VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Sai a lokacin Hamad ya gane dalilin  Captain na maida shi hostel din makarantar da yayi.

“Wata kila ya samu hotunan ne ta hanyar Adam”

Hurriya ta fada, Captain ya daga mata kai.

“Ni ma haka nake zato, ko da sanin Adam ko kuma a sirrance domin dan’uwansa zai iya fada masa matsalarsa shi kuma kishi da haddasar ni na same ki ba shi ba ya saka shi aikata hakan….”

Amma ta share hawayenta tana taba Hamad dake zaune kusa da ita yan biyu suna zaune a cinyarsa.

“Na dauka da gaske Hamad ya mutu, na karbi wannan kaddarar amman Hurriya ta ki ta karbi wannan”

Hamad ya kalli Hurriya ta kalleshi. Captaim ya ce.

“Ya taba fada min cewar Yana fada yawan fada da yar’uwarsa yanzu kuma yana son neman lafiyarta kuma gashi bata nan…”

Suka yi Murmushi. Yasir  ne mutum na farko da ya fara mikewa tsaye ya fice daga falon. Sai da ya dauki lokaci sannan Rukayya ta bayansa. Gingine ta same shi jikin motarsa ya rike kansa ya rasa me ke masa dadi a duniyar nan.

“Yasir…”

Ya dago ya kalleta sai ya kawar da idonsa.

“Minene Rukayya?”

“Ya kake?”

“Lafiya kalau”

“Dan Allah karka boye min ya kake?”

Da ya dube ta sai ya ga hawaye take zubarwa shi ma sai na shi hawayen dake makale suka zubo.

“Ban sani ba, ko za su zabi kai Hajiya gidan yare ko akasin haka, amman ba zan iya zama garin nan matukar mahaifiyata ta kasance a gidan yari, ba ni da sauran farinciki a yanzu. I respect your parents decision da suka hanani aurenki suna da gaskiya”

“Yasir shin har yanzu kana so na?”

Ya dubeta da kyau sai yayi murmushi ya dago wayarsa ya nuna mata hotonsa da yake a screen din wayar, sannan ya sauke ya tafi ya bar a gurin tsaye. Amma da yan’uwanta suka koma bangarensu suna tattauna abun da ya dace Appa ma yana tattauna da nasa yan’uwan. Captain kuma ya fito yana magana da Hurriya, so yake ya dauketa su je family house dinsu su ganta even though Magariba ta gabato, ita kuma tana son kasancewa da yan’uwanta a yanzu.

“Idan mun tafi can Nene zata iya cewa na kwana a can ai ko?”

“Ya za’ayi tace miki haka bayan kuma ta san kina da MiJinki?”

Ya duba yaga babu mai ganinsu sai ya kama fuskarta yana kallon kwayar idonta.

“Alhamdulillah you can see now my baby my heart my soul my duniyata”

Ta yunkura zata yi dariya sai amai ya cika mata baki, da sauri ta ja baya ta juya ta fara kwarara amai a gurin kamar zata amayar da yan hanjinsa. Captain ya shiga cikin ya dauko mata ruwa ya wanke mata bakinta sai da yayi da gaske sannan ya iya danne zuciyarsa domin shi ma aman ya ji yana taso masa. Ya taba jikinta.

“Sannu kina jin rashin lafiya ne?”

“Aa amman kai jikinka da zafi, ko zaka tafi asibiti ne?”

“Maybe gobe, amman ba yau ba dare yayi, ki shiga ciki ki huta gobe zan tafi na kai ki gurin su Nene”

“Toh.. Sai da safe..”

Har ta juya sai ta ji an riko hannunta an dawo da ita.

“Hurry na.. Me kika ci ya saka ki aman nan? Me yasa kika yi amai?”

“Ban sani ba”

Ta dan yamutsa fuska.

“Turarenka nan ne bana so yanzu”

Yayi murmushi ya rika hannunta ya nufi gurin motarsa.

“Me ye ina zamu je?”

“Asibiti”

“Babu asibiti da yamma fa..”

“Ta barrack zamu tafi likotocinsu kullum available”

“To ai ni lafiyata kalau”

“Ni zaki raka”

Ya bude motar ya saka ya zagaya ta dayan bangaren ya shiga yayi ma motar key. Sannan ya kama hannunta daya ya rike yana tuka motar.

“Ban a kwashe aman ba, idan wani ya gani zai ji kazanta”

“Idan mun dawo sai ki fada a kwashe”

Be tsaya ko’ina ba sai asbitinsu na Barrack yana zuwa aka hau yi mata gwaje gwaje mamaki ya hana ta magana bayan kuma yace shi zata raka, ba ayi taru ba sai a gurin da za a debi jininta a auna, nan kam sai da ya zauna a kujera ya rumgume da karfe ya rike hannun sannan aka dibi jinin. A nan ya barta ya tafi yayi sallah ya dawo sannan ya karbi results. Be bude ba sai da suka isa gurin mota yana karantawa yana murmushi.

“Me suka ce? Ka shafa min rashin lafiya ko? Kai ne fa mai ciwo”

“Baby na kin dai shafa min laulayi”

Ya kashe mata ido daya, sai ta yi fuskar rashin fahimta.

“Ban gane ba?”

“Minene Albarka aure?”

Ta dan yi shiru…

“Kwanciyar hankali da zaman lafiya”

Ya daga kansa sama yayi dariya sannan ya jata jikinaa ya rumgume yana jin wani irin kaunarta a ransa.

“Silly Girl, albarka aure haihuwa”

Ta dago da sauri ta kalleshi tana kwalo ido baki sake, sai ya daga mata kai ya sumbaci goshinta.

“Uhmmm”

Ya shiga sumbantar fuskarta ta ko’ina, kamar ba a public place suke ba, he just got lucky inda suke babu kowa gurin aje motoci ne kuma ko akwai bariki babu ruwan kowa da rayuwar kowa.

Ya bude Mota ya saka matarsa sai da ya sumbanci hannunta sannan ya rufe motar ya zagaya dayan side din ya shiga ya sake sumbantar ya kama hannunta ya rike yana tuka motar.
Wani irin farinciki yake ji marar misaltuwa a zuciyarsa, be taba tunanin haka ake ji ba idan mace tana dauke da cikin ďan mijinta sai yau, baya iya bayyana yadda yake ji a zuciyarsa son matarsa ya ninku a ruhinsa.

“Ki kula da kanki please”

Ya fada a lokacin da ya bude mota ta fito. Ya waiga ya ga idan babu mai kallonsu sannan ya juyo ya rumgumeta ya sumbanci goshinta. Ya kama fuskarta ya aika mata da wani killer look.

“I Love You so much sanyin idanuwana, thank you for this”

Ya taba cikinta. Hawaye ya zubo idonta ita kanta she can’t believe ciki ne a jikinta so she’s going to be a Mother now..

“Ni ya kamata na gode maka, you came in to my life by accident sai kuma ka zama cikar farincikina, abokin rayuwata, silar share hawayena, ka min alkawarin kyakkyawar duniya mai ciki da farinciki kuma ka fara va ni tun a yanzu… Buri yana ta cika saboda kana kusa da ni, ina matukar kaunarka Jamal duk mace da ta samu namiji irinka a matsayin miji hakika ta dace da Abokin Rayuwa na gari mai son farincikinta, kai din wata babbar kyauta ce da Allah yayi min ta inda ban yi zato ba kuma a lokacin da ban yi zato ba…”

He weep her tears yana murmushi ya sumbanci bakinta ya latsa kasan lips din.

“My cute Baby my happiness, anything for this Girl”

Ta yi murmushi ta sauke hannunsa kasa.

“Kar wani ya gan mu fa…”

“Zaki kwana gidan nan ne just for today, i can’t wait na bude ido gobe na gan ni a kusa da ke, i love you”

Zata amsa masa da i love you too Hindu da Inna Uwani suka fito, sai ta yi saurin juyawa daga fuskantarsa da take ta kallesu.

“Hurriya ke kika yi amai dazun? Twin yace mana ga aman nan a waje Rukayya ta kwashe kuma sai ba mu ganku ba..”

“Eh Captain ne yayi ba shi da lafiya tun a gida shi ne yau sai yayi amai, yanzu ma na raka shi asibiti ne aka ce malaria ce take damunsa”

Captain ya kalleta da sauri, jin yadda ta daure shi a take tace shi yayi mai kuma shi ta raka asibiti.

“Subhanallahi… Jamal babu lafiya?”

Hindu ta tambaya, sai dan yi shiru kamar wanda ya rasa me zai ce.

“Eh…… Amman da sauki asibiti muka fito yanzu suka ce Hurriya…”

Ta kalleshi da sauri tana zare masa ido. Sai ya sauya maganar daman yayi haka ne kawai saboda ya tsorata shi ba zai iya fadar tana da ciki ba a gurin yan’uwanta.

“Sai suka ce ma Hurriya ina dauke da malaria”

Ta daga mishi kai alamar haka ne daidai.

“Sannu har da gajiya ai, kana kokari sosai Wallahi….”

“Na gode zan tafi sai da safe…”

Ya musu sallama ya bude Motarsa ya shiga yana jin zazzabin da Hurriya ta kira masa yana kara rufe shi. Hindu da Inna Uwani suka nufi gate Hurriya kuma ta shiga bangaren mahaifiyarta tana jin komai kamar ba gaske ba. Ta daga kai tana kallon bangaren bayyana yadda farinciki yake a gurinta yanzu abu mai wahala, mahaifiyarta ta dawo a karkashin inuwar mahaifinta a yayinda ita kuma take karkashin kulawar nata mijin, ga dan’uwanta a kusa da ita. To yanzu me ya rage mata? Mai hakuri mawadaci wahala ko bakinciki basa taba daurewa a rayuwa, haka ma dade da farinciki basa dauwama har abada, sai an bude ko wane shafi na rayuwa… Ta shafa cikinta tana murmushi ta samu amincewar ubangiji zata iya ganin abun da ta haifa nan gaba. Jin kukan Rukkaya ne ya kawar mata da duk wani tunani da take a lokacin sai ta yi hanzarin shiga cikin falon dake dauke da mahaifiyarta, Gwaggo da kuma Rukayya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected