a saka iyayensa ba, duk abun da ya faru laifina na na fada muku”
“Toh Allah ya kyauta gaba, tashi ku tafi”
Khairi ta bita da kallo baki sake tana ayyana idan ita ce ba zata iya daukar wannan iskancin ba. A mota babu kalar nasiha da jan kunnen da Yasir be mata ba, bayan ya yaba mata na boye sirrinta da ta yi.
“Sai dai ba komai yake bukatar boya ba, wani abun idan yayi yawa yana da kyau iyaye su ji saboda a dauki mataki”
“Na gode Yaya kuma In sha Allah zan dauki shawarka”
“Allah ya sauwake kuma ya kawo kwanciyar hankali a tsakaninku”
“Ameen”
Ta bude motar ta fita kamar ba ita ba, aure mai saka ladabo in ji hausawa. Tsayawa ta yi a gurin har sai da yayi reverse mai gadi ya bude masa gate ya fice sannan ta juyo ta shigo ciki.
HURRIYA POV.
Hurriya ta shiga dakinta ta aje mata siyayyar da suka yi sannan fito ta shige dakinta. Namra kam ta dade a motar tana sannan ta fito ta rufe ta shiga cikin gidan. Ko’ina na falon kamshi yake alamar an sauke abincin dare tun kamin magariba, tun kamin ta haura sama ta cire mayafinta ta shiga dakinta, saman gadonta ta aje mayafin kuma a saman dai ta zauna tana duba kayan shower gel ne da perfume. Bandaki ta nufa ta fara jera gel din sannan ta fito ta jera turaren ta dauki daya ta nufi dakin Hurriya, ko da ta shiga Hurriya na tsaye jikin windows rumgume da hannayenta tana kallon waje.
“Hurriya”
Ta juyo ta kalleta
“Ga turare daya ki yi amfani da shi, kuma ki tura min account din sai na saka miki kudin, amman dan Allah me zaki yi da su?”
“Wani abu ne na sirrina Yaya Namra karki takura please”
“Shikenan i trust you na san ba zaki yi wani abu marar kyau da har za ace waya baki kudin ba? You’re not a bad girl”
Namra na magana tana kai hannu ta ja naman fuskarta cikin salon wasa. Hurriya ta yi murmushi ta sauke kanta kasa. Namra ta aje mata turaren saman gado ta fice zuwa dakin Momy. Ta tura kofar dakin tana sosa kanta.
“Momy wai ni kam Sarauta nan suna da Family da yawa ne?”
Momy dake kokarin cire sarkar zinarin dake wuyanta ta kalleta.
“Sarauta sunan kakansu sai ya zama yaya da jikoki suna amfani da shi, me ya faru”
“Ba komai kawai ina mamaki ne, wani muka ji ana fadarsa wai Sarauta”
“Sunan da suke bearing ne, kuma ba laifi suna da kudi kamar dai mu, yanzu kuka dawo?”
“Eh na ji gidan sai kamshi yake an sauke girki”
Momy ta yi murmushi ta mike tsaye, ta nufi bathroom Namra kuma ta kwanta a gurin ta dauki wayar Momy tana tabawa.
After fitar Namra Hurriya ta nufi gurin da turaren yake ta kai hannu ta dauka ta bude kamin ta shinshina kamshinsa Khairi ta turo kofar dakin ta shigo a kufule, waya a hannunta ba tare da ta ce komai ba ta mikawa Hurriya wayar. Sai da Hurriya ta fara kallon wayar sannan ta kalleta. Khairi ta daka mata tsawa.
“Ki karba mana”
Ta karba da sauri ta kai kunnenta ba tare da sanin waye ba.
“Hurriya i wanted to talk to you so badly duk wani abun da kika ji akaina karya ne, kawai Khairi tana fadar son ranta ne”
Hurriya kallon Khairi kawai take wayar a kunnenta ta kasa cewa komai.
“Hello… Are you there”
Ta sauke wayar ta mikawa Khairi ba tare da tace komai ba, Khairi ta karbi wayar ta kai kunnenta.
“Bata son magana da kai ya kamata ka gane mana”
“Yeah that’s because you told I’m a bad person, dazun nan babu kalar maganar da bata fada min ba a gaban mutane kuma duk laifinki ne”
“Ta ina abun kuma ya zama laifina Adam? Ni ban fadi wata magana marar kyau akanka ba, idan ma zan bata ka ko na zage ka ai kamar na yi ma kaina ne”
Cikin fushi ya tsinke kiran ba tare da ya sake cewa komai ba, ita kuma ta kalli Hurriya daman kowa da wanda ya raina.
“Cikin mutane kika ci masa mutumci? Kuma kika ce masa na ce yana shaye shaye?”
“Ni ban ce kin ce ba”
“Amman dai kin masa cin mutunci a gaban mutane ko?”
Ta yi shiru, a take Khairi ta kai mata duka a baki daman tana da haushinta, tana ganin saboda ita Yayanta yaya mata duka ya ci mutuncinta a gaban friends dinta, yanzu kuma saboda ita Adam ya kira yana fada mata magana son ransa.
“Haba Yaya Khairi”
“Au haba ne? Ni banza kika saka aka yi min duka? Munafuka yar kasan wuta, haka kawai kika ja min cin mutunci da duka a gaban jama’a”
Ta kai mata duka a fuska, Hurriya ta matsa baya ganin tana son yi mata illa.
“Wallahi tallahi sai na miki fiye da abun da kika min Hurriya, sai na dandana miki bakinciki”
Hurriya dai bata ce mata komai ba sai kallonta take, Khairi ta yi kwafa ta juya ta fita daga dakin, sai kuma ta dawo da sauri ta nuna da yatsa.
“Sauran kuma ki fadawa Yaya Adam ya kira na kawo miki waya, ki ga yadda zan taka wuyanki wannan kassan na jikinki duk sai na karya su”
Ta yi kwafa a karo na biyu sannan ta fice, Hurriya ta zauna bakin gadonta tana taba bakinta dake mata zugi…
“Allah ya saka min in one way or the other”
Ta fada idonta na cika da hawaye, sai da ta gama taba bakin sannan ta tashi ta dauko pen ta dubuta account dinta ta fice daga dakin, kofar dakin Namra ta fara turawa ganin bata ciki ya saka ta aje mata takardar a kan gadonta juyo ta fito. Dakinta ta sake komawa ta dauki littafin da Gwaggo ta bata na addu’o’in ta sauko, Garden ta nufa sai da ta zauna sannan ta bude ta fara karanta addu’o’in yamma.
HAJIYA KALTUME.
A waya ta labartawa Malaminta abun da ya faru, tana hada masa da magiya tare da alkawarin yi masa duk abun da yake so matukar ya taimaka mata Maama ta samu kan mijinta.
“Haba Malam kai da ka ra kwafar min da Alhaji, kuma ga Iyami ma sai labari za ace wannan ya gagareka”
“Ba gagarata yayi ba Hajiya, wato yaron nan iyayensa suna tsaye akansa, duk lokacin da zamu yi aiki ba ma samunsa ko da ma ya kama zaki ga abin ya bi ruwa, amman duk da haka zamu kokarta zam sake yi masa aiki mai karfi”
“Dan Allah a taimaka Wallahi yanzu ba ni da tashin hankali sai na yarinyar nan, kasan yadda uwa take jin idan ta aurar yarta a gidan tashin hankali, burina ace tana zaune da mijinta lafiya kamar yadda nake da nawa”
“Karki damu zamu yi haka, yau da daren nan akwai wuridin da zan yi mata, komai zai wuce”
“Toh shikenan zan sako mata na goro yanzu a account in Shaa Allah”
“Hajiya kenan toh sai na ga sakonki”
Daga haka suka yi sallama, bata aje wayar ba ta kira aminiyarta, sai da ta fara shimfida mata halin da suka sami Maama sannan na Malam ya biyo baya.
“Oh wannan yaro dai ya zama butulu, an yi aure lafiya lafiya ashe mugu ne”
“Ai ni da na san haka yake Wallahi ba zan yarda ta aure shi, daman can ni be wani kwanta min ba”
“To yaran zamani ne ko kin hana ta ai ba zata hanu ba saboda tana son shi, kuma wani ba za a gane halinsa ba sai an yi auren ba”
“Amman dai Malam yace min zai yi aiki yanzu”
“Ai haka yafi, ni wasu mamaki suke ba ni fa ki duba ko yarinyar nan Afrah yadda aiki be kamata, da yana kamata da yanzu ta bar gidan nan amman sai kashe kudi nake a banza ko gezau”
“Shi ma yace iyayensa suna tsaye a kansa, amman duk da haka na san ba zai gagara ba, karki so ganin yadda Maama ta lalace kamar marar lafiya saboda babu kwanciyar hankali a gidan miji”
“Ai kam dole a tashi mata tsaye, ni ma na kiransa domin ina jin alamar motsi a cikina”