Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Barka dai”
Ta amsa a takaice fuska ba yabo ba fallasa sannan ta shiga motar ta zauna, shi kuma ya rufe murfin motar gently, sannan ya zagaya ga shiga bangarensa, ya kalleta bayan ya rufe bangarensa yana tunanin ko zata masa wani karin bayani ko shawar before su tafi.
“Za mu oya tafiya?”
‘Da gaske umarni na yake jira? Wai duk wannan na miye ne? Meye haka? Why why?’
Ta tambayi kanta, a zahiri kuma sai ta amsa masa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba.
“Yea…”
Yayi baya da motar tare da juya kanta sannan suka fice daga gidan.
HURRIYA POV.
Hurriya na kwance jikin Hajiya Binta tana game da keypad dinta, Hajiya ta ce.
“Wato da wani gurin kika fada shi ke nan babu wanda zai biyo bayanki ya binciki lafiyarki, shi sun rufe masa ido su kuma babu wanda Allah yake ranta kowace daga ita sai Yayanta take hange”
“Haka kwanan baya suka laka min sata, Momy ta ce na sace mata sarka da kudi, kuma ban dauka ba, amman Hajiya ma cewa ta yi wai zan iya yi saboda na canja hali, Appa ne kawai ya wanke ni, da Allah kadai ya san dukan da zan sha a gurin Yayana tun da shi ne mai hukunta mutane, kuma da kowa sai ya rika kallo a matsayin barauniya”
Hajiya Binta ta daki kirjinta.
“Sata Hurriya? Sata dai sata? Ke Nafisa ta zarga da sata?”
Hurriya ta tashi zaune tare da amsa mata da kai.
“Har da cewa ta yi ba zata bari da Allah ba, amman ni dai har yanzu ban ji ance an gane barawo ba”
“lallai rashin uwa a gida kukumi ne, saboda suna ganin baki da kowa shi ne suke kwaso sharar sai ya sauke kanki, ai baki gadi sata ba Hurriya uwa da uba, yanzu da uwarki bata da rai haka mutanen nan zasu rika ki? Ke ta ce kin satar mata?”
“Sakar zinari da kudi mai yawa, har da sarkar Yaya Namra kuma ban shiga dakin kowa ba… ”
Ta fadawa Hajiya yadda komai ya faru, idon Hajiya Binta ya cika da kwalla.
“Ashe haka kike ta rayuwa cikin matsuwa a gidan nan? Duk fadin gidan nan da ma’aikatan cikinsa a rasa waye za a zarga sai ke?”
“Ai Appa ya wanke ni yace ni ba barauniya ba ce”
“Me yasa baki fada min ba? Amman ko yanzu bata bace ba”
Hurriya ta kalleta da sauri.
“Hajiya ai ya wuce”
“Be wuce ba, uwarki bata min komai ba sai alheri, Allah ya mata albarka ya bata lafiya, ta kula da ni kamar ni na haifeta, ba zan taba bari yayanta su wulakanta ba, ba zancen sata kadai ba ko wannan korar da aka yi miki ba zan kyale ba, domin idan aka kyalesu nan gaba za su aikata wanda ya fi wannan ma, gobe zan yafa mayafina na tafi duk sai na ci musu mutunci”
Hurriya ta fasa kuka da yafi kama da shagwaba.
“Hajiya Wallahi zaki ja min ne kawai ace na zo na yi minahicci”
“Uwarki bata min komai ba sai alheri, matukar ina raye ita ko yayanta ba za su wulakanta ba”
“Aa Hajiya ni dai dan Allah kar ki yi”
“Ba gidan zaki koma ba balle su ganki su wulakantaki, nan zaki zauna kuma yadda wannan abun ya tsaya min a rai idan ba amayar da shi ba ba ni da kwanciyar hankali”
Duk yadda Hurriya ta so lallaba Hajiya Binta ta hakura da maganar, bata saureta ba.
“Ni da na sani ba zan fada miki ba Hajiya”
“Ai shi yake cutarki, ta nan kika sha banban da dan’uwanki, Hamad komai aka yi masa sai ya rama kuma sai ya fada min, bawan Allah Allah ya masa rahma”
“Ameen”
Hurriya ta amsa cikin rashin ji dadi tare da daga kai ta kalli kofar falon da Namra ta turo ta shigo da Sallama.
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.
Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo…
Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660
@
1️⃣9⃣
“Yau Namra ce a gidan na mu”
Hajiya ta fada tana kallonta, cikin karfin hali Namra ta yi murmushi ta nemi guri ta zauna. This is the first time da ta ji bata sha’awar hada ido da Hurriya.
“Hajiya barka da dare”
“Barka, yau na ci arzikin Hurriya kin zo gidan nan kenan”
“Haba Hajiya daman can na kan zo na duba ki fa, karki ce saboda Hurriya na zo”
“To ssboda wa kika zo tsakaninki da Allah?”
“Sabosa Hurriya”
Cewar Namra tana dariya, Hurriya kuma dadi ya cika ranta jin cewar yar’uwarta ta biyo sawunta, sai dai abun da bata sani ba shi ne ba tafiyace ta zuwa gurinta kai tsaye ba tafiya ce ta Salim ba dan ita ba.
“Yaya Namra ina wuni”
“Lafiya Kalau Hurriya”
Ta amsa tana murmushin da ya fi kama da an mata dole.
“Ato ke dai kin kyauta da kika biyo sawu, daman ke kin fita dabam ba da yan’uwanki, amman Nafisa kam da Kaltume rayuwarsu tana ba ni mamaki, yanzu Hurriya ta gama karanta min abun da ya faru, ashe abun har ya kai a laka mata sata Namra?”
Namra ta kalli Hurriya ba tare da tace komai ba ta dauke ido.
“Ban yi zaton zamu yi ma yarinyar nan haka ba, saboda kawai bata da uwa cikin gida sai ta zama abar wulakantawa, ban jidadi ba, yanzu ko korar nan da aka yi mata da ke ce ko Khairy ai babu wanda uwarta zata yarda ta bar gidan, da bata da ni ya rayuwa zata zame mata? Ke kuma ya kamata ace kuna nunawa iyayenku wasu abubuwa be kamata su yi ba, wani abun ba za su lura ba sai an lurar da su”
Hurriya dai kanta na kasa tana jin kamar ta rufe bakin Hajiya Binta. A kokarin Namra na kawar da maganar ta kalli Hurriya tana jin wani abu a zuciyarta game da Hurriya ta ce.
“Da bako nake fa, kuma ke yake jira magana ya zo yi da ke?”
Hurriya ta dago ta kalleta. Hajiya kuma ta tambaya.
“Wane bako kuma?”
“Ita tasan wa nake nufi, ya zo ne yayi magana da ita sai mu tafi”
“Waye ne ban san waye ba?”
“Salim Sarauta… Yana waje”
Namra ta amsawa Hurriya kai tsaye kamar yadda ta bukata. Hajiya Binta kuma ta kalli Hurriya ta ce.
“Saurayinki ne?”
“Aa Saurayin Yaya Namra ne, yana yawan tambaya ne, maybe ko yana son mu gaisa ne”
“To tashi ki tafi, idan kun gaisa sai ki dawo”
“Toh”
Ta amsa umarni, Hajiya ta tashi ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka sannan ta fito ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Binta ta fara karantawa Namra sakon da zata bawa Momy da Hajiya Kaltume. Cikin natsuwa Hurriya ta fita harabar gidan, sai da ta gama kallon ko’ina sannan ta nufo gate domin bata ga bakuwar mota a gidan ba bayan motocin da Appa ya ajewa Hajiyarsa guda biyu. Sai da ta fita gate din gaba daya sannan ta yi arba da motar dake fake gefen gate din gidan, tun kamin ta fito zuciyarta ta raya mata a waje ya aje motar ganin babu bakuwar mota a harabar gidan Hajiya Binta. Kamin ta karaso ya bude motar ya fito yana taba wayar hannunsa, da alama wani abun yake typing amman idonsa yana kanta har ta iso, cikin far’a da sakin fuska ta yi masa sallama da muryarsa mai dadin sauraro.