VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Ina son na tafi gida ina son na ga iyayena idan suna raye…”

“Hakan ba zai yiyu ba, sai an dauki permission daga makarantarka hakan kuma ba zai yiyu ba sai da hujja, dole ka kwantar da hankali kamin mu yi tunanin abun da zai fi”

“Ba zan kwantar da hankali ba, 8na bukatar ganin Amma, babu ruwanka da rayuwata you lie to me azzalumi kawai, ka kira min Amma zan yi magana da ita”

Captain ya daka masa tsawa a karo na biyu.

“Ba zaka bar garin nan ba sai da izini, kuma ba zan kirata ba…! And control yourself Hamad na hadeye ka a zuciya Wallahi”

Yadda Hamad din yake ta fada ya kara tabbatarwa da Hurriya lallai dan’uwanta sai dai akwai abun da ita da shi ba su sani ba, waya kawo shi a garin nan? Meya saka ce ya mutu? Ta ya ya hadu da Captain? Kuma me yasa Captain ya boye mata gskiyar har zuwa yau? Ta dago kai ta kalleshi tana jin idonta yana wani dauri kamar zai like.

“Kira min Amma…”

“Toh zan kirata, amman yanzu ki min hakuri mu tafi masaukinmu kim ga Mama Rukayya da Momy Ikilima ma suna waje suna jiranmu! Sai mu magana a masauki zai fi kin ji”

Magana yake mata ta siffar rarashi yana shafa gashinta, sai ta girgiza masa kai ta lake kafadarta daya.

“Aa dan Allah ka kira Amma”

“Okay”

Ya ciro wayarsa ya danna number surukarsa ya aikata mata da kira. Wayar bata dade tana ringing ba Amma ta dauka tana sallama sai da ya amsa sallamar ya gaisa da ita sannan ya mikawa Hurriya wayar. Hurriya ta karba tana kuka

“Hello Amma…”

Hamad yayi saurin kara kunnensa a jikin wayar yana sauraren muryar mahaifiyarsa sai ya fashe da kuka.

“Lafiya Hurriya idon be bude bane?”

“Amma wata gaskiya zan fada miki mai kama da karya, Amma Hamad ne yana raye yana tsaye a gefena yanzu na yi magana da shi kuka ma yake yi Amma Hamad dinki yana raye…”

Amma ta yi shiru for some seconds sannan ta amsa.

“To ba Jamal wayar…”

“Amma baki yarda da ni ba?”

“Na yarda ba shi wayar..”

Hurriya ta mikawa Captain wayar sai Hamad yayi karaf ya karbe ya kara a kunnensa.

“Amma… Amma.. Amma…”

Nan ma Amma bata ce komai ba, domin ba muryar Captain ta ji ba, kuma ba muryar wanda ta sani ba ne, sai dai hankalinta ya tashi sosai tana jin kamar yarta ta samu matsala ne.

“Amma ki ce wani abu dan Allah Hamad ne…”

“Ba Hamad ba dai…. Ko waye kai dan Allah ka bawa Jamal wayar…”

Hamad ya dauke wayar a kunnesa ya mikawa Captain sannan ya nufi kofa zai fice hawaye na sauko masa, Hurriya ta yi saurin sakowa daga kan gadon tana kiranshi.

“Dan Allah karka tafi, dan Allah karka tafi Hamad inda da gaske kai din ne karka tafi dan Allah…”

“Jamal matarka bata da lafiya ne?”

Amma ta tambaya Captain ya sauke ajiyar zuciya.

“Lafiyarta kalau, kuma an yi aikin idon ya bude Alhamdulillah an yi nasara”

“To me yasa take min zan cen Hamad? Ko idonta ya fara ganin fatalwa ne yanzu kuma…”

“Da gaske ne Amma Hamad yana raye, akwai abun da baku sani ba, akwai abun da na boye muku sai a yanxu nake jin lokaci yayi da ya kamata ku san komai…”

“Kai ma baka da hankali ko Jamal? Dana Hamad ya dade da rasuwa…”

“Be rasu ba Amma Hamad yana raye….”

Ta katse wayar ji take kamar wasa suke son yi da hankalinta ko kuma dukansu ba su da lafiya ko kuma dai yana biyewa matarsa ne wata kila ta tabu.

“Ka ga abun da ka janyo ko? Ka kashe kowa a gurina kuma ka kashe a gurinsu…”

“Ban kasheka a gurinsu ba, ba ni na yi wannan ba step mother dinka ce ka tuna wannan? Ban fadawa kowa kana raye ko a mace ba, amman kai na fada maka suna a mace ne saboda ka rayu…”

Captain na kai aya kiran Appa ya shigo wayar Captain cikin girmamawa da mutuntawa ya amsa kiran.

“Lafiya kalau ya matarka?”

“Alhamdulillah an yi aiki cikin nasara Appa ido ya bude…”

“Alhamdulillah maa sha Allah ina take bata wayar..”

A madadin ta karba sai Hamad ya sake karbewa.

“Appa…”

Appa yayi shiru kamin ya amsa.

“Na’am waye wannan…”

“Hamad ne Appa Hamad ne…”

“Hamad na mu?”

“Eh Wallahi ni ne Appa wallahi ni ne ba fatalwa ba ne ban mutu ba”

“Me ka fada min na yarda kai ne? A ina ka hadu da Hurriya? Ina ka san Captain…”

“Ina karkashin kulawarsa ne Appa, ina tare da Captain kusan ko da yaushe, amman ku ya fada min kun mutu…”

“To ba shi wayar zan yi magana da shi….”

Hamad ya aje wayar akan gado domin bakin cikin abun da Captain yayi masa ba zai barshi ya sake hada hannu da shi ba. Captain ya kalli wayar sannan ya danne zuciyarsa domin ya san babba baya zama kamar yaro, kuma dole zai yi ma Hamad uzuri na halin da yake ciki a yanzu.

“Hello Appa..”

Iyami ce ta kirani tana kuka tana fada min wata magana da bata kama hankalinta ba, ni ma kuma bata kama nawa hankalin ba, shiyasa na kiraka sai kuma na ji makamancin abun da take fada min me yake faruwa.

“Labari ne mai tsawo Appa ba zai yiyu a waya ba, dole sai an zauna hakan kuma ba zai yiyu ba sai an dauki permission daga makarantarsu Hamad gudun lalacewar karatunsa”

“Hamad kake kira fa Captain…”

“Hamad Appa Hamad yana raye… Amman yanzu kamin uzuri zan tafi masaukinmu idan Hurriya ta natsu zamu yi magana… Zan kiraka na fada maka yadda komai zai gudana.”

Hankali namiji be taba zama iri daya da na mace ba hakan ya saka Appa ya saurare shi.

“Toh ina jira..”

Captain ya kashe wayar ya kalli Hurriya dake kallon Hamad kamar zata cinye shi tana hawaye.

“Kukan nan ya isa haka, ni da na san haka abun zai zama ba zan bayyana miki shi ba”

“Ni kuma sai na yi ta zama har zuwa lokacin da zaka bayyana ni bayan na ga yar’uwarta?”

Hamad ya fada a tsawace, Captain ko gefe da yake be kalla ba ya kama matarsa.

“Mu tafi Mama Rukayya suna reception suna jiranmu, daga can zan yi clearing kudin asibitin sai mu tafi masauki mu yi magana hakan yayi miki…”

Ta daga mishi kai.

“Hamad zai tafi tare da mu ko?”

Ya daga mata kai yana shafa fuskarta hawayen dake zubar mata yake jinsu har a ransa.

“Toh…”

Ya dauki mayafinta ya rufe mata kai sannan ya kama hannunta suka fito daga dakin.

 

NIGERIA….

Appa ya saka hularsa yana amsawa Yasir.

“Eh can zan tafi gurin Iyami na yi magana da ita, saboda na ji tana ta kuka abun ne da daure kai na rasa gane kan gadon labarin..”

“Ni ma na ji abun wani iri, maybe akwai abun da Captain din yake boyewa ko kuma Hurriya ta samu matsala ne? Yake biye mata…”

Yasir ya fada with confused.

“Amman na ji wata murya yake cewa Appa ni ne Hamad ne har da rantsuwa ni abun ya daure min kai… Shiyasa nake son na tafi gurin mahaifiyarta”

“Okay Aappa Allah ya tsare”

“Amin sai na dawo…”

A tare suka fito bangaren Appa ya shiga motarsa, Yasir kuma na nufi bangaren Hajiya Kaltume domin labarta musu halin da ake ciki. Shigarsa bangaren ta yi daidai ta cire mayafin da Hajiya Kaltume take tana sauke gajiya. Tana kallon fuskar danta ta san ba kalau ba, domin mamaki ne da daure kai a fuskarsa sai dai bata ce masa komai ba har sai da ya zauna.

“Lafiya.?”

“Wani abu ne mai daure kai Hajiya… Yanzu muna tare da Appa a gida muna duba kasafin kudin da suka shiga da fita na wannan watan bangaren Motocin Appa, sai Amma ta kira tana kuka wai Hurriya ta kirata da number Captain tana mata zancen Hamad, Appa ma be gane kan maganar ba sai da ya kira Captain din da kanshi sai wani ya karba yana cewa shi ne Hamad, Appa dai yayi magana da yaron kamin Captain ya karba ya ce idan sun koma masauki zai kira Appa su yi magana kuma shi Captain din ya fada ma Appa cewar Hamad ne, but labari mai dadi dai idon Hurriya ya bude”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected