Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Ya dauke idonsa daga barin kallon yaran ya kalli Hurriya dake tsaye a rikice.
“Hurriya zauna ki rarrashi yaran nan”
“Ba kuka suke yi ba”
Ya watsa mata wani kallo irin na karki bari na maimaita kaina. Ta koma ta zauna ta dafa su.
“Ku yi shiru ku yi hakuri ku yi shiru”
Tana yi tana kallonsa a ranta tana mamakin hikimarsa ta yin haka bayan yaran ba kuka suke ba cin abincin suke yi. Shi kuma ya nufi kitchen din gaba daya hayaki ya cika ko’ina, gurin da wutar take ya nufa electric kettle din Momy ce ta kama da wuta, haka ya lalaba ya kai hannunsa ya taba socket din da niyar kashewa sai ya ji a kashe, hakan yana nufin wutar ma a kashe take amman a haka sai da ya kama da wuta. Abubuwa yayi ta budewa har ya samo mociya ya dauko ya bugawa kettle din ta zubo da ita kasa amman wutar bata daina ci a jikin butar ba. Tab ya kunna ya rika watsa ruwa a banza, da gudu ya fito daga kitchen din yana tare.
“Baka yi komai ba, Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, bari a kira fire service”
Momy ta fada hankalinta a tashe.
“Baku da fire-extinguisher a nan ne?”
“Akwai yana nan ta baya”
Momy ta wuce gaba da gudu kai kace ta kwashe kibar ne ta watsar, ta nuna masa gurin ya dauko ya dawo kitchen din ya fesa, amman wutar taki mutuwa, sai ya sake fita ya samo bargo ya jika shi da ruwa ya lulluba saman wutar, tana mutuwa wata ta kama jikim gas a nan fa hankalin Captain ya tashi ya san gas ba shi da wasa. Ya fito da sauri daga kitchen already Momy ta yi waya a kawo fire service, masu aikin Momy da duk sun shigo falon suna kallon wutar har da masu aikim gida, wasu suka fara zuba ruwa a gas.
“Nono ku daina zuba ruwa, wacan ma dan na sauke ta kasa ne ya sa na zuba ruwa”
Ya hana masu zuba ruwan sannan ya kalli Hurriya.
“Ya sunan wannan?”
“Little Hamad”
Ya kama hannunsa.
“Zo muje mu kashe wuta”
Hurriya na jin haka ta yi hanzarin riko kanenta tana shi bayanta.
“Karamin yaro ba zai iya kashe wuta ba”
“Zan mareki Hurriya, idan ba su suka kashe wutar nan ba ba zata mutu ba, saboda an bata musu rai ne duk silar abun”
Ya nufeta yana matsawa baya ya riko Little Hamad din ya dagashi sama yana masa wasa domin ya san ba zai iya sakawa su yi da karfi ba. Ya nufi kitchen da shi daga bakin kofar ya tsaya ya bashi fire-extinguisher din suka rika su biyu suka hura iskar zuwa inda wutar take amman bata mutu ba, ya dawo da shi ya dauki Hamid yayi masa kwatankwacin yadda yayi ma Little Hamad, sai a ga wutar ta mutu a take kamar an taketa. Captain yayi murmushi mai sauti ya sumbance shi a kumatu.
“That’s my boy”
Ya aje abun ya juyo ya fito da shi falon yana dagashi sama ya jefa ya cha, yaron sai dariya yake sosai, dayan ma ya zo da gudu ayi masa daman ko a gidan Amma haka suke idan aka yi daya abu sai an yi ma daya, idan ba haka ba babu zaman lafiya, ga su so friendly da kowa basa bakunta kuma basa fasa kiriniya a ko’ina.
“Wutar ta mutu kuwa ikon Allah”
Momy ta fada tana leka Kitchen din, bayan Captain ya aje su ya dubi Momy.
“Ba dole ba, wannan shi ne me wutar wacan kuma ina jin shi ne mai kunamar, ko kuma duka Hamid din ne”
“To akan me? Ina mafari ina dalili? Daga zuwa bakunta sai su haddasawa mutane gobara da kunamu? Na ga kunama ni ma daya a dakina ta shige under bed na fito na fada kenan na zo na tararda wuta”
Captain yayi saurin girgiza mata kai.
“Momy karki ja su kara yin abun da ya fi wannan, ba a bata musu rai, ina tunanin ko dai kin musu fada ko kuma taba Hurriya da kuka yi ne ransu ya bace, Ke ma idan kina son zaman lafiya ki ba su hakuri”
Ya karasa yana magana da Namra da ke zaune a kasa tana rusar kuka har lokacin tana lalaba bayanta, gaba daya ta cire zip din rigar amman zabin da take ji sai take jin kamar kunamar tana nan bayanta, tun da ta zo duniya kunama bata taba cizonta ba, sai yau.
“Ya zan yi na ba su hakuri ya ake bada hakuri, dan Allah ku yi hakuri ku yafe min…”
Tana kuka tana rokonsa har da hade hannayenta guri daya. Hurriya bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba sai ta yi saurin rufe bakinta ta juya baya. Kowa sai da ya kalleta Momy ta yi kamar ta yi mata fada saboda ta yi dariyar Namra, sai kuma ta tuna ta kalli twins din ta shanye maganarta. Captain ya sauke kansa kasa a hankali yana murmushi dariyarta is something else da ya daukeshi ya jefa shi wata duniyar ta nishadi, sautin giggles laugh dinta na ta maimaita kansa a kunnunsa.
“Shatu shiga ki dauko mata hijab dinta mu tafi asibiti”
Momy ta fada cikin bacin rai, ba dan tana gudun ran yaran ya kara baci wata Matsalar ta sake afkuwa ba da sai ta yi ma yaran duka kuma ta ci uban Hurriya saboda dariyar da ta yi. Tare da Shatu suka haura sama ita ta shiga dakinta ta dauko keys din mota Shatu kuma ta dauko Hijab din Namra, Momy ta sauka Shatu ta saka ma Namra Hijab din ta rikata ta mike tsaye tana kuka. Momy ta yi zaton Captain zai ce ya kai Namra Asibitin amman be yi wani unkurin ba har direbanta ya shigo ya karbi keys din suka fice. Inna Kulu da Shatu ma suka fice daga falon, aka bar Hurriya daga ita sai kanenta da Captain. Sai a lokacin Hurriya ta samu natsuwar kwashe abincin da twins suka zubar ta zuba a plate ta dauke komai ta nufi kitchen tana aje plate din ta kunna tap ta wanke hannunta, sai ta ji magana a bayanta.
“Kin iya dariyar keta ko?”
Me zata yi idan ba dariyar ba, ta sake kyalkyalewa da dariya irin dariyar nan da baka iya controlling, idan ta tuna yadda Namra ta yi a dazun sai ta kasa rike kanta, ta juyo tana fadar
“I wish ni ma twins ce da an bata min rai… ”
Ta kasa karasa a yayinda ta kalli fuskarsa, tunawa da shi din ba abokin hirarta ba ne kuma ba yayanta ba, hasalima bata da wata alaka da shi, sai dai kuma murmushin da ta yi arba da shi a fuskarsa ya saka ta dan ji sakewa fiye da yadda take ji idan ta kalleshi a baya.
‘I’m your twinned, duk wanda ya taba ki, will see my reaction Immediately, trust me Hurriya i hear the whole story, i know the pain behind this precious smile of yours’
Magana yake daga zuciyarsa zuwa ga Hurriya dake tsaye gabansa yayin da yake rike da murfin fridge.
“Zaki iya haihuwar twins ai, yawanci gadonsu ake, idan kika yi aure zaki iya haifawa mijinki twins ko Tripple, i love twins too”
Ta kara fadada light smile dake fuskarsa kamin ta sauke kanta kasa ta fice daga kitchen din, ba tare da ta sake cewa komai ba. Ya dan daga girarsa kadan ya kai hannunsa ya dauko lemun kwalba ya bude sannan ya rufe fridge din, ya dawo bakin kofar kitchen din ya tsaya shi baya cikin falon shi baya cikin kitchen din ya jingina yana kallon Hurriya dake haurawa stairs tare da twins dinta gwanin sha’awa. Sai da ta haye gaba daya sannan ta juyo ta kalli kofar kitchen din, daman jikinta ya raya mata akwai idon wani a akanta, lemun dake hannunsa ya daga mata yana murmushi, ita ma ta yi murmushi kadan sannan ta dauke kai ta karasa saman ta isa bakin kofar dakinta, ta nan kam baya iya hangota ita ma bata iya ganin wanda ke falon. Dakinta ta tura sai da yaran suka shiga sannan ta shiga ta rufe kofar, kan gadonta dayan ya fada, dayan kuma ya nufi gurin da madubinta yake ya fara yi mata tabe tabe.
“Hamid bari mana, zo ga chocolate”
Ta dauko ragowar chocolate dinta ta mikawa musu. Ko da su Momy suka dawo Captain ya bar gidan, a daren Namra bata yarda ta kwana dakinta ba dakin Momy ta kwana saboda tsoro, washe gari da safe Momy ta kira masu kula da fulawa suka bincike dakin na Namra babu kunama babu alamarta, dakin Momy ma da aka daga gadon ba a ga komai ba.