Huriyyah Book 1 and 2 Complete Hausa Novel
“Samarin yanzu hauka tana damunsu, idan yarinya tace bata sonka sai ka koma bibiyar bayanta kuma? Da alama dai ba son gaskiya yake mata ba shiyasa ya koma bibiyar rayuwarta”
“Ni ma haka na ce”
Captain ya fada babu kuzari babu nishadi da jindadin da ya shigo da shi. Daddy ya ce.
“Amman Barrister tana da gaskiya, mahaifin yarinyar ba zai kawo matsala ba, ka san wasu iyayen basa son bibiyar irin wannan lamarin”
“An abun haushi ma mahaifinta be san ina son yarinyar ba, be san na dauki wannan matakin ba, na shigar da karar ne a matsayin wanda zai aureta ba tare da tunanin wata matsala zata biyo baya ba, amman yanzu ina tunanin zan yi magana da Barrister na fada mata a canja abun”
“Saboda me?”
“Ammy bata so kuma. Na fada mata na hakura Daddy”
“Hakan yana da kyau, amman ka bari mu yi magana da mahaifinta mu sanar masa halin da ake ciki idan ya aminta sai a sauya labarin daga kai zuwa mahaifinta kai tsaye, a matsayin mahaifinta ya shigar da karar ba kai ba, daman hakan zai fi mutuncin saboda kai ba aurenta ka yi ba, da ace kai mijinta ne kana da full hujja”
“Okay, Daddy amman idan ka tafi please ka lurar da shi wasu abubuwan na rayuwa, na tafi asibitin ban ga yarinyar ba kuma na tafi gurin Momy tace min yarinyar tana gurin mahaifiyarta, ina tunanin korarta yayi gashi bata gani kuma mahaifiyarta bata da lafiya bakinciki sai yayi mata yawa”
Daddy ya ji tausayin Hurriya ya kama shi.
“Amman me zai hana a nunawa mahaifinta video nan maybe zai sauko ya yafewa yarsa laifin da bata aikata ba”
“Aa bana son nuna masa shi a yanzu, already case din yana hannun DSS idan aka fitar da video lauyoyin Adam zai su iya cewa an masa cin zafi ne an masa da karfi ya fadi abun da ba ayi ba, kuma na yi ikirarin ban dauke shi ba fitar da video zai rushe wacan ikirarin nawa, and Salim zai iya samun kofar shigar da koke a kaina, bana son ya samu wannan damar, amman idan aka je kotun shi da kansa zai sallamo yarinyar ai kuma dole kowa ya san me suka shirya kuma na saka a bincika mutanen da suka yada hotunan kowa zai fadi inda ya samu ai daga nan gaskiya zata fito”
“So shari’a biyu za’ayi kenan?”
“Yeah… Yarinyar nan mai tsada ce Daddy, su sun shigar da ni saboda na karya ma dansu hannu, mu kuma mun shigar saboda dansu ya ci mutuncin Hurriya, and na yi alkawari kowa sai ya karbi kasonsa sai na kunyata su kamar yadda suka kunyata yarinyar nan”
Yana fada yana jaddawa jikinsa na rawa yana matse hannunsa.
“Allah kadai ya san halin da take ciki yanzu, sanadinsu ta rasa idonta gaba daya daman ba lafiya ta wadace ta ba”
Daddy dai sai kallonsa yake da yanayin.
“Zan tare da mutane a gobe zan jajanta masa abun da ya faru kuma na fada masa matakin da ka dauka, idan ya ba mu hadin kai shi ke nan idan kuma be aminta ba dole mu yi aje case din”
“Daddy please ba zamu aje case din ba, na mata alkawari ko da ba zan aureta ba be kamata na kasa cika alkwarin da na yi mata ba”
Daddy be sake cewa komai ba, ya ciro wayarsa dake aljihu yayi yana tabawa. Can ya dago ya kalli Captain yana murmushi.
“Lawyer na ne ya aiko min sako, wai Bashir Sarauta yace ba a janye case din a gobe, wata kila yana tunanin saboda an kai case din dukan da ka yi masa a kotu ne ya saka ka sake daukeshi”
“Ya zo nan ne?”
“Ya zo nan amman ban yi magana da shi ba na fada masa be kai wannan matsayin ba a yanzu, da kam ina ganin mutuncinsa amman ban da yanzu, kuma na fada masa idan ya sake zargin ďa na da daukar yaronsa sai na shigar da kara a kansa”
Captain yayi murmushi da be wadaci fuskarsa ba.
“Daddy wannan ai shi ake cewa fin karfi”
Daddy ma yayi murmushi mai sauti irin na masu dollars and pounds.
“I have to do the needful kamin na bar garin nan, gobe da yamma zan koma Kaduna ban sani ba ko Ammynka zata bi ni ko kuma zata tsaya jinyar ďanta ne”
Captain yayi murmushin da ya kusan za a iya cewa ya zame masa dole ne kawai, sannan ya mike tsaye yayi ma mahaifinsa sai da safe ya fice.
HAJIYA KALTUME POV.
“Tun jiya da muka yi waya da ke baki sake kirana ba, abun har ya soma ba ni tsoro, da na shirya zuwa gidanki a yau”
Hajiya Fatee ta yi murmushi.
“Ai ni dole na zo na same ki Hajiya Kaltume shiyasa da Fadeel na kira cikin na ce ya zo ya kawo ni gidan nan, amman Hajiya gajin hakuri kika yi ne har kika aikata mata haka?”
“Ina fa wai ni? Wannan ai can ya fito tsakaninta da dan’iskan saurayinta, wata kila matsala suka samu shiyasa ya watsa hotunan, ai ni ya biya ya hutar da ni wannan kadai ya isa ya hana Hurriya aure, domin babu wanda zai daukarwa yayansa uwa irin wannan? Sai dai a samu dan baro can ko masu gyaran talkama a hada su, idan ma ta samu domin babu mai auren makauniya”
“Kuma kika ce ta rantse da kur’ane?”
“Haka Khairy tace, wata kila kuma wani ne acan waje yake taya mu fadan, kuma shi ma yaron nan ta yi masa wulakanci ba, kuma abun da zai baki mamakin idan ba su saba haduwa ba a ina ya samu hotunanta”
Hajiya Fatee ta kyalkyale da dariya ta bawa Hajiya Kaltume hannu suka tabe.
“Ai wannan abun yayi dadi Wallahi ana ganin yarinya kamar ta kirki ashe ita ma yar banza ce”
“To kin gani dai gashi Allah ya tona asirinta, ko uwarta ai zaman banza ta so samu gurin Alhaji shi kuma da yake ba dan’iska ba ne sai ya bijiro mata da aure”
“Amman ni abun ya ba ni mamaki da kika ce Alhaji be koreta ba, ga irinsu nan da yawa ana kora da ya korata da mun huta ma”
“Ni ma abun da yasa na kira na tambaye ki kenan ko dai Malam be fara aikin nan ba har yanzu? Kin ga shiru fa ina zaune a gidan nan amman Alhaji be yi wani unkuri na maida aurensa da ni ba, jiya kuma Khairy ta fada min kuka yayi ta yi yana tsinewa wanda yayi abun nan”
“Zai yi wahala ace ba a fara ba, ya kamata dai mu kara hakuri kar mu yi gaggawa, domin tun ranar da aka tura kudin na kira shi na fada masa an tura kudin kuma yace min sun shiga ya gani, har na yace min anjima kadan zai shirya ya tafi gurin Malamin nasa ya kai masa kudin, tun daga ranar ban sake jin wayarsa ba, ko yanzu na kira bata shiga ba”
Ta sake gwada kiransa a gaban Hajiya Kaltume aka ce wayar a kashe take.
“Kin ji ko? Ina tunanin ko dai wayar tasa ta fadi ne, har wadda ta hada mu da shi na kirata tace ita ma bata samun wayarsa a yanzu”
Da mamaki Hajiya Kaltume ta ce.
“To kuma be siye wata ba? Ni fa jikina ya fara sanyi Hajiya Fatee”
“Karki ji komai, ni na yarda da Malamin nan dari bisa dari, mu kara hakuri idan aka kara kwana biyu ba mu ji komai ba ni zan shirya da kaina na tafi kauyen na bincika na ji”
“Allah yasa dai yayi mana aikin mai zafi, so nake Alhaji ya zo jiki na rawa ya roki yafiyata kuma ya maida aurensa, sannan a shafe masa Hurriya da uwarta a ransa kuma a hana shi auren nan da zai kara a mallaka min shi na juya shi yadda nake so”
“Wannan ai a rubuce yake, daman ya fada miki irin aikin zai yi kuma zaki gani, ke dai ki kwantar da hankalinki ba gashi kin fara gani ba, wata kila aikin ne ma ya saka hotunan nata suka yadu”
Hajiya Kaltume ta rike baki tana mamaki da dariya.
“Haka fa.. Kin ga gaba kenan sai kora, kuma da yardar Allah sai Hurriya da uwarta sun koma bara, tun da idon ya rufe ba zan bar Alhaji ya nema mata magani ba kuma ba zan bari ya maida uwarta ba, kin ga rayuwa ta kare musu kenan, daman na fada mata sai na dandana mata bakinciki kuma sai ta gani, ba za a ci amanata a zauna lafiya ba”