VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Hurriya ta daga ta kai bakinta tana sha.

“Ke ba fa Nonon zaki shanye haka nan shi kadai ba, sai da magani”

Hurriya ta saka dariya.

“Na sani ai Hajiya”

“Toh na san halinki fa, kar na tambaye ki ce kin manta ba ki sha ba, baki san nawa na biya aka karbo min maganin tsarin nan ba, kuma ta tabbatar min idai Malami zai zauna a kan ruwa be nutse ba, to sannan zai miki aiki ya kamaki, shi ma Tsoho sake na yi ban kula da ba shi irin wannan ba, shi kuma be kula da addu’a ba, ai ko ba dan abokan kasuwanci ya kamata ya nemawa kansa gambun karfe, amman be kula da ko daya ba, wata kila da duk wannan abubuwan ba su faru ba”

“Kaddara ta riga fata Hajiya, haka Allah ya tsara”

“Haka ne”

Hajiya ta amsa sannan ta sauke ajiyar zuciya.

“Ina saka ran zuwa Umara ma wannan wata, da na ce zan daga sai wata na gaba amman ina son tafiyar a yanzu, ko dan na yi muku addu’a, a zan zan roko miki na gari”

Ta karashe maganar tana jan kumatun Hurriya, Hurriya ta yi murmushi mai sauki.

“Allah ya kaiki lafiya Hajiya, ya karbi ibada, Hajiya karki manta da Amma”

“Ina zan manta da ita kuwa? Zan mata addu’a kuma zata samu sauki da yardar Allah”

“Allah ya sa Hajiya, Hajiya tashi mu tafi falo kar Momy tace kin shigo nan kin zauna”

“Hurriya”

Hajiya ta kirata, sai ta amsa ta dago ta kalleta.

“Ummm”

“Nafisa matar ďana ce, ba uwata ba, ni nake a matsayin uwa a gareta, kuma na shigo gidan nan ne saboda ke, ba saboda matar da bata dauke ni a matsayin uwa ba, matar da bata san ta taka gidana ba sai idan wani abun ya faru, shiyasa da na shigo na cewa mai aikin ta nuna min dakinki kai tsaye”

“Haka ne, amman dai tashi mua tafi falo Hajiya”

Ita tsoron take ace ta saka Hajiya Binta a daki ta kulla mata munafurci na gaskiya da karya. Closet ta nufa ta dauko doguwar riga ta zuba ta dauki dankwali ta daura, sannan ta dawo gurin gadon ta kama hannun Hajiya alamar tana son ta tashi su tafi. Murmushi kawai Hajiya Binta ta yi ta mike tsaye domin ta san babba baya biyewa yaro ayi ta jayayya balle kuma Hurriya da bata son musu. Suna fara sauko stairs din Momy da Namra suka dago suna kallonsa a takr Hurriya ta ji wani iri ta kasa daga ido ta kalli kowa har suka sauka.

“Hajiya sannu da zuwa”

Momy ta fada dan babu yadda ta iya, if not ba zata gaishe da surukarta ba saboda bata zauna a falon ba, bata jira an kira mata kowa ba ta shige dakin Hurriya.

“Sannu da gida Nafisa, ya yaran?”

“Lafiya Kalau, ya tsufa”

“Gashi nan muna ja”

Namra ta gaisheta cikin muryar da ke nuna an mata dole.

“Hajiya ina wuni”

“Lafiya Kalau”

Ta amsa sannan ta zauna. Namra ta tashi ta shiga Kitchen ta dauko mata lemu da ruwa da dan abun tabawa ta aje mata. Ruwan kawai Hajiya ta sha shi ma dan kar Momy ta ce bata sha komai na ta ba. Bata wuce minti talatin a falon ba ta ce zata tafi.

“Da wuri haka Hajiya, na dauka nan zaki wuni, na ga idan kin zo har yamma kike kaiwa”

“Irin wacan tafiyar kai tsaye daga gida nake fitowa zuwa nan, amman ta yau daga wani gurin an fito sai na biyo nan na duba ku”

Duk suka mike tsaye ganin Hajiyar na ta mike tsaye.

“Allah ya saka da alheri mun gode ai a haka ma, bari na kira Alhaji a waya ina jin be san da zuwanki ba”

“Aa ba bukata na fada miki ba zuwan da na saba ba ne, ko bangaren Kaltume ma ba zan biya ba, sai dai wani lokacin”

Ta kalli Namra
“Namra an kammala karatu kuma sai mu ji shiru”

“Sauran Service, mun kusa zuwa”

“Aure nake magana, ga Khairiyyah ana ta maganar duk dai be turo ba amman ke mun ji shiru”

“Ni ma ina kusa Hajiya”

“Toh Allah ya nuna mana, kuna da labarin Musib da Miwan”

Wannan karon Momy ce ta amsa mata da kanta.

“Eh muna waya da su, suna kusan dawowa shi dayan ya gama nasa karatun ma, dayan ne ya rage”

“Allah ya taimaka ya sa a ci amfani”

“Amin”

Ta wuce gaba suna mata Allah ya tsare hanya, Hurriya ta biyota har gurin motarta ta direba ke ja ya kai ta duk inda take son zuwa. Kamin ta shiga motar ta juyo ta kalli Hurriya

“Karki yi wasa da abun da na kawo miki, kuma ki cigaba da hakuri Allah ya miki albarka”

“Amin Hajiya, na gode”

Ta shiga motar Hurriya ta rufe mata motar tana daga mata hannu har suka fice, sai da ta juyo zata shigo falon sannan gabanta ya fadi.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un”

Ta furta domin faduwar gaba ne da bata saba jin irinsa ba, kuma na zata iya fadar dalilinta na faduwar gaban ba, sai da ta ja dogon Numfashi ta sauke sannan ta shiga falon, kallo daya ta yi ma Momy da Namra ta maida kanta kasa bata sake kallonsu ba har ta haye sama ta shige dakinta.
Namra taja tsaki tana wani hura hanci.

“Gaba daya yarinyar nan ta fita raina, Allah kadai ya san me ta fadawa Hajiya yanzu kin ga tana zuwa bata ko tsaya an kiraki ba ta shige dakinta, ta sauko tana min maganar yaushe zan yi aure wata kila ta fada mata karyar ina mata wani abun shiyasa har take tambayar yaushe zan yi aure”

Momy ta tabe baki.

“Komai zata yi, su je su yi ta yi, gida ne dai ba a isa a kore ni ba, ni har wata magana na ji a gurin Hajiya Mardiya”

“Wace Hajiya Mardiya?”

“Matar Alhaji Shamsu dan masanin tsafe, wai Alhaji zai hada shi da Kaltume tana son ya fara sana’ar crude oil”

Namra ta daki kirji.

“What? Hajiyar?”

“Ita fa, ni ma nace ko dai ba ita ba tace min ita ce fa, wai har sun fara maganar ma, ita ma mijinta ne ya fada mata”

Dariya ta subucewa Namra irin dariyar nan dake dauke da mamaki.

“Hajiya so take sai ta take ki Momy, saboda yanzu daga ke sai ita yanzu, Amma bata nan ganin take kishi ya koma tsakaninku”

“Ai ba zai daure ba, ni fa ina da degree a fannin kasuwanci, ita kuma ko primary bata yi ba, kin tana ganin mace da irin wannan kuma tace zata fi ni? Sannan ni arziki na na ubana ne da na gada da kuma nawa da na nema tun yana da rai har bayan ransa, ita kuma yar talakawa ce kamar Iyami, duk arzikin da zata samu ba zai kaiwa ba, domin ita zata samu ne ta karkashin Alhaji ni fa? Kuma kin ga karatun da na Musib ya tafi yi a waje saboda na saka shi cikin ragamar kasuwancina ne, domin idan mu ne yau gobe ba mu ba ne, ita kuma yanzu zata fara kuma dan ta be sha’awar kasuwanci, dana kuma yana da gogewar hakan”

“Ita ma Hajiya ina zata iya da kasuwancin Crude oil? Tana mace kuma ita da bata yi karatu ba?”

“Ai a duniya yanzu babu kasuwanci dake saurin kawo kudi kamar crude oil shiyasa take son ta fara, amman ina nan dake sai ta koma ko abun da zata daura ya gagareta, ai Iyami ma yanzu ishara ce agareta, ciwon na kwantar da ita ta rasa komai daman can da Alhaji ake tutiya yanzu kuma ba a tare, shiyasa rayuwar talauci bata yi ba Wallahi, ke yanzu kina ganin idan ace Iyami wata shegiyar attajira ce a gidan nan akwai wanda ya isa ya wulakanta mata ya? Kuma kin ga wannan abun da mahaifiyarta akatau a duk lokacin da na kalli yarinyar can ko uwarta na tuna da wannan sai kimarsu ta kara raguwa a idona..”

Bata kai zaren zancen ba ta yanke saboda kukan wayarta ta ji, ta juya ta dauki wayarta dake gefe tana ringing, ganin number da ta yi appearing a gaban gilashin wayar ya saka ta yi murmushi

“Captain”

Ta yi shiru still tana murmushi kamin ta sake fadar.

“Alhamdulillah, Okay maybe ta jefa wayar wani gurin ne”

Cire wayar ta yi a kunneta ta mikawa Namra.

“Karbi Captain yana son magana dake”

Namra ta mika hannu ta kara ta kara wayar a kunnenta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected