Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Sannu da zuwa Hajiya, ai da ma baki zo ba, ga kafafuwa suna ciwo ni kaina idan na warware ai sai na zo na gaishe ki, kuma ai kin kira waya haka ma ya wadatar”
“Aa kara dai na zo, fatar na same ku lafiya”
“Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya ciwon kafafuwan yayi sauki?”
“Alhamdulillah”
Sama sama dai suka yi ta gaisawa Appa na zaune kusa da Hajiyarsa daga kasa, Hajiya Kaltume kuma na daga kan kujera ita da duka yaranta, Hurriya da Hamad ne kadai a kasa domin haka Amma ta koya musu idan babba yana kan gado ko kujera to su kuma su zauna a kasa, kar su zauna tare da shi ko kuma a yadda yake zaune. Da hira ta yi hira ne Hajiya Kaltume ta dauko zancen wahalar da suka sha a dajin tana fadar yadda aka rika mistreated dinsu kamar wasu dabbobi.
“Shiyasa ake son a samu soji masu kishin kasa da za su iya yakarsu idan ba haka ba, kasar nan da wahala ta gyaru domin Shugabannin ma sun zama sai a hankali”
Cewar Yasir. Cikin murmushi Hajiya Binta ta kalli Hamad ta ce.
“Da yardar Allah Hamad soja zai yi, wannan fushi da zuciyar ta soja ce”
Hamad ya girgiza kai.
“Aa ba soja nake so ba?”
Namra ta ce.
“To me kake so? Wannan zuciyar taka Hamad ai soja ya dace da kai”
“Aa ni Likitan idanu nake son zama, idan na kware zan yi ma Hurriya aiki ta, ita ma ta rika gani kamar kowa”
Tsit katon falon na Hajiya Kaltume yayi domin babu wanda ya za ci abun da zai fito daga bakin Hamad kenan. Hurriya ta yi murmushi tana masa kallo irin na so da kaunar dan’uwa, ita kanta ba yi zaton Hamad yana sonta kuma ya kula da damuwarta har haka ba.
“Come here my friend”
Yasir ya mika masa hannu, sai ya taso ya iso gurin Yasir din Yasir ya rumgume yana buga bayansa.
“Yayi kyau babban mutum”
Cikin jindadi da alfahari Appa ya kalli Hamad ya ce.
“Da yardar Allah da yardar Allah, Hamad ba zaka yi karatu a kasar nan ba, waje zan kai ka ka sha ilmin akan idanuwa har ka gaji, da ikon Allah wannan kudirin naka sai ya cika ko da bana raye”
Hajiya Kaltume da ta rasa abun da zata yi ta kalli Appa da murmushin dole.
“Za a karya dokar fitar da yara waje karatu kenan Alhaji akan Hamad?”
“In Shaa Allah, ba shi kadai ba Hurriya ma ba zata yi karatu a kasar nan ba, yadda take da kokarin nan waje ya kamata ta yi karatu, kuma ko ba ni ba Principal dinsu ya fada min suna sa ran da zarar ta gama secondary school zata samu scholarship mai kyau a manya kasasshe saboda kokarinta da yadda take cin gasa ta bangaren lissafi”
“Maa Sha Allahu, Allah ya nuna mana yara masu albarka Allahu akbar Allah dai yayi albar….ya bar zumunci”
Sai ta kasa karasa da Allah yayi albarka ta canja zuwa Allah ya bar zumunci, domin ta san hausawa sun ce addu’ar makiyi karɓaɓɓiya ce, ita ko ba zata so su yi albarka ba. Gashi abun da Appa ya fada cewar yaran Iyami za su karatu a waje ya daki zuciyarta mugun daka irin dakan da ace mashi ne, babu abun da zai hana ya bullo ta bayanta, yanayinta ma gaba daya sai ya sauya hankalinta yayi mugun tashi, ba dan ta yaki zuciyarta ba wata kila ma da ta rasa sukuninta har kowa ya gane halin da take ciki.
“Allah sarki dan’uwa mai kaunar yar’uwarsa, duk da fadan nan da kuke da rashin jituwa wannan soyayyar da kaunar tana nan a zuciyarsa, Allah ya kara hada kanku, ya shirya mana”
Kowa ya amsa addu’ar da Hajiya Binta ta yi da Ameen ban da Hajiya Kaltume da gume ma ya karye mata kamar wadda aka kwancewa zane a kasuwa. Daga bangaren Hajiya Kaltume Hajiya Binta ta fito ta shiga bangaren Momy suka gaisa sannan ta fito tana jin kewar Iyami. Sai addu’a take ma Appa idan dawowar Iyami alheri ce Allah ya daidaita tsakaninsu, ya kasa amsawa da ameen bayan kuma abun da yake nema kenan a zuciyarsa. Mota daya suka shiga Hurriya bayan ta dauko mayafinta, ita da Hajiya suka zauna a back seat, Appa da Hamad kuma suka shiga gaba, Appa yana jan motar suka fi daga gidan.
After mintuna goma da tafiyar Hajiya Binta, Momy ta fito tare da bakuwarta da kuma ɗanta da be ci komai ba a cikin abubuwan da Momy ta saka a shirya musu, Miwan na bayansu tare da dan’uwansa Musib sun yi ma bakuwar Momy da ďanta rakiya ban da Namra da har yanzu tana can bangaren Hajiya Kaltume.
“Captain ai yana yawan zuwa nan, duk lokacin da zai zo garin na ba ya tafiya sai ya shigo, ina jindadin haka Wallahi”
Hajiya Turai ta yi murmushi.
“Ai danki idan yana son mutum to ya huta, Allah ya hada jininku”
“Sosai kam, Allah dai ya nuna mana lokacin auren nan mu rakwashe”
Cewar Momy, Mutumen da aka ta maganar akansa be ce uffan ba ya fara sauko Entrance din hannu dafe a kirjinsa yana murza a hankali domin ba karamin zafi ya ji ba a lokacin da suka yi karo da Hurriya, taku daya biyu uku hudu yayi kamin ya ja ya tsaya yana kallon yadda tsaddadiyar motarsa ta yi ta kasa gaba daya, saboda tayun motar da aka succe duka hudu. Ya juyo ya kallesu.
“Waya taba motar nan?”
“Wace motar?”
Kusan a tare suka kalli motar Musib yayi sauri sauka ya karasa gurin motar da mamaki.
“Lafiya kalau kuka zo da ita?”
“Idan bata da lafiya zamu zo da ita ne? What kind of stupid question is this!”
“Subhanallahi, garin ya haka ta faru!”
Cewar Momy tana saukowa ta nufi gurin motar. Miwan ya ce
“Gaskiya wannan succe tayun aka yi”
“To waya aikata haka? Wannan dai rainin wayo ne da neman mutum yayi magana ace ya cika masifa”
Ya fada da karfi wani karin bacin dai na tunkarosa, cikin bakinciki ya sauka ta isa gurin motar. Momy ta kai hannu ta dafa karjikinsa.
“Kwantar da hankalinka Captain, a cikin yaran nan dai wani ba zai yi gigin yi maka haka ba, akwai dai matsalar da aka samu”
Momy na rufe Hajiya Turai ta miko masa hannu kamar wani karamin yaro dan yaye.
“Captain shigo ka zauna, sai mu shiga wata motar”
Ya sauke ajiyar zuciya tare da jan dagon numfashi ya fi sau goma, sannan ya shuri motar da kafarsa da karfi.
“Duk wanda yayi min haka da gangan yayi, saboda a bata min rai”
“Toh waye zai maka haka Captain? Dan Allah karka bata ranka, na gano, yanzu haka ba zai wuce bakar matar can ba Kaltume, domin na dade da lura da yar bakinciki ce ta karshe”
Momy tana maganar tana jin kamar ta yi tsalle taje ta shake wuyan Hajiya Kaltume.
“Oh kekam baki zaune cikin mutane kwarai Hajiya Nafisa, rayuwa a gidanku tana da wahala”
Momy ta amsawa Hajiya Turai tana kwafa.
“Barta na san yadda zan yi maganinta, da ni take zancen, Captain yi hakuri shigo ka huta sai ka dauki motata ku tafi da ita, idan an gyara wannan Musib zai kai maka ita gida”
Jameel ya juyo ya nufo hanyar falon, sai duk suka dugunzuma suka biyo bayansa, ban da Hajiya Turai da bata matsa daga inda take tsaye ba tun bayan da suka fito daga falon. Cikin natsuwa da kamala ya shiga falon, sai ka rantse ba shi ne ya gama bacin rai a waje ba, zaunawa yayi ya hade hannayensa ya sadda kai kasa ya rufe ido yana motsa bakinsa a hankali, kokari yake na ganin be bar bacin ransa ya ninku a zuciyarsa ba…
☆❁ ❁☆
Hello Habibaties
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy
https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy
1️⃣2️⃣
Musib ya aje ma Captain keys din motar Momy da ta bada umarnin a dauko masa. Kallon Keys din yayi sannan ya mika hannu ya dauka ya mike tsaye. Tsabar bacin rai zuciyarsa har zafi take kamar zata fashe, baya jin yana da sauran wata magana a yanzu kuma baya bukatar yi ma Momy sallama bayan an bata masa tayun mota a gidanta. Shi ya fara fita sannan mahaifiyarsa ta bi bayansa Momy da Musib suka biyo shi suna ba shi hakuri kamar su suka masa laifin shi dai be ce uffan ba ya matsa key hannunsa motar ta fita key ya sannan ya nufita har suka bar gidan kalma daya bata sake fitowa daga bakinsa. Ran Momy be yi dadi ba ganin ďan ďan’uwanta da take ji da shi ya fita cikin bacin rai.