VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Masoyana Asallamu Alaikum mun sake haɗuwa a wata sabuwar tafiya, Allah ya sa mu wanye lafiya kuma mu kai karshenta cikin farinciki da Amince.
Sakon gaisuwa da fatan Alheri daga taku mai son farincikinku Khadeeja Candy 08036126660.

https://chat.whatsapp.com/LimnMeG0kWvIfT6JQvVMh1

☆❁ ❁☆

2️⃣

Ta aje plate din hannunta da sauri ta zari tissue ta goge bakinta.

“Amma na tafi kar na yi latti”

Amma dake kokarin jefa tawul a ruwa ta ce

“Kya ji da shi, kullum ke ce uwar yan latti sai an jiraki, ga kokari ga buga latti”

Hurriya ta dauki jakarta ta makaranta da sauri ta goya tare da daukar lunch box dinta ta fice daga falon da gudu, kamar zata fadi haka ta isa bangaren Appanta sai haki take kamar wadda aka yi yakin duniya tare da ita. Hannu ta mika jikin window falon kamar yadda sauran yan mata sa’aninta da wandanda suka girmeta suke mika na su hannu suna karbar karamin hollandia da chocolate da yake raba musu, tana son karba yan’uwanta na tureta tana yin baya har sai da suka gama karba sannan ta samu karba daga gurin mahaifinta, kyautar wani abun ci da ko abun sha a kowace safiyar week days wani abu ne da ya sabawa yaransa da shi tun suna kanana.

“Na gode Appana”

Ta fada tana murmushi jindadi, shi ma murmushin yayi yana kallon kyakkyawar yarsa, mai yawan yi masa godiya da nuna masa jindadinta a duk lokacin da yayi musu kyauta komai kankantar kyautar domin haka mahaifiyarta Amma ta koyar da ita, kusan ita ce karama a cikin yayansa mata a cikin maza kuma kanenta Hamad ne karami ƴaƴansa na jini amman ya fi sauran yayansa godiya da yabawa idan yayi musu abu.

“Allah ya miki albarka Hurriya, ga ladabi ga basira”

Ta yi yar siririyar dariya mai sauti.

“Appa haka Uncle dinmu yake cewa, har da cewa yayi wai akwai wata gasar da zan sake shiga”

“Da kyau ni ma ya fada min haka, kuma yace wannan gasar ma mai tsoka ce, suna kyautata zaton idan kika yi ta daya za su dauki nauyin karatunki domin haka suke yi ma duk wadda yayi na daya, ni kuma na kara musu da cewa ko da ba su fitar da ke ba, zarar kin kallama makarantar da kike yanzu zan fitar da ke waje ki yi karatu mai kyau, duk kuwa da bana sha’awar fitar da ƴaƴa mata waje yin karatu amman ke zan fara akanki”

Ba shiri Hurriya ta bude baki tana mamakin jin furucin mahaifinta.

“Appa da gaske?”

“Da girmana zan yi karya?”

Ta saki chocolate din da hollandia ta rufe baki tana zaro ido kamar zai fado. Sai kuma ta daka tsalle ta dire.

“Appa i love you i can’t wait”

“Ki dage da karatu Allah ya taimaka ina alfahari da ke, Allah ya miki albarka”

Ya fada yana murmushi yana nuna mata alamar lokaci a hannunsa da babu agogo, sai ta duka ta dauki abun da ta zubar ta.

“Ameen ina sonka Appana, na tafi sai na dawo”

“Allah ya kiyaye,”

Ta amsa da Ameen already ta sauka entrance din tana hadawa da gudu domin yan’uwanta sun kusa isa gurin bus din dake kaisu makaranta ta maido su. Tana daf da isa ta ji an fisge chocolate din dake hannunta kamin ta juyo aka fisge madarar hollandia din dake dayan hannunta. Suna hada ido ta bata fuska ta buga kafa kasa, shi kuma ya saka dariya yana kokarin bude ledar chocolate din.

“Yaya Yassar dan Allah ka ba ni”

“Wallahi ba zan baki ba”

Ya fada kai tsaye yana mata dariyar keta, juyawa ta yi cikin yanayin damuwa ta koma bangaren Appanta wannan karon bata tsaya gurin windows din ba ta murda kofar falonsa ta shiga, sanin talkamin makaranta ne daure a kafarta sai ta fadi kasa tana rarrafe dan kar ta taka masa carpet.

“Appa Appa Appa”

Alhaji Haruna ya fito daga dakinsa da sauri jin yarsa na kiransa.

“Hurriya baki wuce ba?”

“Appa YaYa Yassar ya kwace min abun da ka ba ni, na kowa yana nan ni ya karbe nawa”

Appa yayi murmushi ya juya ya koma ciki, be dade ba ya fito rike da wani chocolate din da hollandia ya mika mata.

“Appa dan Allah ka kora Yaya Yassar daga gidanka ka ce ya tafi ya bar maka gidanka, Wallahi takura min yake yi da yawa”

Tana fada tana saka hannu biyu ta karba.

“Idan kin hadu da shi a yanzu ki fada masa na ce ya hada kayansa ya bar min gidana, saboda ya cika takuraki ke da gidan Appanki”

“Appana na gode, zan fada masa haka a yanzu kuwa”

Cikin shagwaba da jindadi ta fadi haka sannan ta mike tsaye shi kuma ya kai hannu ya shafa kanta dake cikin hijab domin ya fahimci a bakin gaskiyarta take fadar Yassar ya bar gidan. Tana kokarin juyawa Amma ta shigo falon dauke da tray, bata yi mamakin ganin Hurriya a sitting room din mijinta ba, daman ta fi kowa yin latti zuwa makaranta ko fita unguwa. Musamman idan mahaifinta yana gari, a dole sai ta ganshi sannan zata fita, idan kuma bata zuwa ko’ina to tana zaune tare da shi a bangarensa babu ruwanta da ranar girkin Amma ne ko na Hajiya Kaltume ko Momy, ko da bata shiga har inda yake ba indai ta san yana nan zata zauna a part dinsa ne, hakan ya haifar da shakuwa sosai a tsakaninsu.

“Daman ai duk wanda yayi shiririta a garin Gusau a bayanki yake, ke kam Allah ya shiryar da ke Hurriya”

Dariya kawai ta yi ta fice tana fadin.

“Appa ka fada mata abun da Yaya Yassar yayi min. . .”

Daga mahaifiyarta har mahaifinta binta suka yi da kallo jindadi da farinciki har ta fice, sannan Amma ta girgiza kai ta maida dubanta ga Appa.

“Bismillah Appan Hurriyya muje ka karya”

Kamar wanda aka jefo a wata duniyar haka yanayin fuskarsa ya sauya daga murmushi da jindadi zuwa bakinciki da bacin rai da be san dalilinsa ba, ba dan komai ba sai dan jin muryar Amma a bayansa.

“Zan shigo”

Ya amsa ba tare da ya jiyo ba, domin baya son kallonta a yanzu, fuskar dake masa kyau da kwarjini, mace da yake gani yana jin kamar shi da ita sa’anin juna ne, a yau ita yake kyamar gani, muryar da ta fi kowace murya yi masa dadi a duniya yau muryar ce yake jin kamar tana sanar masa mutuwa. Cikin hikima da kokarin danne damuwa ta sauke ajiyar zuciya domin ta san shekaru da aka fito da watanni mijinta ba haka yake ba, a da idan ta kawo masa abinci jiki na rawa yake tarbarta ya fara zuba santi tun kamin ya ci, ba zai ma bari ta fara isa bedroom dinsa ita kadai ba sai ya rika mata tray ko ya dauki wani abun yana zolayarta, amman a yan kwanakin da idan aka a hada su aka kirga zai bada wata daya ya sauya mata gaba daya.

Sai da ya tabbatar ta shige sannan ya juyo ya kalli kofar dakin, hannu ya saka a kirjinsa ya danne tashin hankalin da yake jin yana kusantoshi. Cikin wani yanayi mai kama da nauyin jiki da na zuciya ya cira kafarsa ya fara takawa tare da maida hannayensa baya ya rumgume yana tafiya a hankali. Yana shigowa cikin dakin Amma ta juyo ta kalleshi da damuwar da ta gagara boyuwa a fuskarta.

“Ranka ya dede waya canja Bedsheet din nan?”

Tsaye yayi yana kallonta kamar mai tunanin kalar amsar da zai bata, kana kallon idinsa zaka karanci damuwar dake tare da shi. Can kuma ya kawar da fuskarsa ya dawo da hannayensa dake rumgume a bayansa ya zuba su cikin aljihu.

“Kaltume ce ta canja”

Da matukar mamaki Amma take kallonsa, domin al’adarsu ce duk wanda ke da girki ita zata gyara bangaren mijinta kuma zata tafi da Bedsheets dinta ta shimfida, idan wata zata karbi girki sai ta kwashe kayanta wadda ta karba ta shimfida nata ta kula da bangaren, hakan ya saka ko wace mace da kalar kamshin turaren dake fita a part dinsa idan girkinsu ya zo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected