VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Gata nan”

Namra ta fada, sannan ta zauna Hurriya ta karaso inda yake ta tsaya gabansa ta kalleshi sau daya ta sauke kai kasa, Hamad kuma yake tsaye kusa da kofar falon yana kallon ya ga abun da za’ayi ma yar’uwarsa. Captain ya maido ta hannayensa gaba ya mika mata box din da ke hannunsa da hannunsa na dama ba tare da ya ce komai ba. Ko be fada mata ba, ta san box din glasse ne domin shi dabam yake ta ka ganshi kana ganewa balle kuma ita da take 5&6 da glass. A hankali ta dago ta kalli fuskarsa bayan ta kalli gilashin sannan ta kalli Hamad ya watsa mata harara duk ya bi ya bata rai, domin har yanzu haushi Captain din yake ba shi, daman kuma shi be iya tsana ba idan ya tsane ka sai Allah ke kasa ku sake shiri da shi. Captain ya karkarata da kansa kadan ya kalli Hamad da sai a lokacin da ya san da shi tsaye a gurin sai kuma ya kalli Hurriya. Ita ma ta kalleshi ta dauke kai ta nufi kofar fita daga falon ba tare da ta ce masa Komai ba balle kuma har ta karba, sai da ta fara ficewa sannan Hamad ya bi bayanta yaja kofar falon ya rufe. Captain ya matse box din gilashin dake hannunsa da mugun karfi ya daga kansa sama ya rufe ido.

“Allah ya sassauta min kar na kashe yarinyar nan….”

‘Tab ka kasheta Wallahi kai ma sai an kashe ta dan gata be fi gata ba, ita ma yar gatan banbanta ce’

Namra ta fada a ranta a fili kuma sai ta ce.

“Glasse ne?”

Ya sauke kan ya kalleta.

“Wuka ce”

“Gilashin da Appa yake siya mata mai kyau ne daga waje ake kawo mata”

Ta fada a zahiri a badini kuma sai ta ce.

‘Captain dai kamar ka fi kowa iya bakar magana’

Kamar ta san zai kara mata.

“Wannan a bula na dauko shi”

“Tambaya ce kawai, daman ai na san Hamad ba zai bari ta karba ba, amman ka ba ni zan bata hakuri sai na bata daga baya”

Ya kai dayan hannunsa yana zagayen gilashin da shi.

“Waye Hamad?”

“Kanenta ne wanda ka ga ya tsaya jikin kofa har ta kalleshi, shi ne ya fasa maka tayun mota saboda ka mareta, ni ma ban sani ba sai yanzu yake fada”

Murmushi yayi mai sauti, ya dago ya kalleta ya sake yin murmushi mai cike da mamaki.

“Wow… Nice…”

“Haka ya kamata dan’uwa ya zama, mai kokarin kare yan’uwansa i like him”

Ya fada after yayi taking few seconds yana kallon wani bangare na falon, because he know yayi missing wani part na shi da be taba samu ba, wato yan’uwa da suka hada uwa ko uba ko ma uwa da uban gaba daya.

“Amman haka ba zai hana a hukunta shi ba, they have to pay for what they did”

Ya juya ya fice daga falon ba tare da ya nemi a kira masa Momy ba, daman kuma ba dan ita ya zo ba wannan karon, ya zo ne domin baya Hurriya gilashin da ya siyo Saudiya saboda ya fasa nata, and that slap da yayi mata ya tsaya masa after ya bar gidan saboda lura da yayi da bata gani sai da gilashin kamar yadda Namra ta tabbatar masa tun a wacan ranar. Namra ta san me yake nufi they instead of he, wato Hurriya saboda ta ki karbar gilashin Hamad kuma saboda ya fasa masa tayun mota. Sai da ta leka ta ga tashin motarsa sannan ta saki curtains din tana fadin.

“Ban da kai Captain ana kyauta dole ne, ko ni ce ai ba zan karba ba, ka yi zafin hannu ba wani uzuri da an maka abu sai zafin zuciya”

Ta nufi upstairs, sai da ta fara leka dakin Momy ta ga har lokacin bachi take sai ta ja mata kofar a hankali ta nufi dakinta.

 

HAJIYA KALTUME POV.

“Yanzu kina da number Salame?”

“Eh ina da ita, ai ko shekaran jiya ta zo gidan nan, har take min zancen Malamin ni dai ban tanka ta ba, domin damuwata ta isheni kar na yi abun kunya”

“Kunya Hajiya fatee? Tofar da yawu, har abada ba zamu taba kunyar duniya ba lahirar ma muna fatan nasara, saka number ki kirata ki ce ta turo miki number Malamin ko kuma idan ta samu lokaci ta shigo sai ku yi magana”

Hajiya Kaltume na rufe baki Hajja Fatee ta dauki waya ta shiga laleben number Salame. Knocking aka yi har sau biyu sannan Hajiya Fatee ta amsa.

“Waye?”

“Hajiya Yaron nan ne ya sake dawowa fa, kuma mai Baba mai gadi ya ce yayi yayi da shi amman ya ki tafiya shi sai ya ganki”

Hajiya Fatee ta hanye wayar ta rafka tagumi.

“Oh wannan fitinanne yaro ba zai bar ni da abun da ya ishe ni ba”

“Waye haka?”

“Wallahi wani yaro ne na dauka aikin ba fulawa ruwa, ashe barawo, ni ban sani ba, irin yaran nan yan sare sare, wata rana suka zo nemansa har da fasa mana gida aka ayi, tun daga lokacin sai na sallame shi, amman yaron nan ya ki ya rabu da ni, duk lokacin da wani abun ya same shi sai ya zo ya fada ko mai dadi ko marar dadi, ko kuma ya ce ya zo gaishe ni, yanzu ya bi ya fitine ni yau sati biyu kullum sai ya zo wai mahaifiyarsa bata da lafiya ni yake son gani”

“Ikon Allah toh ke Hajiya irin wadannan yaran ai suna da amfani wata rana”

“Hmmm baki san yadda suke fitinar mutum ba ne, ga su da shegen na ci idan sun ga samu”

“Bari na yi magana da shi, ki kira Salame yanzu”

Hajiya Kaltume ta mike tsaye tabur tabur ta fice daga dakin, Hajiya Fatee kuma ta shiga kiran Salame da wayarta.

“Ina yake?”

Hajiya Kaltume ta tambayi one of masu yi ma Hajiya Fatee aiki da ta zo sanar da Hajiya.

“Yana can gate”

“Muje na ganshi”

Mai aikin ta wuce gaba Hajiya ta sauko tana bin bayanta har suka fita falon suka isa gate ta tambayi mai gadin ina yake.

“Yana waje Hajiya kullum sai ya zo kuma ita Hajiya ta ce kar a barshi ya shigo”

Ya bude mata karamar kofar gate din ta leka waje ta ganshi zaune daf da gate din, a take gabanta ya yanke ya fadi domin ya tuna mata da lokacin da suke cikin daji hannun yan ta’adda, ga fuskarsa duk tambo alamar ya sha sara har ya gaji, bakinsa baki kirin ido kamar an daka tarugu tsabar ja, jiki a murda kamar gashin kansa, kana ganinsa ka ga rikakken dan ta’adda.

“Kai ne kake neman Hajiya Fatee?”

Hajiya Kaltume ta tambaya cikin karfi hali domin zuciyarta har wani zillo take.

“Ni ne Allah ya taimakeki, Hajiya Wallahi ina cikin matsala ne, su kuma wadan nan watsatsin masu aikin kullum na zo sai su hana ni shiga, ba dan ina ganin mutumcin Hajiya Fatee ba da yanzu na farka cikin mai gadin nan Wallahi, sai dai Hajiya tana da kima a idona kamar uwa take a gurina ba zan iya haka ba”

Magana yake da irin muryar mazan nan da shaye shaye ya gama canja kalar muryarsu ta koma mai ban tsoro. Hajiya Kaltume ta yi murmushin karfin hali.

“Ka kyauta haka ake so ai, ya sunan ka?”

“Sunana Isiyaku, amman dai wasu kan ce min Danja yan sunanayen nan dai na zamani Hajiya”

“Toh Amman me kake so gurin Hajiya?”

A take ya fara kuka kamar wani yaro ko wawa kukan da babu hawaye sai zallar iskanci.

“Hajiya Gyatuma aka kwatar a asibiti, kuma ba ni da ko sisin na magani, ita Hajiya Fatee ta sani ba na wani aiki bana sana’ar komai tun da na bar gidan nan ban sake samun wani aikin ba, ina cikin matsala bana da gata sai Allah sai Hajiya Fatee so nake ta taimaka min da kudin magani, kar gyatuma ta mutu Wallahi Allah akwai matsala idan ta mutu ba a taimaka min ba, duk mai hannu a ciki sai na ci uwatar…”

Yana fada yana hada hannu biyu ya buga, Hajiya Kaltume ta dan ja baya sannan ta kalli mai aikin ta ce.

“Zaki iya tafiya”

Sai da mai aikin ta yi nisa sannan ta taka kafarta ta fito daga cikin gidan ta taka nesa da gate din yadda mai gadin ba zai ji abun da zata fada ba. Sannan ta tsaya ta kalli Danja ta ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected