Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
A firgice ta bude ido ta kalli wayar da ke ringing, zuciyarta ta shiga shawarar ta daga kiran na Salim ko kuma ta kyale shi. Bata gama yanke hukunci ba ta samu kanta da amasa kiran.
“Hello”
“Namra… Ai da kin fada min dan’uwanki Captain zaku bawa auren Hurriya da ban wahalar da kaina ina neman ta so ni ba”
Namra ta yi shiru hawaye na sauko mata.
“Na ji an daura aure a yau, ina taya ku murna, amman ki sani amana ba zata bar dan’uwanki ba, ya ci amanata ya aikata abun kunya, ya aure budurwar abokinsa abokin ma na kusa da shi, yanzu na gane dalilin da ya sa baya son ma na yi masa zancen Hurriya ashe kansa yake yi ma campaign, kuma bukata ta biya tun da yayi nasara sai dai ina son ku sani KARMA is real kuma kowa ya aikata mai kyau zai sani”
“Salim bana da masaniya akan komai, laifin ba na Captain ba ne na Hurriya ne, daga mahaifiyarsa har mu ba musa san da zancen daura auren a yau ba, sai sanar mana aka yi, wata kila ta yi magana da shi ne ta roki yayi mata haka, amman Captain ba zai yarda a aikata hakan da son ransa ba, waye zai so ya auri Hurriya bayan duk abun da ya faru a yanzu, kuma idonta ya rufe bata ganin komai a yanzu…”
“To me yasa ya aureta?”
“Shi ne abun da nake kokarin ganewa, ni kaina a rikice nake Salim…”
Be sake ce mata komai ba ya katse kiran, sai ya jefar da wayar a kasa ta fada a gadonta tana kuka mai karfi, bata taba jin kaunar Captain ba irin yau bata taba sanin tana sonsa so mai tsanani ba sai yau.
CAPTAIN JAMAL POV.
Babbar rigarsa ya cire ya juyo ya dauki wayarsa ya amsa kiran dake shigowa.
“Ranka ya dade barka da yamma”
“Barka dai Allah yasa akwai labari mai dadi”
“Akwai ranka ya dade, duk mutanen da ka aiko mana da sakon sunayensu mun kama wasu mun bincike su wasu kuma mun musu barazana a waya sun goge posting din sun bada hakuri, sai dai dukansu sun ga horunan ne a wani gurin ne suka kwafa suka yada abun, su ma kuma duk mun bisu mun saka sun goge kuma sun bada hakuri, mutum daya ne ya ce mana wani ya turo masa hotunan da bayani shi da aka turowa da kuma mu da ya fadawa mun bincika account din sai muka samu an goge account din.
“Na gode sosai already a nan mun riga mun gane wanda ya aikata abun, daman dai bukatar mu a batar da hotunan daga internet, thank you so much, zan tuntube anjima”
“Thank You Sir”
Ya sauke wayar Adaidaita lokacin da mahaifiyarsa ta biyo bayansa ta daga bangaren Daddy. Kallonta yake yana rike da wayarsa har ta karaso inda yake tsaye tana murmushin takaici.
“Congratulations ka yi aure Jamal, ka auri yarinyar da haukan ka yake nuna maka kana sonta, alhalin kanka ka wulakanta, makiyi zasu mana dariya su maka, ka zama abun kwatance a cikin sa’ainka da friends dinka, saboda ka auri makauniya kuma yarinyar da a yau idan na bude data na zan iya ganin siraicinta, wani ya rigaka taba jikinta, yarinyar da mahaifiyar da kuma kaf danginka ba a maraba sa zuwanta amman a haka farinciki kake kana jindadin ka samu mata, a daura aurenka a cikin gida, daga mahaifinka sai masu aikin gida sai uban yarinya, kai da ya kamata duniya ta san ka yi aure labarin aurenka ya cika kafafen sada zumunta sai gashi ya kare a karamin gida kamar wanda ya aikata sheri”
Ya rage tsawonsa ya zauna akan gado.
“Ammy na san baki son yarinyar nan, ba zan iya sakawa ki so ta ba, amman dai ina son ki sani ni dai ina kaunar yarinyar nan irin kaunar da ban taba jin ina yi ma wata mace ba, kuma jifanta da kike da kalamai marasa dadi ni kike gogawa bakinciki domin ita din matata ce a yanzu”
Ta kara yin murmushi tana daga gira.
“Haka ne Romeo uban soyayya, matar ka ce tabbas babu wanda ya isa ya goge wannan, ni kuma uwarka ce na fi matarka karfin ikonka a kanka, kuma har abada ba zan taba karbar Hurriya a matsayin suruka ba, ba zan taba sonta ba”
Har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleshi ta nuna shi da yatsa.
“Jamal ni na haifeka ka nuna min karfin soyayya, mahaifinka kuma ya nuna min karfin iko, ni kuma a yau zan nuna maka karfin hakki…”
Da kakkausar murya ta fada masa haka ta juya ta fice daga dakin. Captain ya soke kai kasa damuwa na baibaiye shi.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…
Bayan kwana biyu….
After ya yanke kiran da ya shigo daga Ethiopia, cikin rashinya sauko da kafafuwansa ya sauko daga kan gadon cikin rashin kuzari, ya saka bedroom slipper dinsa ya nufi kofar falon ya bude ya fita. Downstairs ya sauko ya nufi falon kakarsa Hajiya Nene ya zauna a kusa da kakarsa yana gaisheta. Sai ta kai hannu ta taba jikinsa ta amsa.
“Lafiya Kalau Jamal ya karfin jikin?”
“Alhamdulillah”
Ya kalli Ammynsa dake zaune sanye da doguwar rigar abaya kanta babu dankwali.
“Ammy ina kwana?”
“Lafiya Kalau, ka ci abinci?”
“No zan ci anjima”
“Haka ka sabawa kanka da wannan dabi’ar baka son cin abinci? Saboda ka daga min hankali ne?”
Ya kasa daga ido ya kalleta.
“You fake it ko Captain? Tun ranar da mahaifinka ya bar garin nan baka sake sakin jikin ba, abinci ma baka son ci”
Ko bata fada masa kai tsaye ba ya fahimci abun da take nufi.
“Ammy an faking ciwo ne? Bana yin komai saboda na daga miki hankali. Tashin hankalin tashin hankalina ne”
Ya kalli wayar hannunsa ya mike tsaye.
“Bari na amsa wannan kiran”
Ya fice daga falon. Ammy ta bishi da kallo
“Da gangan yake wannan abun”
“Da gaske ba shi da lafiya, na taba jikinsa yanzu da zafi sosai, ki kalli idanuwansa ki gani yaddda suka sauya alamar zazzafi yana damunsa sosai kuma ya rame sukuninsa duk ya sauya, Turai karki zama irin sukunan mana masu kishi da matan yayansu”
Ammy ta juyo ta kalli In-law dinta.
“Ba kishi nake da yarinyar ba, Allah ya tsare ni ba zan taba zama daya daga cikin irin wadannan iyayen ba, kawai ba ma the same team ne, ke ma kuma kina goya masa akan abun da kowa ya san ba daidai ba ne a gidan”
“Miye ba daidai ba? Goyo masa akan abun da addinin be haramta ba? Ko kuma son abun da danki yake so? Ke ce ba daidai ba, tun a ranar da aka daura auren yaron nan baki bar shi ya fita ko’ina ba, kin tsare shi a gida kamar mace gashi nan kin haifar masa da damuwa”