Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Toh Allah yasa, da wacan Malamin ne da ya rasu da yanzu aiki ya fara amman su babu wani motsi har yanzu”
“Gaggawa aikin shaidan ne ki saka hakuri sa sannu zaki ga aiki yayi, kuma yanzu ma idan mun gama wayar nan zan sake shiryawa na tafi gurin Malam na gangare na sake masa bayani”
“To sai na ji ki Allah ya taimake mu”
“Amin”
Ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.
*** **** *****
Ya shafa fuskarta sannan ya tsika ci abarba ya kai mata a baki, daker ta dago daga kirjinsa ta bude baki ya saka mata.
“Tauna mana haba Baby, an fada min gida ma fa haka kike yi ba ki wani cin abinci, shiyasa ko kibar amarci da kowa yake yi ke baki yi ba, sai dai ni na yi”
“Daman ni bana wani cin abinci”
“Ai mantawa na yi na ce Amma ta roka mana ki rika cin abinci tun da Hajiya ta dawo balle na ce da ita”
Hurriya ta yi dariyarta mai kayatarwa.
“Har da cin abinci sai an roka”
Ya sumbance ta.
“Eh mana, yanzu ma ba mu yi latti ba, cikin week din nan za su dawo kamin su dawo zan fada musu su roka miki cin abinci”
“Daman na sha addu’a a gurin Kakata Hajiya Binta tun tana Saudi gurin Ummara har ta dawo addu’a take min, su Amma ma da suke can addu’ar suke ta mana Allah ya tsaremu ya bani lafiyar ido ya sa a yi aikin cikin nasara da sa’a.”
“Amin ka ji yar gata, ta ko’ina roka miki ake”
Ta dago kamar tana ganinsa.
“Allah yasa kamin mu tafi aikin nan su dawo”
Ya kai mata kiss a goshi.
“Da wahala gaskiya, mu da zamu tafi jibi su kuma sao karshen satin nan za su dawo ai”
Ta bata fuska.
“Ko ka daga har wani satin please”
Ya kwaikwayeta yana jan hancinta har ta turo baki gaba yadda ta yi.
“Ko ka daga har wani satin please”
Ta daga hannu zata dokeshi sai ya rike hannu ya matse har sai da ta yi kara sannan ya sake ta yana dariya.
“Ke ba ganin kike ba sai fitina, ka ji min mata haka kika fitini zuciyata kina dukan kirjina har sai da kika shige ciki…”
“Ba wani nan kai ne daga ganin yar yarinya kyakkyawa ka cusa kai har da wani ba ni chocolate da gilashi kana saka ni cin abinci dole a office dinka”
Ya zaro ido yana dariya.
“Ta nan kika bullo kuma”
Ta nauyi cikinsa.
“Yanzu duk sai na rama abun da ka yi min har da marina da kai yi”
Ta lalaba fuskarsa ta kai ma kumatunsa cizo har sai da yayi ihu ya rumgumeta yana dariya yana mata chakulkuli.
“Na daina… Na daina…”
Ta yi dariya sosai har da su dari.
“Ki biyani chocolate din da kika ci nawa, daman na rubuta duk abun da kashe miki ai ba dan Allah na yi ba”
“Ka fadi ko nawa ne, idan Saurayi Captain ya zo zai biyaka, amman fa soja ne kana yin wasa zai harbeka yana da fushi sosai”
Yayi dariya ya cigaba da tsakalar cikinta tana ihu da dariya a lokaci daya.
Two days later… Jirginsu ya tashi daga Abuja tafiyar awa hudu da mintuna 40 suka yi sannan suka sauka Addis Ababa babban birnin Ethiopia. A Oasis hotel apartment /Haya Hulet suka sauka Hotel ce mai kyau da aka wadata a abubuwan more rayuwa. Mama Rukayya da ta kasance yar rakiya daga bangaren Hurriya sa kuma Momy Ikilima daga bangaren Captain suka sauka a daki daya, Captain da matarsa kuma suka sauka a daki daya, sai wanda suka zo da shi domin hidima shi ma aka ba shi nasa dakin dabam. Kwana biyu a hotel din Hurriya na tafiya kwararrin likitocin da suke Bethel Hospital, addis Ababa, Landmark General Hospital, Medical center hayat hospital MCM suna duba idon, daga karshe dai aka yanke shawara yi mata aiki a Medical Center Hayat Hospital MCM, saboda kwarewar aikinsu da kuma kyakkyawar alakar dake tsakaminsu da wani na kusa da Hurriya.
Ana gobe za ayi mata aikin ta tsora sosai duk kuwa da irin karfafa guiwa da tabbacin da likitocin suka bata cewar za’ayi nasara. Har yanzu zuciyarta bata yarsa 100% idonta zai bude ta samu lafiya kamar kowa ba, ganin tun haihuwa take da ciwo har zuwa yanzu d ta girma.
“Baki yarda da ni ba? Baki yarda za’ayi nasara ba? Baki yarda Allah zai iya warkar dake ba? Baki yarda Allah ya karbi addu’ar da ake ta yi miki ba?”
Ta kwantar da kanta a kirjinsa.
“Na yarda, kawai ina tunanin idan ba ba ayi nasara ba, zan tabbata a haka ne har abada”
“Za’ayi nasara da yardar Allah”
Ya kwantar da ita kan gadon ya fara kissing din wuyanta, tana ta kokarin hana shi amman be saurara mata ba sai da ya raya daren kamar darensu na farko har tana masa kuka a yanzu din ma. Da asuba shi ya taimaka mata ta yi wanka suka yi sallah, ta hau gado da niyar bachi kamin lokacin zuwa asibitinsu yayi, a nan ma be bar Hurriya ta huta ba, sai da ya sake gajiyar da ita har tana masa miya. Misalin karfe daya na rana suka isa asibitin aka wuce da ita dakin da aka ware mata na musamman sannan aka fara yi mata wasu treatment din. Ba a shiga aikin da ita ba sai karfe bakwai na yamma. And the most expensive news is anyi aikin cikin nasara sai dai babu tabbacin ko zata gani daidai ko kuma irin na da ne ko ma idon be bude gaba daya ba sai idan ta bude idon, hakan kuma ba zai samu ba sai nan da sati idan idonta ya warke. Daga ranar da aka yi aikin suka saka mata dokokin na abun da zata ci ko ta sha da irin motsi ko aikin da zata yi. Sun bada damar mayar da ita gida ayi jinyarta kamin ranar da za a bude idon, sai dai Captain ya zabi ta zauna asibitin saboda ta fi samun kula kuma ya san a gida ko a Hotel din da suka sauka zata iya karya dokarsu.
A asibitin Hurriya ta yi jinyar idonta for one week, ranar da za a bude idon ba ita kadai ba har Captain da Rukayya da Iyayensu dake gida da fargaba suka wuni na tsoron rashin nasarar aikin. A hankali aka fara warware daurin dake idonta har aka cire, ita kanta ta ji alamar nasara a tare da aikin domin tana iya jin haske a idonta dake rufe tun kamin ta bude.
“Hurriya can you open your eyes please….”
Ta fara motsa ido da take jin kamar ya like mata. Wani likitan an ganin haka ya dauko wani magani ya diga mata a idon dake rufe.
“Open it slowly…”
Ta bude idon a hankali, sai dai bata iya daga shi sosai yayi mata kamar na masu shan kwaya (Irin na Ummu Falsak) sai dai tana iya ganin abun da yake gabanta da dishe dishe hakan kuma ya faranta ranta.
“Don’t let tears drop”
Ta yi kokarin hade kukanta bayan dayan likitan ya bukaci haka. Sai ta sake maida idon ta rufe sannan ta bude a hankali. Fuskar Captain ta fara cin karo da ita kamin ta bi sauran Likitocin hudu da suke dakin da kallo dukansu farar fata ne kamar kasa mijinta babu daya da ta sani.
“Alhamdulillah”
Captain ya fada yana durkusawa kasa yana kallonta tsabar farinciki.
“Congratulations”
Cewar Likitocin suna tabawa kansu kowa ne na gaisawa da dan’uwansa. Captain ya dago ya rumgume ta yana farinciki.
“Ina gani yanzu ina gani ina gani Alhamdulillah”
“Daman na fada miki za’ayi nasara gashi kuma anyi”
Hawaye ya sauko mata tason ta share tana tsoron saka hannu a gurin, blink din sa take da idonta ma ganin take kamar idan idon ya rufe ba zai bude ba. Captain ya sumbance ta a gaban Likitocin sannan ya sake ta ya juyo.
“Dukansu sun yi kokari gurin aikin nan Baby Aisha Alhamdulillah, wannan shi ne Dr Camil, sai a Dr Nille….”
Haka ya bi yana gabatar mata da Likitocin da suka yi nasarar yi mata aikin Maza uku mace daya tana musu godiya.
“Bayan su akwai wani matashin yaro mai karatun Optometrist.. Wato likitan ido who will perform medical and surgical treatment for eye condition, shi ma ya kamata a gode masa, domin tare da shi aka yi aikin a kokarinsa da yake na koyon aikin kuma duk saboda ke ne, ina da yakini Allah ba zai kunyata shi ba shiyasa na yarda 100% idonki zai bude Babyna kuma saboda shi Muka zabi yin aikin a wannan asibitin da yake karatu gashi kuma an yi nasara Alhamdulillah”