Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Mun shiga uku mun lalace, ya zamu yi?”
“Shiyasa bana son shigowa dajin nan gari gaba daya ya lalace a yanzu”
Cewar Hajiya Kaltume ido na raina fata.
“Kai direba ya zamu yi?”
“Hajiya ni ba ku kuka kawo ni nan ba, kuma gashi motoci a bayanmu balle mu juya”
Maganar yake yana leken motocin dake bayansu ga karar bindigar sai matsosu take.
“Toh ko dai mu kira Malamin nan mu fada masa”
Hajiya Fatee da fitsari ya fara zubo mata ta kalli Hajiya Kaltume.
“Ya mana me? Soja ne shi ko dan sanda?”
“Ya turo aljannu su dauke mu mana, Hajiya mutanen nan suka kama mu ai mun shiga uku, kuma na cewa Alhaji me? Daga zuwa sulhun aure!”
Cikin tashin hankali Hajiya Fatee ta ce
“Aljannu suka dauke mu ai shikenan mun bar duniya kuma kara ma wadannan da aljannu dan su kai mu za su inda babu kowa su aje, ko su kai mu China aljanni ai ba zai dauke ka ya aje ka nan kusa ba sai wata duniyar”
Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana neman agajin Allah.
“Allah ka yafe mana Allah ka dube mu Allah Innalillahi wa’inna Ilaihiraji’un, ni har na bata zane”
Direba ya bude kofar a hankali ya sulale ya yanki daji cikin ciyayi. Hajiya Kaltume ta saka kalma shada, Hajiya Fatee ta kama mata suka karasa suka kallon juna kowacce na kai hannu ta taba yar’uwarta. domin sun san yadda suka ci suka koshi nan ba za su iya gudu ba ko sa sun gwada hakan.
____________________
Hmmmmm masu karatu kun taba gani ko jin mugun kishi da bakar hassada irinta ta Hajiya Kaltume?
Ni dai Hurriya ta ba ni tausayi domin rayuwa gurin da baka bukatarka yana da wahala, musamman idan babu uwa a kusa.
Ta wani bangaren kuma Iyami tana da laifi daga zuwa aiki sai ki aure mijin mata? Ina laifi ki rumgume talaucinki ki shafawa kanki lafiya, yanzu wa gari ya waya…?
Mu hadu da ku page din gobe, amman kamin nan ina son na ga Comments baza-baza line by line in ji Bature…
☆❁ ❁☆
7️⃣
Ana kiran sallah asuba ta sauko daga kan gadon ta nufi kofar dakinta ta bude ta fito, a hankali ta sauko downstairs, tana isa bakin kofar falon bata tsaya komai ba ta kai hannu zata bude kofar.
“Ina zaki je?”
Ta juyo da sauri domin bata yi tsammanin wani zai iya fitowa at this early ba.
“Fita zan yi”
Ta amsawa Namra. Cikin mamaki Namra ta wara ido.
“Asuba ne fa”
“Na sani, Hijab zan dauko na yi sallah”
“Haba Hurriya shiga dakina ki dauko nawa mana, saboda Hijab sai ki fita tun a asuba ki koma part dinku kamar wata bakuwa, ke a gida kike fa”
Hurriya ta dan sauke kai kasa daga barin kallon yayarta wadda ta bata shekara uku da haihuwa. Namra bata sake ce mata komai ta nufi kujerar da ta zauna a jiya ta dauki agogonta da assignment din da ta yi, sai da ta kusa hayewa sannan Hurriya ta rufa mata baya, cikin ladabi da natsuwa ta shiga dakin Namra ta tsaya jikin kofa, haka Hurriya take bata sakewa da mutane tana da wahalar sabo, musamman idan ta san zaka tsangwame ta ko ka yi mata fada. Namra ta juyo ta jefo mata hijab din cikin hanzari Hurriya ta cafke.
“Akwai carpet din Sallah a can?”
“Aa babu”
Namra ta dauki nata ta jefa mata Hurriya ta sake cafkewa ta juya ta fice daga dakin zuwa dakinta. Bata shiga nata dakin ba sai da ta kwankwasa kofar dakin Hamad tana kiran sunansa.
“Na tashi”
Ya amsa mata daga can ciki, sannan ta wuce dakinta ta maida kofar ta rufe. Tun bayan da ta yi Sallah bata sake fitowa ba sai da ta auna lokacin makaranta yayi mata, sannan ta bude kofar a hankali kamar wata bakuwa ta rufe ta nufo hanyar saukowa kasa gabanta har faduwa yake kar ta hadu da Musib ko dan’uwansa Miwan balle kuma Momy da ta san bata ishe ta kallo ba. Sai dai ta yi rashin sa’a Momy da duka yaranta suna falon zaune, abun da bata saka tsammani ba domin Momy bata tashi da wuri sai idan tana bangaren Appa shi ma da zarar ta kai masa abun karyawa zata sake komawa bachi kuma babu mai tashinta sai gidan maigidan ne da kansa if not kowaye ya tasheta zai gane kurensa a ranar.
“Baka fada min zaka zo ba, ai da na saka an shirya mana abinci mai kyau”
Cewar Momy tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune a kujerar dake facing nata, kyakkyawan saurayin farin saurayin mai jini a jika ya girgiza mata kai yana duba agogo hannunsa.
“Noo Momy na gode tafiyar ta gaggawa ce, yanzu zan kama hanya, kawai na ce bari na biyo mu gaisa ne”
Momy ta yi murmushin kasaita irin na manya mata.
“Daman na sani, abinci idan ba na Hajiya Turai baka ci na kowa”
Ya dan fadada fuskarsa da murmushim da ya kara masa kyau da haiba yana daga kai ya kalli Hurriya dake saukowa. Momy ta dan juya ta kalleta kadan ta dauke kai irin ba ki isheni kallo ba din nan.
“Momy ina kwana”
Hurriya ta gaisheta cikin ladabi Momy har ta yi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ci albarkacin bakonta amsa ciki ciki kamar an mata dole.
“Yaya Musib ina?”
Ya amsa, ta juya gurin dan’uwansa shi ma ta gaishe shi, sai ya amsa mata fuska a sake kamar dan’uwansa, ta kalli Namra ta gaishe ta kamin ta rufe baki Namra ta amsa tana mata an tashi lafiya, daga karshe Hurriya ta cike gaisuwarta da bakon da take kyautata zaton yana da muhimmanci a gurin Momy da yaranta ganin yadda suke ta murna da ganinsa kuma suka fito dukansu da sanyin safiyar nan suka zauna a falo just because of him.
“Ina kwana”
Ya d’auki ‘yan dak’ik’u kafin ya amsa gaisuwarta, shi ma kuma ba da baki ba kai kawai ya daga mata and light smile. Binta yayi da kallo har ta wuce ta gabansa ta nufi kofar fita.
“ƴar Mijina ce, kanenta ne ka ga ya fita dazun”
Momy ta fada masa domin ta san ba zai tambaya ba, ta san kallon da yake mata be wuce na neman sanin wacece ba, dan zuwan da yake gidan jefi jefi be taba ganinta ba, haka ma bata yi masa kama da masu aikin Momy ba balle yace ko yar aiki ce, ba zai ce ya san kowa a gidan ba, amman yadda ya san familynsu musamman Momy idan har ta bawa wani damar shiga ma a falonta to yana da muhimmanci a gareta, sai dai abun da be sani ba wannan shigar ta dole ce ta cilastawar Appa ba dan Hurriya tana da muhimmanci a gareta ba.
“Yaya ance an daga bikinka”
Miwan ya tambaya yana kallonsa. Mutumen da Miwan ya kira da Yaya ya juyo ya kalleshi.
“Ka aje wannan Yaya aside ka kira ni da real sunana Jamal”
Momy ta yi murmushi mai sauti.
“Haba dai Captain dukansu fa kanenka ne ta ina za su iya kiranka da sunanka kai tsaye, dole sai da girmamawa”
“Wallahi na tsani wannan Yayan na fi son a kira ni da sunana na gaskiya”
Ya amsa mata da murmushi sannan ya mike tsaye sai zuba kamshi yake. Namra ta mike tsaye kamar sauran yan’uwanta tare da fadin.
“Tafiya nan da nan Yaya ba zaka dade ba”
Da hannu ya nunata.
“Yanzu na gama yi ma Miwan gargadi shi ne ke ma zaki ďana ko?”
Sai duk suka saka dariya ban da shi da ya nufi kofar fita yana yi ma Momy sallama. Momy ta mike tsaye ta rako shi har bakin kofar falon Miwan da Musib suka karasa gurin da ya faka motarsa suna masa a sauka lafiya, Momy da Namra kuma na tsaye jikin kofar har sai da ya shiga motarsa yayi musu horn ya fice sannan suka dawo cikin falon.
“Captain baka iya masa, Allah kadai ke masa daidai, komai ka yi sai yace ba haka ba ga zuciya abu kadan ya fusata shi”
“Ai gaskiya Ammy tana hakuri da shi”
Cewar Namra Momy ta ce.
“Toh ya zata yi haka Allah yayi shi, kuma shi kadai ya bata daga ita har Yayana magajin da suke da shi kenan”