Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Captain ya fada mata yana kokarin kwantar mata da hankali. Hamad ya share hawayensa ya ce.
“Idan ace Hajiya bata mutu ba, sai na kashe ta da hannuna…”
“Baka bukatar yin haka, jami’an tsaro da kotu zasu yi aikinsu”
Captain ya fada sannan ya karasa ya zauna kusa da matarsa ya kama hannunta ya rike sai ta kwantar da kanta jikinsa.
“Da gaske wai Hamad din ne dai? Innalillahi Wa’inna’ilaihirraji’u, wannan wane irin abu ne? Hamad…”
Mama Rukayya ta fada sannan ta nufe shi ta rumgume tana kuka sosai shi ma kuka yake yana kewar kanwar mahaifiyarshi…
Sai da suka sake yin two days a garin saboda processing din da Appa ya bi na ganin an samu dawowa tare da Hamad ba tare da wata matsala ba, a tsawon kwanan biyun nan kullum Hurriya tana tare da Hamad sai idan ya bar hotel din zuwa school, idan ya dawo Hurriya tana tare da shi tsawon wunin ranar tana labarta masa abubuwa da suka faru bayan baya nan yadda rayuwa ta zame mata a gidan Appa bayan tafiyarsa har zuwa aurenta da sherin da aka yi mata. Duk abun da suke Captain sai da yayi ta kallonsu gwanin sha’awa domin shi dai be san dadin dan’uwa ba.
“Na yi kewarki sosai Hurriya na fi jin kewarki fiye da kowa, saboda ina yawan dukanki ina zalintarki, da Captain ya fada min cewar bani da kowa a yanzu, sai na tuna abubuwa da nake miki na ji kamar na akashe kaina abun yana ta damuna…”
Hurriya tana hawaye ta ce.
“Yanzu duk mun girma Hamad, daman can kurciya ce, kana da zafin zuciya ni kuma bana iya raba kaina da kai, shiyasa har Amma ta yi maka takwara ban yarda ka mutu ba..”
Captain ya mika mata waya.
“Cry Cry Baby Ammy zata yi magana dake”
Ta karbi wayar ta kara a kunne.
“Hello Ammy ina wuni..?”
“Lafiya kalau, ya idon naki?”
“Alhamdulillahi ina ta samun sauki”
“Ya na ji muryarki wani iri? Ko Captain din ne yayi miki wani abun?”
“Aa ba shi ba ne”
“Ba shi wayar”
Hurriya ta mika masa wayar sai ya zauna kusa da ita ya kara wayar a kunne.
“Ammy”
“Wani abun ka yi mata ne? Na ji kamar tana kuka?”
“Ban mata komai ba, ya za’ayi na mata wani abu Ammy yaushe muka yi auren ma da za’ace har mun fara samun tsabani?”
“To waye be san halin maza ba? me take yi ma kuka?”
“Tana tare da dan’uwanta ai na fada miki abun da ya faru, kuma idan suna tattauna labarin baya tana yawan kuka shi ne kawai”
“Ayyah ba ka ce gobe za su dawo ba?”
“Eh in Sha Allah daman amincewar makaranta Muke jira kuma sun ba mu takardar a rubuce za mu taso gobe da safe da yardar Allah”
“Allah kawo ku lafiya, ku kula da kanku”
“I will i love you Ammy”
Ta gwatsale shi.
“Dan Allah can ko kunya baka ji a gaban matarka da kanenta sai ka ce wani yaro”
Yayi dariya ya sauke wayar. Hamad ya kalleshi.
“Kai mutumen kirki ne Captain ka kula da ni yadda ya kamata, Hurriya ta ba ni labarin yadda ka yi mata yaki, amman me yasa ka ce min kowa ya mutu?”
“Idan mun je zaka ji”
Captain ya juyo da fuskar Hurriya
“Mai tsada me za miki order?”
Ta juya ta kalli Hamad.
“Hamad me zaka ci?”
“Haba Baby ina lallabaki ki ci abinci ke kuma da wannan gwaskan kike? Babu inda be sani ba a garin Addis Ababa ki daina damun kanki da cinsa”
“Ko a gida haka muke, inda har zan ci abinci to zan zuba masa ne ya ci, ka yi hakuri
Yaja hancinta yana murmushi.
“Tsokanarki nake, tambaye me yake so sai na siyo muku”
Hamad yayi murmushi yana ganin kamar mafarki ne, wai yayarce da mijinta zaune tare da shi a yau.
“Yayata mai kaunata yar’uwata abar alfaharina”
“Ba ka ce ni ba yayarka ba ce?”
Ta tambaya tana hawaye shi ma hawayen yake yana murmushi.
“Ada kenan yanzu na bar miki girman”
Ta yi murmushi cikin hawaye, Captain ma Murmushi yayi ya tashi ya fita.
Ya sake daukarsu awa biyar da mintuna kamin su iso Nigeria daga babban birnin Ethiopia. A Abuja suka sauka, ba su tsaya komai ba suka sake booking flight from Abuja to Kaduna, Ammy ta yi musu tarba ta musamman tana ta na’am na’am da matar danta kamar daman can babu wani abun da ya taba shiga tsakaninsu. Sai da suka yi wanka suka huta sannan suka hadu a teburin cin abinci da yake gidan. A nan Hurriya ta gane ubanta Alhaji Haruna Mai Yadi karyar arziki yake domin falon Ammy ma ba tile ba ne wani abun ne aka shimfida mai kamar ruwa, ga manyan kujerun da bata taba ganin kalarsu ba a rayuwarta, dinning din ma wani abun kallo ne a gurinta balle kuma dakin da suka sauka. Ko’ina na gidan kyalkyale ni kamar an watsa zinari. Bakauya ta zama a gidan komai ta gani sabo yake zama mata, a nan ta yarda da Momy take ganin kamar bata dace da auren Captain ta bangaren arziki. Masu aikin gidan ma kansu abun kallo ne basa barin komai ya zuba a kasa da zarar an aje abu za su zo da gudu su dauke.
Captain da kansa yaja mata kujera ta zauna, sannan ya zauna yana magana da mahaifiyarsa da ta zabi serving din matarsa da kanta ba kamar Momy Ikilima da Mama Rukayya da masu aiki suke zuba musu abinci ba, sai da ta fara ajewa Hurriya plate din abinci sannan ta zubawa Captain ta aje masa warin kwai dake kan salad ya saka shi jin tashi zuciya da sauri ya kawar da fuska yana yunkurin amai.
“Me ya faru wani abu ka gani a abinci?”
“No kwan ne na ji shi wani iri, bana son warinsa”
Ammy ta dauke plate din ta zuba masa wani abinci babu kwai har ya fara ci sai kuma ya ji baya son abinci kawai wani abun kwadayi yake so.
“To ko dan kun yi tafiya a jirgi ne?”
“Ammy karki sa na ji kunya mana, yau na saba hawan jirgi?”
Hamad ya kalleshi.
“Ko dai baka da lafiya ne?”
“I think so, jikina ma yayi zafi, tun da muka je ba wani lafiya nake ji ba, kawai dai ina daurewa ne saboda akwai abubuwa da yawa a gabana”
Ammy ta kalli Hamad.
“Wannan ne yaron? Shi da wanda kake yawan zuwa Ethiopia gurinsa daman? Da zarar ka samu sarari sai ka tsallake ka tafi Ethiopia ashe duk saboda shi ne?”
“Wallahi kuwa Ammy”
“Bari na kira Family Doctor ya dubaka kamin ku tafi”
“Okay”
Ammy ta tashi ta bar dinning din, Captain ya kalli daya daga cikin masu aikin gidan ya ce.
“Samo min wani abu mai ruwa ruwa na sha”
“To ranka ya dade”
Sai da Ammy ta kira likitansu na gida ya zo ya auna Captain ya duba shi ya fada musu fever ne kawai yayi masa allura ya kuma dorashi akan magunguna sannan suka bar garin Kaduna a business flight din Daddy da baya kasar domin ta waya ya gaisa da Hurriya yayi mata maraba da zuwa gidansa kuma ya saka Ammy ta hada mata goma ta arziki a madadinsa.
*A duk lokacin da nake littafi sai an tambaye ni minene POV saboda ina saka shi a duka books dina, POV yana nufin POINT OF VIEW. idan wata ta sake tambayata sai na cire mata hakorin gaba *
HAJIYA FATEE POV
“Hajiya jikin ne dai?”
Fadeel ya tambaya yana taba jikinta cike da damuwa Hajiya Fatee ya dago ta dubi danta, cikin bakinciki da nadama ta ce.
“Ko da jikinki bana bukatar tafiya asibiti yanzu Fadeel, ku bar ni na yi abun kunyana a nan idan ma kasheshi saku yi ku kashe, bayan na tafi”
Afrah ta girgiza kai.
“Haba Hajiya ki daina fadar hakan, abun da ya same ki kaddara ce daga Allah, kowa da yadda Allah ya rubuta masa kaddararsa, zai iya samun kowa, Allah ya tsare mu da kashe abun da kika haifa, ko me kika aikata muna son rayuwarki kuma ina sonki a haka saboda kw mahaifiyar Fadeel ce ina son miJina ba zan taba tsanar mahaifiyarsa ba”
“Na yi abun kunya, sanar matar ďana ina ta ganin kamar kin tare shi daga gareni ashe sheidan ne yake ta min gizo da sake sake, dubi yadda na zama na janyo muku abun kunya”