Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Ai dole, tun da ta fara hada munafurci, amman duk da haka ni da kaina zan tafi na dawo da ita gobe, sai na nuna mata hankalin Babba dabam dana yaro, kuma idan za a asake korarta sai daia yi nata korar da zata tafi nesa da garin nan gaba daya, ba wai ta tsaya a kusa da Hajiya ta hada mu ko kuma Appanta ba”
“Shi ke nan Hajiya, daman na ce bari na fada miki ne abun da na ji”
“Kin kyauta kuma ina son cigaba da abun da kike yi, da zarar kin ji kyas ki zo ki fada min, tun daga kan Hurriya har Nafisa da kasuwancinta”
“Toh Hajiya na gode mu kwana lafiya”
Hajiya Kaltume ta daga mata kai, sannan ta bita da kallo tana tauna maganar da ta fada mata a ranta. Waye yaje yana masifar a dawo da Hurriya? Sonta yake ko kuma me? Waya sani ma ko kanta take bashi ko yake neman samu saboda ta zama marar aji yanzu, tun da uwarta ta bar gidan, kuma gashi har wani dan iskan ma Adam ya ce yana sonta.
“Hajiya…”
Ta juyo ta kalli Yasir dake saukowa yana sanye da jallabiyar da ya siye a Khadeeja Candy Store, sai shinning take kamar an zuba mata mai.
“Yasir ka dawo?”
“Eh, na shigo ai baki dakinki Khairy tace kin tafi bangaren Appa”
“Eh na je na yi magana da shi ne akan Hurriya, kasan kai baka son laifinta shiyasa ban fada maka abun da ta yi ba”
“Kararta kika kai gurin Appa kuma? Haba Hajiya? Duk bayan wannan abun?”
“Aa ba kararta na kai ba, sako Hajiya ta aiko mana wai muna takurawa Hurriya magana dai babu dadi ji, ni kuma na je na samu Appanku na bashi shawarar dawowa da Hurriya a gidan nan zai fi, ka ga mun guje bacin ran Hajiya kuma mun shirya ta da mahaifinta”
Yasir yayi murmushi dake fitowa har daga zuciyarsa.
“Haka na ke son ki zama Hajiya, kuma na ji dadin haka Allah ya saka miki da alheri”
“Amin”
Ta kalleshi sama da kasa.
“Yau ka dawo da wuri baka tafi gurin hirar ba ne”
Ya dan yi murmushin kunya ya shafa kansa, tare da cira kafa ya nufi dinning, Hajiya ta bishi da kallo na kauna da alfahari.
“Wai ni kam wace yarinya ce wannan mai tsada, har yau baka kawo min ita mun gaisa ba, kamar fa baka daukar komai naka da muhimmanci, ni bana son Miwan da Musib su rigaka aure, ka san kuwa suna dawowa kasar nan babu abun da za su yi sai aure”
Kai ya rankwafar alamar damuwa kadan na bayyana a fuskarsa.
“Hajiya, su dabam ni dabam idan ma sun riga ni aure miye a ciki? Komai fa lokaci ne, ni ma kuma yanzu yarinyar da nake jira ta kare karatu kuma ina son na maida hankali gurin gini na da hada kayan lefe, sai dai ni da ita muna tsoron yadda iyayenmu za su karbi abun ne, musamman ma ta bangaren iyayenta”
Hajiya ta Kaltume ta nufi gurin da yake
“Miye abun tsoro, ka tafi kanka tsaye ka fada musu waye ubanka a garin nan, dole a karba maka uwarka ma nan gaba kadan za a fara sakawa da ita cikin manya mata yan kasuwa na garin nan ko ma na ce na arewa gaba daya”
Ta karasa yayinda ta dora hannunta a kan kujerar da yake zaune. Juyowa yayi ya kalleta da murmushi a fuskarsa.
“Kasuwanci zaki fara Hajiya”
“Sosai kuwa, ina son na bude shagunan tufafi masu kyau da tsada, kuma zan bude gidan mai ba da jimawa ba”
“Kuma Appa zai yarda?”
“Me zao hana shi yarda? Nafisa ma ba kasuwancin take ba? Ina ce nan take siyar da sinari a shagonta ga kuma shagon aski da na gyaran jiki da na cin abinci da take da shi a garin nan, babu mai kalar shagunanta, sai kuma yace zai hana ni? Ai ba zata sabu ba”
“Toh Allah yasa albarka kuma ya hadaki da mutane na gari, amman ki kula sosai da wanda zai kula miki da abubuwanki”
“Amin, ai kai nake son ka zama shugaba”
“No ba zan iya ba, harkar kasuwanci ai sai Appa, ni ko zan iya sai nan gaba, yanzu akwai abubuwan da suke gabana?”
“Aure? Tun da na san ka gama karatu kuma kana aiki”
Ya daga mata kai.
“Aure Hajiyata”
“Wacece to? Da har kake tsoron iyayenta su ki karbarka? Ai babu yarinyar da zaka so a garin nan ita ko iyayenta su ce maka a’a”
Ya karkato ya fuskance da kyau.
“Har da Rukayya?”
“Ko Wacece kuwa, amman wace Rukayyar?”
Sai da yaja dogon numfashi ya aje ya sauke idonta saka dan kar ya hada ido da Hajiya Kaltume sannan ya bata amsar tambayarta
“Rukayya yar wajen Bappa”
“Ka kara batar da ni a duhu”
“Yar wajen Gwaggo, kanwar Amma, little mom din Hurriya…”
“Eeeehhh….. ”
Hajiya Kaltume ta dage hannunta da sauri matsa can baya kama wanda ta ga abun tsoro.
“Ba a gidana ba, da yardar Allah ba a gidana ba, duk wani sihiri da suka ma mahaifinka ya kama shi har Iyami ta aure kai kam ba zai kama ka ba, Innalillahi Wa’inna Ilaihiraji’un, yau na ga bala’i ganin ido… Rukayya kuma yarinyar da ta fi Iyami rashin mutunci da raina mutane? Haba Yasir duk matan duniya ka rasa waye zaka so sai jinin Iyami?”
Yasir ya mike tsaye.
“Jinin Amma me ye matsakarsu? Suna da tarbiya suna duk wani abu da ake nema a gidan mutunci, meye matsalar Rukayya”
“Bana sonta Yasir, ni da jinin iyami har abada, Hurriya ma rokon nake Allah ya raba ni da ita balle kuma ka dauko min wasu yan baki gida, ba ni ba yan baki gida har abada, kai kanka ba a banza suka barka ba”
“Komai dai na magani ne a gurinki Hajiya, kin ce Amma ta mallake Appa da mallaka ce me zai saka ya saketa? Ni dai In son Rukayya kuma ita za aura, matsalata a yanzu na yadda iyayenta za su karbe ni ba, ba kuma saboda kowa mai sai dan ke Hajiya”
Ya bar dinning din ya nufi stairs ransa a bace, sometimes ya kan gane kan mahaifiyarsa, ita kam binsa kawai ta yi da kallo zuciyarta na karanta mata cewar ba a hayyacinsa yake wannan maganar ba. Irin abun da aka yi ma Appa ne aka yi masa, wato son suke ta ko’ina su mallake mata da da miji. A ranar da tunani ta kwana washe gari Sallah asuba kawai ta yi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Fatee ta fada mata abun da ya faru, kamin ta kira Malaminta ta gabatar masa da bukatar.
HURRIYA POV.
Kafafuwanta a nade fuskarta kuma dauke da kayataccen murmushi take kallon Amma dake cin abinci da kanta, duk kuwa da kasancewar hannun nata rawa yake rabin abincin na zubewa, abun da bata iyawa tun a lokacin da ciwon ya same ta, gaba ta tisa Amma tana ta kallonta kamar zata cinyeta tsabar murnar mahaifiyarta ta fara samun sauki. Bayan Amma ta gama, Hurriya ta dauke plate din da cup din ruwa ta fitar sannan ta dawo ta zauna kusa da Amma.
“Allah na gode maka da ka fara bawa Ammata lafiya”
Amma ta yi murmushi domin shi ne kadai abun da take iya yi Idan farinciki ya same ta, idan kuma damuwa ce sai dai ta yi kuka, saboda bata iya magana, tana da abubuwa da yawa a zuciyarta da take son ta tambayi Hurriya amman babu baki, ita kuma Hurriya bata yarda ta yi hirar gidansu da ita, domin ba abubuwa masu dadi ne zata fada ba, ko da Gwaggo ta tambaye ta, ba zata fada ba sai dai tace tana zaune kalau. Cikin wani yanayi na tausayi da kauna da soyayya irin ta uwa zuwa ga yarta Amma ta mika hannunta dake rawa ta kama hannun Hurriya idonta na cika da hawaye..
“Minene Amma? Bana cikin damuwa a yanzu, Appa ya maida ni gurin Hajiya Binta, kin san yadda take so na ai, ita tace min na shirya na zo nan na wuni, saboda na kwana biyu ban zo ba, ashe zan zo na farar da farinciki ne, gashi na ganki Amma kina cin abinci”
Tana maganar tana sharewa mahaifiyarta hawaye a idonta. Twins din Amma suka zo da gudu suka kwanta jikinta suna ta son yin fitina, da Amma ta kallesu sai ta ga sun hadu su uku babu daya, da Hamad yana raye da yanzu yayanta sun cika hudu cif.