Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Hamad……!”
Hajiya Kaltume ta fada da karfi kamar zata rusa dakin.
“Karya ne ba dai Hamad ba, Hamad din da ya mutu? Hamad din da aka kashe? Yaushe zai rayu? Wane irin Hamad kuma? Wannan karya ne, an riga da an kashe Hamad ba zai dawo ba, wannan wai duk na minene Yasir? Duk na ganin bayana ne? Duk na son a ga karshena ne? An hana ni zaman lafiya da mijina, an fitine ni har sai da Alhaji ya sake ni, yanzu kuma zai maida Iyami, idon Hurriya ya bude, ta yi aure ta auri babban mutum, sannan n fasa auren tawa yar, mahaifinku ya juya min baya, na gagara neman lafiyata na gagara zaman dakina kullum bana gurin wannan boka bana gurin wannan malamin, amman har yanzu shiru, yanzu fa na dawo daga wani gurin, sai kuma ka zo min da labarin wai Hamad yana raye? Yaron sa aka kashe tuntuni? Yaushe zai rayu? Hamad ya mutu wani ne dai ya dawo yana son a kai ni gidan yari, burin Iyami ya cika… Shikenan tawa ta kare”
Cikin rashin fahimta da mamaki Yasir yake kallon mahaifiyarsa, be da dalilin daga hankalinta saboda Hamad ya dawo ba har da zancen gidan yare, above all ta gama fada masa tana bin malamai da bokaye.
“Ta ina dawowar Hamad zata saka a kaiki gidan yari idan ma gaskiya ne?”
Tana tambayarta ne a daidai lokacin da Ruma da Khairy suka sauko domin har dakunansu suna jin muryar Hajiya Kaltume saboda yadda take daga murya.
“Saboda ni na saka aka sace Hamad… Ni na saka aka dauke shi tare da Umm Ruman, Hurriya na ce su dauka sai aka yi kuskure aka dauki Hamad… Amman ban ce su kashe shi ba, Danja ne ya aikata hakan ba da umarnina ba..?”
“Waye kuma Danja?”
“Wanda na saka ya sace Hamad, a gidan Hajiya Fatee na hadu da shi.. Ni na saka shi aikin saboda ina son a karbe kudin Iyami ne da Alhaji ya bata lokacin da ya sake ta ya damka mata kudi da gida ga sarkar zinari ya siyawa Hurriya wannan ya saka na aikata… Iyami ta hana ni jindadi ta hana ni zaman lafiya ta saka na rasa komai daga zuwa aiki ta aure min miji sanadinta na rasa Salma ni na kashe yata da kaina… Iyami na ce a halbe sai aka halbe Salma ta cikin madunin Tsafi nan ma ni na saka mai aikin Nafisa ta kai ni duk saboda Iyami ne… Shikenan na lalace rayuwa ta ta kare…”
Kama ganin yadda take maganar yana murza jikinta zaka san bata a cikin hayyacinta. Khairy da Yasir ne mamaki ya cika su, Ruma kam kuka ta fashe da shi domin ta san asalin gaskiyar.
“Hajiya… Wannan maganar ba a cikin hayyacinki kike yinsu ba…”
Yasir ya fada tana tasowa daga inda yake zaune ya dafa mahaifiyarsa ta kai kasa tana kokarin cire riga.
“Ni na saka aka dauke shi Wallahi… Ni na ce a sace Hurriya su kuma suka dauke shi ina ta murna asirina yana rufe sai kuma ka ce min wai Hamad ya dawo? Gidan yari zan tafi kenan? Gidan yari zani Yasir?”
Ya rike rigarta yana kuka, ya dago ya kalli kenansa.
“Akwai wanda ya san wani abu a cikinku…”
Cikin kuka Ruma ta ce.
“Eh gaskiya ta fada, ita ta saka aka sace Hamad, kuma Hamad da ni duk mun ji muryarta lokacin da take magana da su, Har yake cewa Hajiya me na yi kika ce a kawo mu nan? Idan na dawo sai na fadawa Appa, sai ta fara fada tana cewa ya ji muryarta zai tona mata asiri, bayan ta kashe wayar ne suka buga mishi karfe akai kan ya fashe yana ta jini, Hamad yana ta ihu yana kiran sunan mutane har da ni, suka fitar da shi daga dakin suka bar ni daga nan ban san me ya faru ba…”
“Innalillahi Wa’inna’ilaihirraji’u ײ”
Yasir ya furta har sau biyu sannan ya mike tsaye ya rike bakinsa. Khairy kuma ta fadi zaune tana kuka domin bata taba jin wannan ba sai yau. Hajiya Kaltume kuma bata fasa tonawa kanta asirin abun da ta yi ba, tana ta firgar rigar jikinta da zanenta.
“Hajiya me yasa baki ki tunanin makomarki ba da ta mu kamin ki aikata? Wane irin abun kunya ne wannan? Har yaushe zuciya zata bushe ki aikata hakan ga dan mijinki dan be miki komao ba, be tare miki komai ba? Idan ma kishi kike da mahaifiyarsa shi meye nasa a ciki? Gashi har kina fadar sanadinki Salma ta mutu…”
Hajiya Kaltume ta kyalkyale da dariya ta buga kafa. Ta janyo jakarta ta ciro maganin da ta dawo da shi ta zube a gurin.
“Ai ba Shikenan ba, ni na saka Khairy ta dauke gilasan da suke dakinka na Hurriya, ni na yi ma Hurriya da Appanta farraqu, aka saka masa tsanar Hurriya, ni na saka aka saki Iyami Yasir ni na yi mata wannan asirin kuma na ce a kwantar da ita ciwo, kuma na ce ayi mata asiri kar wani ya ganta ya aureta, yanzu wannan maganin shi kuma bokan ya fada min idan na yi amfani da shi Alhaji zai zo Jiki na rawa ya maida aurensa, kuma Fadeel zai dawo ya auri Khairy… Kawata Hajiya Fatee ita take kai ni ko’ina ita ma kuma tana can da ciki cikin haihuwa wanda ta saka malam ya danne, na biyawa Malam makka saboda na jidadin aiki, na mallaka Alhaji sai abun da nace yake min… Tabbas na aikata Hamad kuma ni na dauke shi ni ce nan na aikata, kuma na yi shiga gaban Alhaji da Sapna na kawar masa da ita a zuciya ya fita maganarta na shashantar da ita a zuciyarsa…”
Kusan duk wani abu da Hajiya Kaltume ta aikata tun cancan da har zuwa yau sai da ta fadawa yaransa da wanda suka sani da wanda ba su sani ba. Yasir sai ambaton Allah yake be taba tunanin mahaifiyarsa ta yi nisa haka ba sai yau be taba tunanin ita ce sanadin barin Amma a gidan ba sai yau, be san ita ta shiga tsakanin Hurriya da Appa ba sai yau, be san ita ta aikatawa Hamad haka ba sai yau. Ya rasa ta ina zai fara ya rasa ina zai saka kansa ya samu sassaucin rayuwa.
“Ku shiga da ita cikin daki ku rufe karku bari ta fito”
Ya fada sannan ya share hawayensa yana jin kamar ace ya mutu kamin yau. Ruma ta kalleshi tana kuka.
“Yaya yanzu idan da gaske Hamad ya dawo gidan yari za a kai Hajiya Kenan?”
Ya cije baki ya saka cewa komai sai hawaye ke sauko masa. Tashi yayi ya fice daga falon ya nufo bangaren mahaifinsa ya zauna a gurin yana jin wani bala’in gabas da na yamma yana hade masa, da ma ace wata ce daga cikin kannensa zai ji sauki amman uwarsa? Abun yayi masa muni gaba daya ma sai ya rasa abun da zai yi, tun farko be ga dalilin Hajiya na aikata hakan ba, domin bata rasa komai a gidan Appansa ba idan ma ta tasa me yasa ba zata barwa Allah ba. Yanzu wa gari ya waya? Karshenta jifan akan wa ya dawo? Waye yayi mummunan karshe? A yanzu ya kara jin kaunar Amma a ransa domin ita da ta wakkala ga Allah gashi yayi mata mafita kuma yana kan mata, Hurriya ma haka, Amman Khairy gashi ta girbi abun da ta shuka tun abun be yi nisa ba, Hajiyarsa ga abun na kokarin taba hankalinta ko ma ya taba.
Allah kawai yake ambato ya rasa me zai yi, wa zai tunkara da maganar ya rasa ina zai bullowa lamarin. Yana zaune a gurin har la’asar, sallamar ma yana yi ya sake dawowa gurin ya zauna tunani yake amman tunanin ya ki tsaya masa ya tasa wanda zai ba shi shawarar abun da ya dace ya aikata. Asibiti zai dauki Hajiya ya kaita? Ko kuma dai ya sanar da Iyayenta da kanenta domin babu iyaye a yanzu, ko kuma dai ya samu mahaifinsa da maganar. Daga balcony din da yake zaune ta bangaren Appa ya hango shigowar motar Maama, hakan ya saka shi tashi ya nufi bangaren mahaifiyarsa, a dakin ya sameta tare da sauran yan’uwanta Khairy da Ruma suna kuka har lokacin Hajiya Kaltume bata daina tonawa kanta asiri ba.