VENNETE
Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel

“Innalillahi Maama kunna haske, na shiga uku… ”

Kamin Maama ta kunna fitilar wayarta Mekano dake aikin bada hasken wuta a gidan ya fara aikinsa, haske ya cika ko’ina. Hajiya Kaltume ta dafa zuciyarta tana sauke gajiya.

“Kai Allah raba musulmi da wahala, har yanzu ji nake kamar ina kusa da dajin nan, shiyasa ko waya bana son karba, mun ga tashin hankali mun ga shiga uku duk saboda bakar Iyami”

Hajiya ta karasa tana fashewa da kuka, domin Iyami ta hana ta zaman lafiya ta hana ta rawar gaban hantsi.

*** *** ***

Ta dayan bangaren Iyami tana ta fama da nata, tunanin da damuwa sun hana ta walawa ko da kuwa tsakar gidan ne, ga wani sabon lalurar laulayi da ya same ta bayan dawowarta gidan iyayenta, iyakar kokarinta tana yi na nunawa Gwaggo da Bappa ta karbi kaddara, sai dai a kasan zuciyarta tana fama da tunani domin kuwa tana son mijinta, domin tana zaune lafiya a gidan tana rumgume da yayanta ciwonsu lafiyarsu duk ta sani, ba kamar yanzu da tunanin halin da suke ciki yake hana ta sukuni ba. Gashi a duk lokacin da Hamad ya zo gidan sai ya fada mata abun da aka yi musu, Hurriya ce bata fada saboda bata son tashin hankali Amma kuma tana da zurfin ciki. Gwaggo ma tana iyakar kokarinta na kwantar mata da hankali ganin cikin dake jikinta gudun kar ta jawa kanta wata matsala. Addu’a kuma su dukansu suka dukufa da yinta ta neman Allah ya daidaita tsakaninta da Appa, sai dai ta bar kyau tun ranar haihuwa domin bata damu da yin azkar din neman tsari ba, tana ta tawaya a wannan babin, duk kuwa da ta san tana cikin kishiyoyi irinsu Hajiya Kaltume da Momy.

☆❁ ❁☆

Hello Habibaties
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy

1️⃣0️⃣

Washe garin ranar…

Hurriya na cire uniform dinta na makarantar boko ta dauki bakar abaya ta saka, ta bude gurin da take zuba hullunata tun bayan da ta kwaso kayanta daga bangaren Amma ta dawo da su bangaren Momy a dakin da aka bata, ta dauko farar hulla ta saka a kanta. Sannan ta fara gyara dakinta ta kintsa komai, cikin natsuwa ta fito daga dakin ta shiga dakin Hamad da ya watsar nasa uniform din akan gado ta dauka ta aje masa ta gyara masa dakin, daman shi be kula da gyara daki ba ko a lokacin da Amma na gidan balle kuma yanzu da tufafinsa ma sai da Hurriya ta kwaso ta dawo masa da su dakinsa dake bangaren Momy. After ta gyara nasa dakin ta sauka kasa domin dauko abun shara da mopper haka take kullum idan ta dawo take gyara nata dakin da na Hamad domin Momy ta hana masu aikinta share dakin Hamad da Hurriya haka ma ta hana ko cokali suka aje masu aiki su dauka, kamar ya yaran gidan ba haka Momy take treating dinsu, musamman ma Hurriya da bata iya budewa kowa cikinta, Hamad kuma idan ya ci abinci a nan yake bari sai dai Hurriya ta dauke masa, ba kowane rules and regulations na Momy ya sani ba, ko na ya sani ba amfanin da za su masa domin ba bi zai yi ba.

Gurin da ake aje kayan taje ta dauko ta hauro sama a hankali, domin Momy ta jaddada mata bata son jin karar tafiyar kowa a saman, hakan ya saka take kokarin ganin ta kiyaye dokokinta, ta san ba dan komai take nata haka ba sai dan ta takura mata idan kuma ta fadawa Appa wata kila zata iya jawa kanta matsala a gurin Momy. Dakin dan’uwanta ta fara gyarawa sannan ta shiga nata dakin ta fara sharewa. Cikin ɗoki Hamad ya shigo dakin nata.

“Hurriya za mu je dauko Hajiya yanzu”

Ta juyo ta kalleshi da sauri.

“Wace Hajiya”

“Hajiyar Appa tace zata zo, Appa ya kira ni yace na zo muje daukota yanzu nan”

Hurriya ta daka tsalle tana murna, daga ita har Hamad suna matukar son zuwa gurin Hajiya Binta kuma suna daukin ganinta a gidan ubansu, al’adace ta Alhaji Haruna, duk ranar da mahaifiyarsa zata zo gidansa da kansa yake zuwa ya daukota idan kuma ta tashi tafiya shi zai maidata gidanta, komai yake zai aje ya dauko ko ya kaita gida matukar gidansa zata zo, wannan ya saka tun ana sauran kwana biyu ta zo gidan take sanar masa, shi kuma ya sanar ma matansa a shirya mata tarba mai kyau. Murmushin da murnar da Hurriya ta gani a fuskar dan’uwanta Hamad ya ninka farinciki zuwan Hajiya Binta da take a gidan, domin tun tafiyar Amma bata san wata rana da Hamad ya sake fuska yana far’a kamar yau ba.

“Zan mata wanka mai kyau kin san ta iya tsokana ta tana cewa ban iya wanka mai kyau ba, tufafi zan canja yanzu nan”

Da karfi yake maganar, kamar yadda ya saba yi a bangaren Amma idan yana cikin farinciki. Hurriya ta yi saurin yi masa alama.

“Yi a hankali kar Momy ta ji ta fara maka masifa?”

“Saboda me?”

“Bata son hayaniya kuma tace idan zamu hauro ko sauka stairs mu yi a hankali kar mu yi making sound bata son ana hawa mata da karfi”

“Yaushe tace haka?”

“An dade, kai ai ba zama kake bangaren ba sai idan zaka kwanta shiyasa baka sani ba”

“Sai na fadawa Hajiya duk abun da ake mana a gidan nan”

Hurriya ta saki mopper dake hannunta ta nufo kofar dakin gun da Hamad yake tsaye.

“Hamad kar ka yi haka, kasan zata yi ma Appa fada shi kuma zai yi ma Momy, idan aka yi Momy kuma kan mu zai dawo”

“Sai na sake fada mata, Appa ma dan ina fushi ne da shi shiyasa ba zan fada masa ba, ni ba zan ma iya zama bangaren nan ba i hate them”

Ya saki kofar ya nufi tasa kofar ya bude, Hurriya ta dora hannu daya akai tana jin ina ma ace bata fada ba, tsoro take kar ace daga dawowarta bangaren ta fara hada munafurci, kuma ta san at the end abun gurinta zai dawo. Hamad na canja tufafi ya dauki turare ya saka ya canja shoes ya fito daga dakin ya sauko kasa ya fice daga falon daga Miwan har Namra dake falon be cewa kowa komai ba. Miwan ya bishi da harara

“Yaro nan fa ya raina mutane, idan zai shigo haka zai shigo babu sallama idan ya tashi be iya gaishe da kowa”

“Yaya idan ka ce zaka biye ta Hamad za ku yi ta samun matsala ne fa, Amma ma da tana nan fama take da shi balle kuma mu”

“Ba ruwana da rashin jinsa ko rashin kunya ni ubansa zanci Wallahi”

Ya amsawa Namra yana ayyana yadda zai yi ma Hamad mugun duka idan ya shiga gonarsa. Namra dai bata sake cewa komai ba ta shiga ta jera warmers din da masu aikin Momy ke ajewa a kasan dinning, Hurriya ce ta fito rike da boket din da ta yi mopping da mopper ta nufi hanyar tsakar gidan dake ta cikin falon Momy ta bude kofar baya ta fita ta wanke komai sannan ta dawo cikin falon, a daidai lokacin da aka turo kofar falon aka shigo wata doguwar mace ce tana sanye da bakar abaya da aka kawata da blue stone ta daura dankwalin atamfa saman kanta sannan ta dora mayafin abayar a sama ya sauko mata, hannunta na rike da Gucci bag, tsalle Namra ta saka ta kwala ihu ta nufi matar da alama ta nuna murmushi sai ma sai yayi yaki yake samun mazauni a fuskarta, kallo daya zaka masa ka fahimci ta ninka Momy kasaita da ji da kai.

“Ammy sannu da zuwa”

Cewar Namra cikin zumudi tana rumgumeta, Miwan ya mike tsaye yana gyara rigarsa tare da yi mata barka da zuwa.

“Namra…ana gida”

Ta fada kamar mai jin wahalar magana.

“Eh Ammy sannu da zuwa, tun safe muke duban hanyarki”

“Toh gani na iso, Ina Hajiya Nafisa?”

Ta tambaya tana kallon Hurriya da ta yi tsaye da ta fito daga dakin da da ake aje mopper.

“Momy Momy Momy…”

Namra ta daga murya tana kiran Momy, Hurriya kuma ta dan risina kamar yadda ta saba ta gaisheta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected