Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
Ta daga kanta ta kalli gurin da take kyautata zaton fuskar Appa take, bata iya ganin komai saboda rashin masoya biyu, wato idanuwa, amman a haka zuciyarta take ayyana mata yadda fuskar mahaifinta take. Bata ganin komai sai duhu, sai dai makanta bata hana idanuwanta suke zubar da hawayen da tun da Appa ya fara magana suke mata zuba. Appa ya dauki sarkar dake gaban Hajiya Binta ya dora a cinyoyin Hurriya.
“Wannan sadakinki ne… An umarci iyaye su bawa yarinya sadakinta domin nata ne… Wannan naki ne Hurriya…”
Hurriya ta kasa cewa komai bata jin komai sai _A yau na aurar da ke Hurriya_ haka kalmar ta yi ta maimaita kanta a kunnenta kwakwalwarta na juya kalamin.
“Aure….”
Amma ta tambaya domin Mamaki ya hana Gwaggo cewa komai.
“Hajiya ban fahimta ba, wane irin aure kuma? ”
“Ki kwantar da hankalinki zaki fahimta”
“Ban gane na kwantar da hankalina ba, taya zai shigo cikin gidanmu kai tsaye ya fada mana ya aurar da Hurriya? Saboda ya mayar da mu talakawa? Ni ba ni da hakki akan Hurriya kenan? Wane irin magana ne wannan?”
“Kin fini hakki akanta Iyami, Annabi ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci Uba… Ban aurar da ita yau saboda na wulakanta ki ba, ban aikata hakan da wata manufa ba sai dan ina ganin hakan ne abun da ya cancanci ko wane uba na gari aikata, na aurar da ita ne a inda nake kyautata zaton za mutunta a rike ta amana, Iyami ki yi hakuri tabbas na yi kuskure ban nemi shawararki ba na aurar da Hurriya”
“Wa ka aurawa ita? Saboda abun kunyar da ya faru ne ka yanke shawarar aikata haka?”
Gwaggo ta tambaya a fusace. Appa ya tausasa murya ya ce.
“Aa Wallahi su suka zo neman aurenta da kansu, sunan yaron Jamal da ne ga Nafisa, dan wajen Alhaji Aliyu Turaki…”
Hawaye ya subucewa Amma.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, me ya sa zaka aurar min da ya a inda ba a san darajar mutane ba? Macen da bata son hada hanya da talaka? Zaka dauki Hurriya ka jefa a cikin danginta? Yarinya karama ta kafa fuskantar irin bala’in da na fuskanta a gidanka, da na san haka rayuwa zata zama gaba daya Wallahi da ban aureka ba, amman kaddara ta yi min zanen da ban isa na goge ba”
“Subhanallahi Subhanallahi Subhanallahi”
Appa ya maimaita har sau uku sannan ya ce.
“Na san ban kyauta miki ba Iyami, amman ki tausasa ko dan yaran nan”
Amma ta masa wani kallo na takaici da bakinciki.
“Yara? Wadannan twins din da aka haifa ka kasa zuwa ka tara hannu ka karba? Ko kuma ďan da aka kama ka ce ba zaka bada kudin fansar sa ba! Sai da na hada komai da na mallaka na bada, sannan Hajiya Kaltume ta baka umarnin biya? Ko kuma Hurriyar da ka juyawa baya?”
Appa ya kasa amsawa ya sauke kansa kasa yana mai jin kunya da nauyin abun da ya aikata.
“Bari na fada maka da bakina ka ji, yata bata auru ba, ba zan bada ita a inda za a wulakanta ta ba, abun kunyar da aka yi mata kazafin aikatawa ni zan iya rumgumarsa”
Ba tare da Appa ya dago kai ba ya ce.
“Iyami karki furta kalami cikin fushi”
“Irin kalamin da ka furta a lokacin da na ke cikin gidanka da cikin yayanka? Irin zuwan da iyayena suka yi ka wulakanta su? Yata ba zata je ko’ina ba Haruna…. Ban amince da wannan auren ba…”
Hajiya Binta ta ce.
“Adai hakuri Iyami a daina tuna baya, a bar baya ta wuce”
“Haka ne Hajiya, da dan yaran nan ba da be isa ya shigo cikin gidan nan ya zauna a nan yana magana da ni ba”
Appa ya share hawayen da suke masa zuba.
“Na cancanci tozarci da wulakanci da rashin mutunci a gurinki Iyami, ban kyauta ba na sani, kuma na karbi hakan”
Ya kalli Hurriya dake amayar da ruwan hawaye ya ce.
“Ba zaki ce komai ba Hurriya? Wata kila ban kyauta miki ba, domin ban tsaya na ji ra’ayinki ba”
Hurriya ta mika hannayenta ta kama hannayen mahaifinta ta rike.
“Hakika kai uba ne na gari Appa, ba zaka aurar da ni a inda kake tunanin zan wahala ba, ba zaka aurar da ni a inda za a musguna min ba, ko da ban gani a aikace ba na san a cikin zuciyarka haka ne, Appa ko kare ka aura min a matsayin miji, Wallahi zan karbe shi na zauna da shi, balle kuma mutumen da kake kyautatawa zato, na gode da zabin da ka yi min. Ya Allah mahaifina na ciyar da ni da halak, Allah ka ciyar da shi da abinci da ya fi ko wane abinci dadi a aljanna, mahaifina ya shayar da ni da halak, Ya Allah ka shayar da shi da ruwan alkausara, ruwan da bayan su babu sauran ƙishi bayan shansu, Mahaifina ya tufatar da ni da ni da Halak, Ya Allah ya tufatar da shi da mafi kololuwar darajar tufafi a aljanna, Mahaifina ya sama min muhalli, Ya Allah ka yi masa muhalli kusa da Annabi Muhammad S A W, Ya Allah ka shaida a yau mahaifina ya sauke nauyi na zaba min mutumen da yake ganin ya dace da ni, Ya Allah ka sauke masa nauyin zunubai, a saka a aljanna a saukake”
“Ameen, Allah ya miki albarka Hurriya”
Appa ya amsa yana kuka, sannan ya kalli Amma ya ce.
“Iyami na gode da kika haifa min ƴa mai tarbiya da sanin ya kamata a kananan shekarunta, wannan ma kadai abun alfahari ne a gurin, ku yafe min a inda na yi ba daidai ba, na barku lafiya”
Ya mike tsaye ya saka talkaminsa ya nufi kofar fita daga tsakar gidan, sai ga yaransa yan tawaye sun shigo sanye da uniform din makaranta rike da lunch box, suna ganinsa sai suka yi gurinsa suna murna kamar sun saba da shi.
“Appa…Appa…. Appa…”
Durkusawa yayi yana shafa kansu a madadin ya amsa sai ya fashe da kuka kamar ba shi ba. Yasir mai ya sauke kansa kasa yana hawaye, Gwaggo ma hawayen take ita da Hindu, Rukayya kuma ta koma kusa da Hurriya ta zauna ta rungume suna kuka. Cikin karfin hali Appa ya mike tsaye ya kama hannun yaransa ya fice daga gidan, Yasir ya share hawayensa ya kalli Amma.
“Amma…”
Sai ta daga mishi hannu tana hawaye.
“Dan Allah tashi ka bi mahaifinka”
Ya mike tsaye ya kalli kakarsa.
“Hajiya tashi mu tafi”
Hajiya ta yi murmushi.
“Zan tafi Iyami amman zan dawo idan kin huce”
Sannan ta mike tsaye suka fice tare da Yasir. Amma ta share hawayenta ta kalli Hurriya dake kuka ta ce.
“Shikenan abun da zaki fadawa mahaifinki? Kin goyi bayan auren da yayi miki? Kin san wacece Nafisa, kin kuwa san irin zabin da Alhaji yayi miki?”
Hurriya ta dago daga jikin Rukayya ta ce.
“Amma, mata da yawa iri na ba su san ubansu ba, saboda uban ya mutu a lokacin da suke ciki ko suke da kurciya, da yawa iyayensu ba su ga ranar aurensu ba saboda mutuwa ta yi katanga, suna da yawa wadanda iyayensu ba su samu damar zaba musu miji ba, wasu kuma an fasa aurensu, saboda ba a san ubansu…. Shim ni a gareni, wannan na gata ba ne?”
Amma ta kasa amsawa. Cikin kuka Hurriya ta cigaba.
“Amma…, baka sanin muhimmanci uba sai ranar da ka rasa shi, uba yana da ƙima, shi uban bango ne majingina ko wace ƴa. Idan kana son ka san darajar uba tambaye maraya, idan kana son sanin tsadar uba da halin da ƴa mace take shiga idan bata da shi, tambayi Ƴar da aka haifa ta hanyar zina…”
Ta saka hannunta tana share hawayen da suka ki tsaya mata
“Ni dai kam na sani, dukan abun da zai zo daga gurin Ubangijina mai kyau ne, dan haka zan tara hannu biyu na karba, ko da ba zai min dadi a yanzu ba, zai zama daraja ce da nasara a gaba, shi dan’adam ba ya kauce kaddara, kaddara bata wuce bawa, wannan ma daga gurin Allah ne….”
Amma ta girgiza kai tana kuka.
“Aa Hurriya ban yarda da wannan auren ba, ba zaki je ki sha wahalar da na sha a gidan ubanki ba, na yi irin wannan wautar na ki a lokacin da nake da kurciya kamar ke, amman yanzu me ya haifar min?”