VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Amma bata san lokacin da hawaye suka zubo idonta ba murmushi kuma ya cika fuskarsa, yau Appa rayuwa yake aiwatar a gabanta irin yadda suka saba a baya kamin abubuwa su chabe musu.

“Allah ya saka maka da aljanna ya rabaka da Hajiya Lafiya ya yafe zunubanka ita kadai ce godiyar da zan iya maka a yanzu”

“Godiyar kenan, a daura auren ma idan tafi Ummara kina dawowa ki tare a dakinki idan ma baki bukatar zama a wannan gidan ni zan iya gina miki sabo da irin samfurin da kike so Hajiyata”

Amma ta rausayar da kai cikin yanayi na farinciki da damuwa domin a tsorace take har gobe.

“Ya Salam Alhaji…”

“Ahhh to Hajiya a free zan baki kujerar Ummara ki tafi ki dawo ki auri wani? Saboda ga Alhaji Haruna Mai Yadi Shashasha ko hmm?”

Dariya da kanta ta yi mazauni a hakoran Amma har sautinta ya fito tare da hawaye. Farin cikin da ya kwana biyu be ziyarci zuciyar Appa ba ne ya ziyarce a yanzu saboda ganin murmushin amaryarsa uwar yarsa Hurriya abar kaunarsa mai yawan biyayya a gareshi.

“Haba ko ke fa, ni na san ban saba cewa eh ki ce a’a ba yana daga cikin abun da nake yabonki da shi a kullum idan na tashi fada ko tuna, dan Allah karki fara a yanzu, ba halin kirki ba ne, wannan kafewar ma ban san inda kika aro ba, domin ba halinki ba ne baturiyata”

Amma ta saka hannu biyu ta karbi takardun ta koma ta zauna speechless tana kallonsu. Appa kuma ya ciro wayarsa dake ringing ya amsar wayar yana mamaki kiran da ya kwana biyu be shigo wayarsa ba sai yau.

“Wa’alaikussalam”

“Na’am Alhaji Hafeezu”

Appa yayi shiru na dan lokaci sannan ya ce.

“Aa ina wani guri mai muhimmanci amman dai yanzu zan tafi gida, mu hadu a can”

Ya katse wayar ya saka aljihun gaban rigarsa da babbar riga ta tare sannan ya kalli Amma ya ce.

“Hajiya zan tafi gida yanzu, daya daga cikin iyayen maneman auren Khairy ne ya kira ni a waya, ya ce yana bukatar ganin a zai same ni ni kuma na fada masa mu hadu a gida zai fi, tun da ga Alhaji Musa ma a tare da ni sai mu ji ko minene”

“Allah yasa mu ji alheri”

“Amin, kuma dan Allah ki fadawa Bappa ba sai ayi min godiya ba, kar ya kira ni na ki dagawa yayi zaton wani abu, Wallahi godiyar ce bana bukata, kuma ina jiran kiranki idan an saka ranar tafiyar kar lokaci ta matse”

“In Shaa Allahu”

Amma ta amsa da murmushi, shi ma murmushin yayi.

“Na gode uwar biyu”

Ya fada sannan ya fice ransa fes buk’atarsa ta biya, hakarsa ta cin na ruwa. Daga gidansu Amma kai tsaye gidansa ya nufa tare da Alhaji Musa yana bawa Alhaji Musa labarin irin biyayyar da Iyami take masa wanda abu ne da duk wanda yake kusa da shi ya sani. Yayi mamakin tarardar mutanen da ba zai iya kiransu da baki ba a gidan domin shi da su suna kusan zama surukai ne a matsayinsu na iyayen Fadeel. Tun a waje Appa ya gaisa da su sannan yayi musu iso suka shigo cikin falonsa suka zauna tare da shi, ganin yanayin fuskarsu dake dauke da damuwa ya saka Appa be yi wata hubbasa gurin ganin an kawo musu wani abun tabawa ba, domin alamu ya nuna ba farinciki ne ya kawo su ba, sai kishiyarsa.

“Toh Allah dai ya sa lafiya, irin wannan ziyara da rana tsana ba tare da wani abu ba”

Wanda ake kira da Alhaji Hafeezu ya yi gyaran murya ya kalli Appa cikin kyautata ladabi ya ce.

“Alhaji lafiya amman ba lau ba, wato maganar ce da nauyi shiyasa na ce zamu sameka a inda kake ban so mun zo nan gida ba sai dan ka bukaci hakan, domin ka yi mana karamci da hallacin da be dace ace mun furta wata magana makamancinyar wannan ba a gidanka”

Appa yayi murmushi mai cike da takaici.

“Karka damu Alhaji Hafeezu daman na saka tsammanin faruwar hakan, tun a lokacin da abubuwa masara dadi suka faru a gidana, na shiryawa fuskarta ko wane kalar kalubale, kuma na san zancenku ba zai wuce ku ce Fadeel ya janye daga zancen neman auren Khairy ba?”

Sai duk suka kallo juna ganin yadda yayi saurin harbo jirginsu. Appa ya sake fadada murmushinsa.

“Karku ji komai, yayi abun da ya dace kowa yana son auren yar kwarai, kuma ita kanta Khairy ba wai bata da tarbiya ba ne, kaddara ce dai irin wanda ta saba fadawa bawa, shi kuma yayi abun da yake ji ya natsu da shi ne, babu ta inda zai zama mai laifi a gurin kowa, ni din nan ma mai shiga gaba ne a nema masa aure idan ya samu wata yar da yake so”

Appa ne mai magana Alhaji Musa kuma ya fara fada yana ganin kamar hakan be dace ba, Fadeel din be rumgumi kaddara ba.

“Kayya dai assha dai..! Ba haka aka so, amman yara ne basa jin shawara kuma basa jin maganar manya na su hangen dabam yake, ya same mu sa zancen ne kuma yace shi ya janye, mu kuma muka ta inda aka hau ice ta nan ake sauka, da ace ya janye jikinsa kuma baka ji wani bayani daga garemu ba kamar hakan be dace ba, a matsayinmu na iyaye”

Appa ya sauke ajiyar zuciya daman ya san za arina, sai dai kuma jin albishirin be masa dadi ba, ko kadan domin yana neman mai kwashe masa Khairy ne a yanzu da shi kansa baya sha’awar ganinta.

“Yaro yana da gaskiyarsa kowa yana aikata abun da yake jin natsuwa da shi ne, a addini ma ance ka bar abun da kake kwankwato zuwa ga wanda baka yi, ba wani abu ba ne”

“Mun gode Alhaji mun gode da Fahimta”

Alhaji Musa zai sake magana Appa ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu. Suka tashi suka fice cikin kunyar sakon da suka isar.

“Alhaji be kamata ka yi haka ba, taya zasu same ka har gida da wannan maganar?”

“Sun yi abun da ya dace Alhaji Musa, haka ake son iyayen na gari su kasance sun warware ne saboda su suka nema masa aure, to da ace anyi tsammanin shi zai aureta ko kuma mu ji shiru a kara tun wuri su sanar mana, kuma yana da gaskiyarsa babu namiji da zai son auren mace kamar Khairy saboda abubuwan da aka fada ta yi ma yar’uwarta ta jini, balle kuma ga maganar Fyade ta shigo ciki kuma ka san yadda society mu suke daukar abun da girma”

Cikin takaici da Allah wadai Alhaji Musa da ya kasance kane ga Alhaji Haruna ya ce.

“Ummu Khairy bata kyautawa kanta ba, bata kyauta ba ban jidadi ba ta bata maka suna ta lalata rayuwarta ina amfani haka”

“Idan ma akwai amfani a yanzu ta gani idan ma babu kuma ta gani, Allah ya shirya mana zuria”

“Amin, yaran ne yanzu hankalinsu da tunaninsu sai ka rasa ina yake zuwa, ita na Hurriya saboda bata aikata ba ne Allah ya dubeta ya kawo mata wannan yaron ban da haka ai da sun zame maka su biyu abun babu dadi”

“Ko su goma suka zama zan iya dauka Alhaji, yadda kaddara ta rubuta ai haka za a wanke a sha, Allah baya aje kayansa ga wanda ba zai iya dauka ba, jarabawa ce ta rayuwa Alhamdulillahi”

Appa ya fada cikin tsananin bakincikin da be isa ya boye a zuciyarsa kadai ba har sai da fuskarsa ta bayyana.

 

CAPTAIN JAMAL POV.

“Akwai wani abun da zan iya taimaka maka da shi ne?”

Captain ya girgiza kai ya kwanta jikin kujera kamar mai jin bachi.

“Aa anyi komai, daman ba wata hidima za’ayi ba, Ammy ta hana taron biki ta hana komai ka ga babu bukatar yin wani abu”

“Amman dazun ina jin ka a waya da Abdulkareem kake masa zancen gyaran gida”

Captain ya zaburo masa da fada ganin yana son matsa masa ya shigar masa hanci.

“Already ina da gidan a nan da Kaduna Salim ka sani, na hannata masa komai ne saboda yayi kwangilar kula da komai idan akwai abubuwa da za a canja ko a saka yayi saboda sabon gidaje ne, kai kuma ba sana’arka ba ce to miye abun takuwara dole sai ka shiga ciki?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected