VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ayyah wai Malam? Malam ai yau kwanansa tara da kwanta dama, Malam ai lokaci yayi”

Hajiya Fatee ta dora hannunta akan tulun kirjinta ido a waje kamar za su yi magana.

“Malam kike nufin ya rasu?”

“Malam ya rasu lokaci yayi, gobara yayi cikin dare wutar ta ci shi ta cinye yaransa biyu kuma bata bar komai da yake gidan ba, amman sauran yaransa da matansa sun fita da rai suna nan lafiya kalau”

Hajiya Fatee ta kai zaune tana dafe da kirji.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, na shiga goma na lalace yau kashi na ya bushe, Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un Wayyo Allah na ni….”

Kuka da ambaton Allah da take ne ya saka Hajiya Kaltume shigowa, sai kuma ta shigo a sa’a, domin ta shigo ne a daidai lokacin da matar take kara radawa Hajiya Fatee cewar.

“Matansa sunan na yamma da mu kadan, a sabon gidansa suke takaba, ai Malam ya kowa ya ji mutuwarsa duk wanda ya zo nan kuma yake mana”

“Mutuwa? Malam din ne ya Mutu?”

Hajiya Kaltume ta amsa a razane da karfi tana kallon matar dake rike da tabarya tana surfe.

“Yau kwana tara kuwa, gobara aka yi a gidan, komai ya kone, zane wannan na daura sai da aka taimakawa matansa da shi a lokacin da lamarin ya faru”

“Shi nan na shiga uku, ni kam ta kare min…. Al’amurra sai kara rinchabe min suke…. Yanzu Malam be tashi tafiya ba sai da wahala ta tunkaro ni gaba da yamma, na shiga uku na lalace”

“Ba ke kika shiga uku ba Kaltume ni na shiga uku, wayyo Allah wayyo ni kaina”

“Sai hakuri haka mutane suke ta kuka idan suka zo, ai mutuwar Malam ta taba kowa musamman customers dinsa”

Hajiya Kaltume ma ta kai kasa ta zauna kusa da kawarta suna kuka kowa da dalilin kukansa kuma da abun da yake yi ma fargaba. Tun matar na ba su magana har ta gaji ta zuba musu ido, domin ko da matansa ne iyakar kuka da bakinciki da za su yi kenan.

“Ku yi hakuri bayin Allah mutuwa ai ta gaji haka shiyasa kullum ake son a shirya mata, Salmanu tashi ka kai su gidan matan Malam”

Ta fadawa babban ďanta, domin kukan da suke ya fara yi mata yawa har makota na lekowa ta katanga wasu kuma na shigo suna kallonsu. Hajiya Fatee ta mike tsaye rike da jakarka ta tana kuka, taku daya ta yi kamin ta yi na biyu wani hudun zuciya da ido ya rufeta ta saki jakar ta fado kan Hajiya Kaltume da ko alamar tashi bata yi ba, domin jikinta ya mutu kamar an mata allurar kasala.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un idan kika mutar min a yanzu ai sai abun ya taru yayi min yawa ku taimaka min jama’a”

Matan dake kofar gidan suka karasa shigowa suka rika Hajiya Fatee suka daga ta daga jikin Kaltume, suka shimfidata a kasa wasu suka fara mata fifita matar idan kuma ta tashi da gudunta ta debo ruwa aka kwarawa Hajiya Fatee. Sai gata ta farko tana hakki.

“Malam ya mutu, Malam me yasa ka mutu a yanzu? Asirin an tonu na shiga uku wayyo Allah, Malam ya mutu ya bar ni da wahala wayyo Allah na….”

Wani irin shidewa ta yi luuuuuuu jikinta ya sake saki, har sai da matan suka jin tsoron wannan suman nata na biyu, Hajiya Kaltume kuma tana zaune a gurin ta kasa aikata komai sai kuka take kamar ita kadai ta rasa Malam. Ruwan aka sake zuba mata sannan ta farfado tana kallon matan karkarrar dake juya mata tana jin sannun da suke mata kamar a mafarki, fada mata da matar ta yi cewar Malam ya rasu ma sai ta ji abun shi ma kamar mafarki ne ba gaske ba.

“Abun da zai fi akaisu gidan Matan Malam ko kuma a kaita asiri”

Wata daga cikin matan dake rike da ita ta fada, Hajiya Kaltume ta kalleta da jajayen idanuwanta ta ce.

“Ina ne gidan”

“Daga nan ne yamma kusa da kuka uku, Sslmanu wuce gaba ka kaisu”

Yaron da aka kira da Salmanu ya dauki tayarsa da karen kada tayar ya wuce gaba yana zumuncin nuna musu hanya, ganin mutanen daga birni suka zo. Ba dan taimakon Allah da rahmarsa ga bayinsa ba da Hajiya Kaltume bata kai kanta gurin motar da suka shigo ba, domin gaba daya kafafuwan rike mata suka yi, Hajiya Fatee kam sai da aka riko aka saka ta motar idonta sai juyawa yake kamar bata san inda take ba. Yaron ne ya wuce gaba da tayarda yana turawa su kuma suna cikin motar zaune a baya, Hajiya Kaltume ce kadai ke iya kuka a yanzu Hajiya Fatee kam kai kawai take juyawa kamar mai kokarin fita daga hayyacinta, direbansu na biye da su har suka isa katon gidan ginar bolu kana ganin gidan da ba’ayi ma filista ba ka san ba duk kauye ba, ko a kauna sai wanda ya tsaya da kafafuwansa.

“Wai yanzu da gaske Malam ya mutu Hajiya Kaltume? Shikenan Malam yayi tafiyar da babu dawowa? Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, shi ke nan ta kare min dari ta hade min da dubu, Wallahi ganin nake kamar ba gaske ko dai mafarki nake Kaltume?”

Hajiya Kaltume kam kaddara ta riga fata, bata iya cewa Hajiya Fatee komai a yanzu domin ita ma bata da wannan kwarin guiwar. Hajiya Fatee ta unkura zata fita ta kasa saboda jiki yayi nauyi a zaunen da take ma jiri ke debanta yana zubarwa.

“Dukiyata…. Cikin nan….. Ga Afrah… Indai Malam ya mutu a yanzu Malam be kyau min ba”

Direban motar ya juyo ya kalli Hajiya Fatee dake sabbatu tana wani mashalo kamar mashayiya. Cikin gidan Hajiya Kaltume ta shiga babu ko sallama sai tafiya take a gajiye, daga a tsakar gidan ta fadi zaune tana kallon matansa dake zaune da kayaransa.

“Daga tsohon gidanku muke aka fada Malam ya rasu, dan Allah ku ce mana ba gaskiya ba ne”

Karamar ta sauke kai kasa idonta na cika da kwalla, mai karfin halin ce fa amsawa Hajiya Kaltume.

“Malam kam rai yayi halinsa ya riga mu gidan gaskiya, sai dai mu bishi da addu’a, ba Malam kadai ba har da yara biyu”

Hajiya Kaltume ta rushe da kuka tana dora hannu akai tana ihu kamar zata tara musu mutane.

“Kashi na ya bushe a yau, ashe shiyasa komai yaki daidai, na zuba kudi ina duban Malam yana nan yana aiki ashe Malam yana barzahu, na kira waya shiru ashe babu Malam”

Matan suka taso suka rika Hajiya Kaltume suna kuka domin ta tsikaro musu bakincikin rasa mijinsu da suka yi. Hakuri suka rika bata sannan suka rikata suka zaunar da ita a ciki barandar gidan (Balcony) dayar ta debo mata fridge ta aje mata sannan ta zauna tana bata labarin abun da ya faru tana kuka.

“Kin ga gidan nan be dade da gama shi ba, ya saka komai a ciki tv da fridge irin na yan birni ya saka mana, kayan daki ma masu kyau ya zuba mana, na dubu 70k, duk kauyen nan sai labarin gidan nan yake ashe Allah be kaddara a koma tare da shi ba sai bayan ransa”

Hajiya Kaltume ta sharce kwalla ta girgiza kai tana kuka, kai ka ce kukan rashin Malam kawai take da gaske ba kukan neman mafitarta ba.

“Yaushe ya rasu?”

“Yau kwana tara, kuma mutuwarsa ta bawa kowa mamaki, shiyasa har wasu suke zargin ko jifansa aka yi, domin Malamai suna haka, idan aka ga ka taso ana yi da kai a gari sai hassada ta shiga ciki”

Dayar ta karba mata.

“Ai ba kama ba ce wannan abun jifa ce kawai, domin yana cikin aikinsa karfe daya na dare sai wuta ta fara kamawa a dakin, ihunsa kawai muka ji muka fito aka yi ta dukan kofar ta ki budewa sai da ta cinye shi tass, kuma wutar bata tsaya nan na haka ta bi gidan nan ta cinye komai har da yarana biyu iro da dan inna, zane wannan na daurawa ba mu fita da shi ba, sai da makota suka kawo mana Hijabai, bayan wutar ta cinye komai ta kama ginin gidan ta kone kamar watsa fetur, wannan abun ya bawa kowa mamaki bayan an yi masarar kashe wuta aka bude dakin wuta ta ci Malam abun babu kyau gani, haka ma aka saka shi ba tare da an yi masa wanka ba sallah akwai aka yi masa aka saka shi a rame, saboda jikin ya kone wanka ba zai yi ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected